BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Dariya Halwa tayi tana waro idanu tace
“me nayi miki kuma? Don kawai nace kibada kuɗi?”.
“Oho ke kika sani”. Cewar Zainab
Still dariya Halwa tayi tace
“Kiyi haƙuri to, wlh banda kuɗi ne yau, nasan kuɗin da nake dashi bazai ishe ni har nabiya miki ba, coz akwai abinda nake so nasiya dashi”.
Zainab tace “uhmm naji, but kinsan da muka zo nan sai natuna da Haris? Wlh sai naji gabana na faɗi sabida abinda kikai mishi ranan Wednesday kullum mukazo nan sai na tuna, I know zai zo yarama”.
Jin sunan Haris da Halwa tayi ba ƙaramin bugawa zuciyar ta tayi ba, tsoro da fargaba suka zo suka dirar mata alokaci ɗaya, nan da nan annurin fuskarta yaɓace ɓat, ɗan sauran kuzarin da take ji shima yaɓace ɓat, take tasoma jin kamar wani sabon zazzaɓi ne zai rufe ta, Zainab sai magana take mata but ko kaɗan takasa furta komi har suka shige makarantan, koda suka shiga cikin class ɗin su tunda Halwa tazauna bata sake magana ba, Zainab da tatambaye ta ce mata tayi “kanta ke mata ciwo, da alamu zazzaɓin ne ke son dawo mata”, don haka Zainab ɗin bata wani matsa mata ba taƙyale ta, a ranan haka ta wuni duk bata da walwala, sai gab da za’a tashi ne wani Malami yayi musu Test sannan aka tashe su.
Lokacin da suka dawo gida, suna zuwa ƙofar gidan su Zainab, Zainab ɗin tace mata
“To ƙawata sai gobe kenan”.
Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi tawuce gida, akan dakalin ƙofar gidan su tahangi Nura zaune shi kaɗai, ƙarisawa tayi tasami waje kusa dashi tazauna tana kallon shi tace
“Yaya har kadawo aikin yau?”
Ɗago kan sa yayi dasauri don da alamun be san da zuwan ta wajen ba sai maganarta da yaji, yace
“Uhm kin dawo? ai banji zuwan ki ba”.
Murmushi tayi masa tace
“Tunanin me kake yi to?”
Ɗage kafaɗa yayi yace
“Tunanin wajen aiki mana”.
Still murmushi tayi tace
“Menene abin tunani to? Ada da baka samu ba kana tunani, yanzu kuma kasamun ma baza kabar zuciyarka tahuta ba?”
Murmusawa yayi yace
“Bazaki gane bane Dear, amma dai yanzu share wannan batun, kinga kin dawo kinsha hanya kishiga gida”.
“To kai kuma fa?” Tatambaye sa tana ƙure sa da ido
Ɗan kawar da kan sa yayi yabata amsa
“Ba yanzu ba, ni yanzu ma wajen Ali zani”.
“Ok.. sai kadawo”. Tafaɗa tana wuce wa tashige gida batare da tajira amsan shi ba
Shi kuma kallon bayan ta yayi har tashige kana yakau da kan sa yana sakin ɓoyayyen ajiyan zuciya, hannayen sa yasaka yatallabo cheeks ɗin sa yana ci gaba da tunanin sa.
**** **** **** *****
Da gudu tashigo cikin parlour’n tana kiran sunan Mami, matashiyar budurwa ce da shekarunta bazai gaza 24yrs ba, bayan ta kuma matashin saurayi ne me kimanin 20yrs, da alamun ƙanin ta ne don sosai suke kama da juna, Mami da fitowar ta kenan cikin ɗakin ta taji muryan ɗiyar nata tana kwaɗa mata kira, sai tawashe baki tana faɗin
“Oyoyo daughter”.
Da gudu tazo tayi Hugging ɗin ta tana me cike da farin ciki
“Mamina I’m back”. Tafaɗa tana sakin Mamin
Murmushi Mamin tayi tace
“Welcome My daughter, fatan kin dawo lafiya?”
Tana murmusawa tace
“Lafiya ƙalau Mamina” ina Dady?”
“Ai yanzu yafita”. Mami tabata amsa
Ɓata fuska tayi kana tace
“Shine yafita bayan yasan da zan dawo?”
Mami tace “Ayya Daughter be yi ninyan fita ba, kiran sa akayi daga office yayi baƙi shine yafita but bazai daɗe ba zaki ganshi ai”.
Matashin saurayin me suna Ahmad yace
“Aunty ga jakan ki nan tunda kin manta dani”.
Juyowa tayi tana kallon shi, dariya tayi tace
“Sorry my bro, murnan ganin Mami ne”.
Hugging ɗin sa tayi tasakar masa peck a cheeks ɗin sa
Mami tace “kashigar mata da kayan mana, muje ke kuma kizauna kihuta sai kici abinci ko?”
Langwaɓar da kanta tayi tace
“O’o Mami bari dai in soma wanka, na gaji wlh da yawa”.
“Ok tom je kidawo” cewar Mami sannan tajuya taƙarisa cikin parlour’n, su kuma suka wuce suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan da suke parlour’n, Ahmad yana aje mata trolly ɗin ta yafito yadawo wajen Mami dake zaune cikin parlour’n suka soma hira
Ita kuma bayan tayi wanka tasauya kaya cikin wata ƙaramar riga ja me kwalliyan heart ???? agaban, tasanya blue pencil jeans sannan taɗaura hula akan ta tafito parlour’n, a kusa da Mami tazauna tana faɗin
“Washhh Mamina”.
Mami tace “har yanzu gajiyar ne?”
“Wlh kuwa Mami, kinsan zaman jirgi”.
“To ya Maleysian? Yau dai kin dawo gida komi ya ƙare”.
“Wlh kuwa Mami, kullum fatana naganni na gama karatun nan na dawo gare ku”.
Mami tace “alhmadulillah gashi ai komi ya ƙare, yanzu kije kici abinci kar kuma kin dawo da yunwa”.
Kallon Ahmad tayi tace
“Bro ɗauko min inci anan, bana jin zan iya tashi”.
Dariya Ahmad yayi yace
“Aunty Kausar uwar son jiki, kin dawo kenan”.
Itama dariya tayi tace
“Kai dai bari Baro, but yanzu fa na sauya kar kayi tunanin ko da ne”.
Dawowa yayi riƙe da coolar a hannu haɗe da plate yace
“Ai bazan yarda ba sai naga kin soma aiki”.
Shafa fuskarta tayi kana tace
“Wa ke maganar aiki yanzu?” Tabb ai sai na huta”.
“You see? Dama na faɗa ai, kina jinta ai Mami”.
Mami tace “ai kibar ma wannan maganan, don tuni Dadynku ya samo miki aiki a gidan t.v dake nan garin”.
Waro idanu tayi tana tsayar da hannun ta daga zuba abincin da tasoma tace
“Mami da wuri haka? Ya Dady zai min haka bayan ni ba haka mukayi dashi ba?”.
“Ai sai kibari in yazo kitambaye sa kun fi kusa”.
Kaɗa kai kawai Kausar tayi taci gaba da zuba abincin, yayinda Ahmad yasaki dariya yamiƙo mata spoon yana cewa
“Aunty to meye amfanin zaman naki? Tunda kin riga kin gama karatun ki ai aiki yadace dake, ko kuma kin fi so kiyi aure ne?”
Harara tawurgo masa tana kai abincin bakin ta, sai da tagama taunawa kana takalli Mami tace
“Mami naga anguwar tamu duk tacika da sabbin gini, duk yanzu mun sami maƙota”.
Mami tace “ai kam, ai gine-ginen ma sun jima, don waɗanda ma suke maƙotaka damu sunyi shekaru kusan biyu da tarewa”.
Girgiza kai kawai Kausar tayi, daga nan sukaci gaba da ɗan taɓa hira tana cin abincin ta.
[9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 19*
*4DAYS*
Ƙarfe 10:00pm. Na dare jirgin da yakwaso su Brr. Ibrahim Khalil daga Egypt yasauke su a airport ɗin Katsina, driver’n shi yaje yaɗauko shi, lokacin da suka isa gidan kowa yana barci don ba kowa yasan da dawowan sa ba illa me gadi, bayan sun shiga yafito daga motan yanufi cikin gidan jaye da trolly ɗin sa, ƙofan parlon a kulle yake don haka sai yasaka keey yabuɗe yashiga, duhu ne dumɗun cikin parlour’n, Direct ɗakin sa yanufa yabuɗe yashige tare da rufowa, akan gadon sa yayi ma kan sa mazauni, sai da yaɗau 10mins yana hutawa kafin yamiƙe yasoma rage kayan dake jikin sa yashige toilet, wanka yayi yaɗauro alwala yafito, baƙar jallabiya me hula yasanya sannan yatayar da Sallah, magrib da isha’i yayi, bayan ya idar yayi shafa’i da wutri kafin yamiƙe yahaye saman gado cike da gajiya, babu daɗewa kuwa barci me nauyi yaɗauke sa, wanda be tashi farkawa ba sai da gari yayi haske sosai wajajen ƙarfe 11:03am.