BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Hasken ranan da yashigo ta cikin windon sa ne yabugi fuskar sa, ahankali yasoma buɗe idanun yana rufewa har yaware su gaba ɗaya, take hasken yaƙyalle masa idanu don haka yayi saurin juyawa yaba ma windon baya, 5mins yaɗauka ahaka kafin yamiƙe zaune yana miƙa tare da hamma, ahankali yasanyo ƙafafunsa saman shimfiɗaɗɗen carfet ɗin dake malale cikin ɗakin, bedroom slippers yasaka a ƙafan nasa yamiƙe yanufi toilet, a bakin Toilet ɗin yacire slippers ɗin yashiga bayan yasanya Toilet slippers.
Koda yafito yana ɗaure da towel ajikin sa, ya riƙe ɗaya yana goge suman kan sa, Direct wajen mirror yanufa yasoma shafa Expensive Lotions ɗin sa, bayan ya gama kintsawa yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, brown t.shirt ne me gajeren hannu sai blue jeans yasaka, feshe jikin sa yayi da Parfumer’s ɗin sa masu ƙamshin daɗi sannan yafito parlour hannun sa zube cikin aljihu, dainning yakalla yaga babu komi sai yajuya da ninyan komawa ɗakinsa ɗauko waya, har yariƙe handle ɗin kuma sai yaja siririn tsaki yana juyawa yanufi ɗakin Lubna, ahankali yatura ƙofan yana motsa bakin sa, shashsheƙan kukan ta ne yasoma shiga kunnin sa kafin yasauke idanun sa akan ta, tana zaune a ƙasa ta manne a jikin gado sai takifa kan ta saman gadon, shiru yayi yana kallon ta na tsawon daƙiƙu kafin yakira sunan ta in a cool voice
Dasauri taɗago da kanta face ɗin ta jage-jage da hawaye tasauke idanunta kan shi, sosai tayi mamakin ganin shi don batasan ya dawo ba, shi kam takowa yayi yashigo ciki sosai yana kallon ta yace
“Meke damun ki?”
Ahankali tasunkuyar da kanta ƙasa cikin sanyin muryan ta da be fita sosai tace
“Babu komi”.
“Ke banson ƙarya ki faɗa min abinda ke damun ki nace?” Yafaɗa da ɗan ƙarfi murya a kausashe
Jikin ta har rawa yake yi tace
“Dama wasu ne suka sace min Mamana da ƙannina”.
“Whatt..” yafaɗa da ɗan ƙarfi yana tsare ta da idanu
“Meyasa to?” Yasake jeho mata tambayan
Cikin rawan murya tace
“Dama.. dama sabida sun saka ni aiki ne ban musu ba shine suka kama su”.
Wani kallo yasakar mata kana yace
“Wani aiki kenan?”
“Uhmm hm sun ce ne naɗauko musu duk wani abu da nagani cikin ɗakin ka kamar takardu ko Lapton ɗin ka..”
Sai kuma tayi shiru tana zub da hawaye, Khalil ajiyan zuciya yasauke har yanzu idanun sa akan ta, dama yadaɗe da zargin ta, tun sanda yashigo ɗakin sa yaga ta tsorata hakan yasaka yaɗaura ayar tambaya akan ta, daga lokacin ne yasaka Camera ???? cikin ɗakin sa yana ɗaukan masa duk abinda take yi, wannan dalilin ne yasaka ko kaɗan baya barin ɗakin da yake aje muhimman abubuwan sa aciki abuɗe, but besan da cewa mutanen da suka saka ta aikin sun yi garkuwa da mahaifiyar ta da ƙannin ta bane, sai yaji tsananin tausayin ta ya kama shi, ahankali cikin sanyin murya yace
“Ki dena kuka Lubna, insha Allahu Mahaifiyarki da ƙannin ki zasu dawo gare ki karki damu, ki kwantar da hankalin ki kinji?”
Ɗago kanta tayi tana kallon sa kafin tagyaɗa masa kai tana jin zuciyarta na mata sanyi sosai, bata yi tunanin zai ɗau abin da sauƙi haka ba idan har yagane cin amanar sa take yi, take tasake jin ƙaunar sa na sake shiga cikin zuciyarta
“Bani wayan ki”. Yace hakan yana ciro hannun sa cikin aljihu
Dasauri tamiƙe taɗauko mishi tabashi, amsa yayi kawai yafice, ita kuma tabi bayan sa da kallo tana sauke ajiyan zuciya, zamewa nan ƙasa tayi tazauna tana share hawayen fuskarta
Shi kuma Direct waje yafita yanufi motan sa yashige yafita gidan, kamar ko yaushe yana jan motan ne ahankali yana riƙe da wayan sa ahannu yana neman layin Brr. Tahir, dai-dai zai karya kwana yafita titi yaɗago kan sa don duba hanya, nan yaga wata farar Mota itama ta shanyo kwana kamar zasu yi karo da juna, dasauri yaja burki yana son kaucewa but duk da haka sai da suka gwarawa juna, aje wayan nasa yayi kafin yabuɗe motan yafito dai-dai itama tafito cikin motan ta suka kalli juna, atare kuma suka faɗi
“I’m sorry”.
Hakan yasaka sukayi murmushi kafin ita tace
“Kayi haƙuri bansan da zuwan ka ba ne”.
“No laifina ne ai, nima ban kula ba, but kiyi haƙuri ko”.
Murmushi tayi masa tagyaɗa kan ta
“Babu damuwa”. Tace dashi kana tajuya tashiga motan ta
“Shima ɗin motan nasa yashiga, sai da taja nata motan yawuce kafin itama tawuce, Direct police station yawuce yayi reports ɗin ɓatan mahaifiyar Lubna da ƙannin ta biyu sannan yawuce gidan su.
[9/16/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 20*
Tana kwance saman katifan ta daga ita sai farar doguwar riga irin me taushin nan da zanen flowers ajikin rigan, kanta babu ɗankwali sai gashinta da yawargaje yazubo mata har kafaɗunta, littafi ne a hannunta tana karanta wa tajiyo sallaman ƙawarta daga waje, amsa mata tayi sannan tashigo takalle ta tana faɗin
“Ƙawata hutawa kike yi ne?”
Tashi zaune Halwa tayi tana yatsina fuska tace
“Uhm hutu kuma? Karatu dai nake yi”.
“Yayi makaranciya, kinga ni wlh ban ma bi ta karatun ba don bani da lokaci yanzu, ina Mama naji kamar ke kaɗai ce gidan?”
“Eh Yaya Nura ya kai ta kasuwa”.
“Kai ƙawata wlh baki ga yanda kika sauya ba, wai meye sirrin ne ni naga kamar kina ƙara wani haske ne da kyawu kamar bakijin dawan garin? Ko dai yaya Nura ne?” Zainab tafaɗi hakan tana ƙare mata kallo tare da dariya
Murmushi Halwa tayi, sosai itama take ganin sauyi daga gare ta, tayi wani haske fayau duk da ita ɗin ba fara bace, gashi kuma ko ina nata yaciko gunun sha’awa
“Hmm ke dai ban son tsegumi me kikeson cewa akan Yaya Nura?”
Dariya Zainab tayi tace
“A’a babu komi, kawai dai ina tunanin ko har yafara sauya kulawan sa ne daga gare ki tunda yaga kin kusa zama mallakin sa, kin gane dai irin uhm uhmmm..”
Dukan ta Halwa tayi a cinya tana cewa
“Banson sharri shegiya ke babu abinda kika iya sai saka idanu, yanzu me kikazo yi ne don nasan ba banza takawo ki ba?”.
Waro ido Zainab tayi tace
“To me kike nufi? Ko nace miki wani abu nazo amsa wajen ki? Kinga ni tare da Safna muke zamuje gidan aunty Zaituna, shine nace bari in shigo ko zamuje tare sai gashi Mama ma bata nan”.
Halwa tace “wato da Safna ma kuke taƙi shigowa? Lallai kam zataci uban ta wlh dani take zancen”.
Zainab tace “ni fa bana faɗa miki bane kije kuyi halin naku”.
“Ai kibar ni da ita zamu haɗu ne wlh, kuma kisanar da ita hakan”.
“Baki da ƙafa ne? Kifito kije kisame ta mana”. Zainab tafaɗi hakan tana nufan ƙofa zata fice
Gyara zaman ta Halwa tayi taɗau littafinta tana faɗin
“Banda lokacin ku yanzu, sai mun haɗe a school”.
Zainab tace “Allah yakai mu to” sannan tafice da gudun ta
Kifa littafin Halwa tayi saman katifan tabi kai takwanta tana sakin numfashi, shiru tayi tana tunani aran ta, abun da yafaru da ita kwanaki 8 da suka wuce ne yadawo mata cikin ranta, take hawaye masu zafi suka soma sulmiyo mata a fuska