Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Har yaushe ne zata dena tuna wannan abinda yafaru da ita? Yaushe ne zata manta da wannan baƙin ranan acikin sauran ranakun da tayi a doron ƙasa? Har yaushe ne zuciyarta zata dena shiga cikin wannan ƙunci da baƙin cikin?”

“Ya Allah gani gare ka, ya Allah kabi min haƙƙina akan wannan azzalumin, haƙiƙa yazalunce ni yasaka min tabon da bazan taɓa iya cire wa ba, Allah ya isa tsakanina dashi bazan taɓa yafe masa ba har duniya tanaɗe”.

Tafaɗi hakan afili tana saka bayan hannunta tashare hawayen fuskarta.

***** ***** ********

*AFTER THREE DAYS*

Fitowa yayi daga ɗakin sa hannun sa riƙe da waya, yasami waje saman kujera yazauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayan sa yasoma latsawa yana yi yana ɗan ɗago kan sa yana kallon t.v, Lubna ce tafito daga kichen riƙe da coololi a hannun ta, dainning tanufa tajera kana tasake komawa taɗauko wasu su ma tajera su, bayan ta gama tanufi inda yake zaune ahankali tace mishi

“Na gama girkin, ko akwai wani abu?”.

Girgiza mata kai kawai yayi idanun sa a kan wayan sa, juyawa tayi tanufi ɗakin ta, shi kam sai da yafi 10mins kafin yamiƙe yanufi dainning ɗin yazauna, aje wayan nasa yayi yasoma buɗe coololin abincin yana taɓe baki, gaba ɗaya babu abinda yayi masa aciki don baya tunanin zai iya sanya wani abu me nauyi acikin sa, rufewa yayi yatashi yanufi kichen, babu daɗewa yadawo hannun sa riƙe da glass cup ya haɗa Black tea, direct dainning table ɗin yakoma yaɗau wayan sa yadawo cikin parlour’n yazauna yasoma sipping tea ɗin yana kallon t.v, ahaka har yagama kafin ya’ajiye cup ɗin saman Centre table yaɗau remote yasoma sanja Channels, har yasaka wani tasha me suna *ƳAN CI T.V* yana shirin sauyawa aka nuno fuskar ta, hakan yasa yatsayar da tashan yana ƙure ta da idanu, duk da ba sosai yakalli yarinyan ba but zai iya shaida itace wacce sukayi karo a kwanakin baya, tana sanye ne cikin wata baƙar abaya me ɗan karen kyau da tsada, ta yane kan ta da Black veil, kasancewar ita fara ce sosai tayi kyau cikin kayan, tana gabatar da shirin ta kamar haka:

“Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa acikin sabon shirin mu na *RAYUWAR DUNIYA,* wacce ni Kausar Ali Aliyu zan riƙa kawo muku aduk ranan Litinin da Alhamis, shiri ne dake kawo muku abubuwan dake faruwa acikin duniyar mu, tare da bankaɗo muku duk wani abinda ke ɓoye don kusani…”

Ahankali yalumshe idanuwan sa yana jingina kan sa saman kujeran, yana jin muryan ta na ratsa cikin kunnen sa, sai kuma yabuɗe idanun sa yasake saukewa akan fuskarta, sosai yarinyan yaji ta burge shi, rana ta farko kenan da yaji mace tabashi sha’awa har be san sanda yadunga murmusawa ba, yanda take gabatar da shirin ta da komi nata a natse ne

Wayan sa da yasoma ringing ne yasaka shi ɗan ɗago kai yana kallon wayan, ganin sunan DPO na yawo a screan ɗin wayan, hakan yasaka shi miƙa hannu yaɗau wayan tare da rage volume ɗin t.v’n yana karawa a kunne, basu fi 5min suna wayan ba yacire Phone ɗin a kunnin sa yamiƙe yanufi ɗakin sa, Direct sif ɗin sa yawuce yasauya kaya zuwa milk colour ɗin riga me dogon hannu, rigan kamar Jaket ne da coller a wuyan, but sai dai bata da nauyi ƴar shugula ce, wandon sa pencil ne kalan blue Black, sai yasaka Combat shi ma kalan wandon da igiyar shi milk, sosai yayi kyau cikin shigan yafeshe jikin sa da Expensive Parfumer’s ɗin sa me shegen ƙamshi, yaɗau wayoyin sa da car keey’s yafice, yana fita Compound ɗin gidan yashiga cikin motan sa ash colouer yabar gidan.

…… ……. ………

Yana zaune a office ɗin DPO yana mishi bayani kamar haka:

“Ah BARRISTER a binciken da mukayi na daga ɓatan Matar da kakawo mana, ahm lokacin da kabamu report mun je wajen gidan ka don gudanar da binkice anan muka haɗu da wani mutum yana leƙa gidan ka, dama numban da kabamu mun riga da mun duba sai dai akashe yake kuma an datse hanyar sadarwan shi, to wannan dai mutumin mun kamashi don bamu yarda dashi ba, don haka koda muka kawo shi nan muka saka shi yayi bayani sai yayi mana taurin kai, sai da muka bashi wahala tukun yafaɗa mana abinda yasani, yace “shine wanda yake gadin Matar da ƴaƴan ta, sannan yazo gidan ka ne saboda aiko shi da akayi wajen ƴarinyan Matar da take gidan ka, munyi-munyi yayi mana bayani akan mutanen da suka saka shi aikin but yace “shi be san su ba, shi dai kawai an saka shi yatsare su ne”, kaji abinda yafaru, but duk da haka dai muna tsare dashi ko zamu sami wani inpermation akan su”.

Gyara zaman sa da kyau Khalil yayi yana kallon DPO ɗin yace

“Yanzu ina suke?”

“Suna nan mun aje su a wani ɗaki, zaka iya tafiya dasu yanzu haka but ko wani lokaci zamu iya neman su”.

“Ok babu matsala ai”.

Miƙa mishi hannu yayi sukayi musabaha kafin suka miƙe atare suka fice.

       Bayan kamar minti goma Khalil yafito cikin station ɗin, bayan sa wata dattijuwar mata ce da matasan yara maza su biyu, buɗe musu mota yayi suka shiga sannan yakulle shima yashiga yaja yatafi, Direct gidan sa ya’isa, bayan yayi parcking yasake buɗe musu suka fito yace “su biyo bayan shi” babu musu suka bi shi a baya har cikin parlour’n, zama yayi bayan da yace

“Umma kuzauna mana”.

“Toh”. Cewar matar sannan suka zauna

Wayan sa yasaka yakira Lubna sai gata tafito, ai tana cin karo dasu tasheƙo da gudu tana kiran “Ummana”, rungume Umman tayi tasaki kuka, su ma ƙannin ta suka rungume ta duk suka fashe da kuka, Khalil kallon su kawai yake yi yana murmushi cike da tausayin su, sai da suka gama rungume-rungumen junan da koke-koken kafin Lubna taɗago kanta fuska a jiƙe takalle shi tace

“Nagode Sir, ban san da bakin da zan maka godiya ba, na gode sos..”

“Shiiiiihh ya isa haka, kibasu abinci suci su huta sai ki kira ni bayan sun gama ok?”

Gyaɗa masa kai tayi tana share hawayen ta, shi kuma tashi yayi yashige ɗaki yarufo ƙofan, ahankali ya’isa gaban gadon sa yazauna tare da jinginar da kan sa a jikin gadon, rufe idanuwan sa yayi yana jan iska da ƙarfi yana fesar wa, tunanin abinda yakamata yayi kawai yake yi, tsawon lokaci kafin yaji wayan sa tana ringing, Koda yaduba yaga Lubna ce sai yamiƙe kawai yafice

Kallon Umman yayi bayan da yazauna yace

“Umma kuna da wasu ƴan uwa ne a wani wajen, ko dama anan kuke zaune?”

Umma tace “a’a muna dasu a ƙauye, dama mu ma can muke zaune sanadiyan aiki ne muka dawo nan muka kama haya”.

Gyaɗa kan sa yayi kana yace

“To Yakamata ki ɗauki ƴaƴan ki gaba ɗaya kubar nan, ko ki koma ƙauyen ko kuma ku sauya wani waje me nisa, sabida mutanen da sukayi garkuwa daku ko wani lokaci zasu iya dawowa gare ku”.

Sannan yamayar da idanun sa kan Lubna wacce itama kallon shi take yi yace

“Kije kihaɗa kayan ki”.

Daga haka yamiƙe yakoma ɗakin sa, ita kam Lubna kasa riƙe kukan da yazo mata tayi tasake shi ahankali, Umman nata tace

“Ai hakan yadace muyi Lubna, wlh ko be ce mubar nan ba baza mu sake kwana ba, ai Allah mun gode maka da yataimake mu da bamusan me mutanen nan zasu yi mana ba, kitashi kije kihaɗa kayan ki mutafi”.

Babu musu tamiƙe tashiga ɗaki, lokacin da tafito riƙe da trolly ɗin kayan ta shima Khalil yafito yana kallon ta, sauke kanta ƙasa tayi hawaye na zubo mata, bazai iya juran ganin hawayen ta ba don haka yaɗauke kan sa yanufi wajen Umma yace

“Ga wannan Umma, da fatan zai ishe ku ko da sana’a ne sai ku kama”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button