Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

Jiki na rawa Umma tasaka hannu ta’amshi maƙudan kuɗin da yamiƙo mata

“Har da ɗawaniya ɗan nan? To mun gode Allah yasaka da alheri, Ubangiji yabiya maka duk kan buƙatun ka, mun gode ƙwarai da gaske”.

Murmushi kawai Khalil yayi yana motsa laɓɓan sa, yana nan tsaye har suka fice kana yasami waje saman kujeran yazauna, lumshe idanuwan sa yayi yana tuna ranan da Mom ɗin shi takawo mishi Lubna a matsayin ƴar aiki, wacce zata riƙa taimakon shi da gyaran gida

Asali ita Umman Lubnan itace ƴar aikin Mom, daga baya ne tayi wani ciwo da yakwantar da ita tsawon lokaci har ta’ajiye aiki Mom kuma tasamo wata, lokacin bayan Umma ta sami sauƙi sai tazo wajen Mom tane mi alfarma ta samar ma Lubna aiki, shine ita kuma Mom tace “Khalil yaɗauke ta yatafi da ita, tunda dole yana buƙatar wacce zata riƙa dafa mishi abinci da sauran abubuwa na gyaran gida” babu musu Khalil yatafi da ita, wannan shine dalilin da yasaka LUBNA take aiki a gidan sa, kuma a gidan nasa take kwana but wani lokacin kuma tana komawa gidan su, musamman kamar ranan Weekends haka.

Ajiyan zuciya yasauke yana buɗe idanun sa, gyarawa yayi yakwanta a kan kujeran yasake lumshe idanun sa.

[9/16/2020, 8:26 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 21*

Kiran sallan magriba ne yasanya shi buɗe idanun sa da suka yi ja sakamakon barcin da yaɗauke shi, ahankali yamiƙe yanufi ɗakin sa, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, as usual sai da akayi sallan isha’i yadawo gida, Direct ɗakin sa yawuce yacire rigan sa yabar singlate ɗin dake jikin sa, drower yabuɗe yaɗauko keeys sannan yarufe, yaɗau briefcase ɗin sa yafito parlour, akan 2sitter yazauna yana ajiye briafcase ɗin saman Centre table, wayan sa yaɗauka sai da yalatsa kafin yakara a kunne, yana jin an ɗauka yace

“Kazo ina neman ka”.

Daga haka yacire wayan ya’ajiye, buɗe jakan yayi yaciro Computern sa yasoma aiki

Da sallama wani matashin saurayi yashigo ciki, amsa masa sallaman yayi batare da yaɗago daga abinda yake yi ba

“Gani Sir”. Cewar saurayin bayan da yaduƙa gaban sa

Ɗago kai yayi yana kallon sa yace

“Sale daga yau aikin ka zasu ƙaru agidan nan, zaka riƙa zuwa kana gyara min cikin gidan nan, don haka zan ƙara maka albashi in babu matsala”.

Washe baki Sale yayi yace

“Ai babu komi Sir duk zan iya, har da ma abun da bakace ba”.

“Ok.. ga keeys ɗin gidan sai kariƙe a hannun ka ko”.

Hannu biyu yasa ya’amsa

Yace “katashi kaje”.

Miƙewa Sale yayi yana godiya kafin yatafi, shi kuma yaci gaba da aikin sa, wajen ƙarfe 09:00pm. Yadakata kasancewar yunwan da yaji yana ƙwaƙulan cikin sa, miƙewa yayi yanufi kichen, tsayawa yayi yana nazarin abinda zai ci domin sosai yaji cikin sa na kukan yunwa, don haka kawai yayanke shawaran dafa indome, cikin abinda be gaza minti 12 ba yagama, indome ne haɗe da ƙwai yasoya yaɗauka yafito, zama yayi yasoma ci ahankali yana tunani har yagama, yatashi yamayar da plate ɗin da spoon cikin kichen sannan yadawo yaci gaba da aikin sa, sai wajen ƙarfe 12:04pm. Sannan yanufi ɗakin sa, sai da yaɗauro alwala yagabatar da sallan nafila tukunna yasauya kayan sa zuwa kayan barci yakwanta.

Washe gari ƙarfe 06:45am. Tuni yagama shirin sa na zuwa office, suit yasanya sky blue da ƴar cikin milik colour, sosai yayi kyau babu abinda yake yi sai tashin ƙamshi, yaɗau briafcase ɗin sa yafice, a farar motan sa yashiga yabar gidan.

Ƙarfe 02:30pm. Yadawo gida, yana shiga cikin ɗakin sa ya’ajiye briafcase ɗin sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafan sa da socks, bayan ya gama yacire suit ɗin tare da necktie ɗin wuyan sa duk yazube saman gado, miƙewa yayi yashiga Toilet, be daɗe ba yafito yanufi parlour, kichen yawuce yahaɗa tea me kauri yazauna nan yasoma sha, bayan ya gama yafito yakoma ɗaki yacire kayan sa yashiga wanka

Lokacin da yafito yashirya cikin wani ɗanyen Boyel maroon colour, ba ƙaramin kyau suka yi masa ba kamar wani sabon ango, yafeshe jikin sa da farpume’s yakwashi wayoyin sa da keeys ɗin mota yafice, mota yashiga yabar gidan, Direct super makert yawuce yayi shopping masu yawan gaske, yahau motan sa yanufi gidan ɗan uwan sa

Lokacin da ya’isa yana yin hon aka buɗe masa motan yakutsa ciki yayi parcking, yanayin gidan da komi irin nasa ne, sai dai ɗan abinda ba’a rasa ba, yana fitowa me gadi yanufo sa da gudu yana kai gaisuwa tare da taimaka masa yashigar da kayan, a parlour ya ajiye masa, shi kuma yaciro kuɗi yabashi yana ta godiya sannan yafita, zama yayi saman sofa yana sauke idanun sa akan plasma dake aiki shi kaɗai babu kowa, yafi minti 5 da shigowan sa be ji wani zai fito ba, hakan yasaka yaɗau wayan sa yasoma latsawa yana neman layin Sameer, sai ga Abida tafito, ƙanwa ce ga matar Sameer ɗin, tana hango shi tanufo wajen shi cike da fara’a tana faɗin 

“Laa Ya Khalil yaushe kashigo?”

Ɗago kan sa yayi yakalle ta kana yace

“Yanzu”.

“Sannu da zuwa to”.

“Yauwa, ina masu gidan?” Yatambaye ta yana mayar da idanun sa kan wayan sa

Murmushi tayi tana zama akan hannun kujeran da yake kai, kana tace

“Suna ciki, ko in Kira su?”

Gajeren tsaki yaja batare da yace mata komi ba, yana ganin rainin hankali ne, har sai yace ma takira su zata kira mishi su? wayan sa yakara a kunne yana faɗin

“Bro gani a gidan ka fa”.

Abinda yafaɗa kenan yakatse kiran, ita kam Abida kallon sa kawai take yi tana murmushi, sosai take ƙaunar Khalil sai dai ko kaɗan shi baya sakar mata fuska, ko tayi yunƙurin shiga jikin sa to baya bata dama

Sameer ne da Hakima suka fito daga ɗakin su, sun ci ado cikin wani farar kamfala iri ɗaya har aikin

“Uhmm ai wlh nayi fushi ba kaɗan ba, wai ace tun yaushe kadawo ƙasan nan har akayi suna bakazo ba sai yanzu?”

Cewar Hakima tana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlour’n, yayinda shima Sameer yasami gefen ta yazauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kyakykyawar murmushin sa yayi kana yace

“Afwan Matar Bro, I know nayi laifi, amma sai da nace ma Bro yafaɗa miki uzurina, ko ba haka muka yi ba Bro?”.

“O’o niii? Kar kahaɗa ni da matata, a yaushe mukayi haka da kai?” Cewar Sameer ɗin yana ɗaga hannaye sama tare da fito da idanuwan sa

“You see ka gani ko? Ai nasan Mijina bazai maka ƙarya ba, kai dai kawai bakayi ninyan zuwa ba sai sanda kaga dama”. Hakima tafaɗi hakan tana murmusawa

“To yanzu dai first kifara ɗauko min My son nagan shi sai aci gaba daga baya”.

“Hmm ai yayi fushi shima bazai gan ka ba”.

“Haba Matar Bro Ni ne fa ko kin manta ni? Bro kasaka baki mana”. Khalil yafaɗi hakan yana langwaɓar da kan sa kamar ƙaramin yaro

“To sweetheart ki yafe masa tunda naga kamar yayi nadama, but nest in yasake ki hukunta shi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button