BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Tunda suka fito daga asibitin suka shiga cikin keke napep Halwa take faman kuka, duk ta takure waje ɗaya ta rufe fuskarta da Hijab, Mama kuwa itama tunda tazauna taɗauke kai gefe, maganganun Doctor kawai suke dawo mata cikin kunnen ta, zuciyar ta sai wani irin tafarfasa take yi ƙiris take jira, suna kai wa tasauka tabashi kuɗin shi tashige gida dasauri, Halwa kuwa ahankali tasauko tanufi gidan nasu, sai dai takasa shiga ciki sai tatsaya a zaure tana ta kuka, tana nan tsaye a wajen sai ga Baba da Nura sun shigo atare, suna ganin ta sukasan babu lafiya, domin Mama takira su a waya tace su dawo yanzu, kuma bata faɗa musu abinda ke faruwa ba, Baba ne yasoma cewa
Bata ɗago kai ba sai ma ƙara volume ɗin kukan ta da tayi, nan da nan jikinta yasoma rawa kamar an sakata a shocking, Nura zuwa yayi yariƙo ta yana faɗin
“Lafiya Halwa? Menene haka wa yabige ki?”
Still shima shiru tayi masa
Baba yace “Nura taho da ita mushiga gidan sai muji ba’asi wajen Maman taku”.
Riƙo ta kuwa Nura yayi, babu musu tabi shi suka shiga ciki, ɗakin Mama suka nufa gaba ɗayan su, Mama na zaune tana faman hawaye suka shigo, abinda yaƙara ɗaure musu kai kenan suka hau tambayan ta “lafiya?” Hankalin su duk atashe, but Mama taƙi tayi magana sai Hawayen ta take yi, zama Baba yayi gefen ta yayinda Nura ma yasamu waje yazauna yajanyo hannun Halwa itama tazauna kusa dashi
Baba yace “wai Hauwa lafiya muka ganku a wannan yanayin? Meke faruwa ne kiyi mana bayani?”
Ɗago kan ta tayi cikin baƙin ciki tace
“Wani bayani kakeso kaji Baban Nura? Ace wai yau Halwa ce tayo mana ciki agida, cikin shege fa Halwa tayi a gidan nan”. Sai tasake fashewa da kuka
Atare Baba da Nura suka maimaita cikin Shegen, Nura har da ja da baya yana matsawa kusa da ita, cikin kaɗuwa Baba yakalli Halwa da har yanzu takasa buɗe idanun ta yace
“Dagaske ne cikin Shege kikayo min agida?”
Shiru Halwa tayi
“To ya za’a yi tafaɗa maka? yanzu muka dawo daga asibiti likita yatabbatar mana tana ɗauke da cikin Shege acikin ta, to wlh tallahi ba dai nan gidan ba, bazai taɓa saɓuwa ki haifa mana ɗan Shege agidan nan ba, duk gatan da mukayi miki Halwa kikasa saka mana da abun kirki sai abun tsiya? ashe duk zaman da muke yi dake amanar mu kike ci mu duk bamu sani ba? To baza mu ga wannan abun kunyan ba dole ki koma can dangin mahaifin ki tunda bakisan halacci ba, na rabo ki da can ne don naga kina shan wahala amma kin nuna mana ke ba mutumiyar arziƙi bace”.
Baba ya’amshe zancen cikin sauri yace
“Ni Malam Ayuba za’a zubar min da mutunci agida? da ƙima ta da daraja ta yau za’a haifa min shegen ciki?”
Halwa kuwa in banda kuka babu abunda take yi, sosai zuciyarta takaɗu da kalaman Maman nata, “wanna wace irin baƙar rana ce tazo mata?” Meyasa duniya take son juya mata baya?”
Baba yaci gaba da faɗin
“Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za’a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba dole kibar min gida, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji, in kin shirya kizo ki amshi kuɗin mota”.
Ɗago kanta Halwa tayi da idanuwanta suka kaɗa sukayi jazur sukayi luhu-luhu, cikin tsananin kuka tace
Don girman Allah Mama kuyarda dani wlh Fyaɗe akayi min, Yaya Nura ma ya sani wlh ban taɓa sanin wani namiji ba..”
Dasauri Nura yace “keeee Halwa sharrin kuma kaina zai koma? Aina nasan anyi miki Fyaɗe? Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake”.
A firgice takalle shi sai dai takasa furta komi sabida zallan mamaki da kuma rawan da bakin ta yake yi, shi kuma Baba cikin ɓacin rai yace
“Halwa wato so kike yi kidangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?”.
Girgiza kan ta kawai take yi tana hawaye, ita har yanzu takasa yarda da cewa Yayan ta Masoyinta shine yajuya mata baya yake faɗan kalman ɓatanci akan ta, takasa yarda Mama da Baba zasu ƙi yarda da ƙaddaran da yasaukar mata
“Ya Allah.. meke shirin faruwa da ni ne? Wayyo Allana ko dai mafarki nake yi?”.
“Abinda kika aikata ne yake bibiyanki Halwa, kitashi kiwuce kibar mana gida, wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe ki”. Mama tafaɗi hakan tana sake fashewa da kuka, cikin kukan take faɗin
“Allah mun gode maka da ɗana be auri mazinaciya ba, da yanzu anyi auren shikenan kin cuce shi”.
Tsawa Baba yasake daka mata babu shiri tamiƙe tana dafe da kanta dake faman sara mata kamar zai rabe gida biyu tafice, bata iya tsayawa ko ina ba Direct waje tanufa, sabida gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta sun gushe, maganganun Nura kawai suke dawo mata cikin kunne
_”Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar Soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake”_
Hannu biyu tasanya tatoshe kunnuwan ta tana wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, kuka take yi sosai da har yasa bata iya ganin gaban ta, sabida yanda hawayen suke ambaliya kamar an kunna famfo, har yanzu takasa yarda da cewa abinda ke faruwa da ita a yau ɗin gaske ne, so take yi kawai tafarka daga wannan mummunan mafarkin, tasan dacewa Mama, Baba, Nura bazasu taɓa juya mata baya haka ba
Wani lungu tasamu tazauna nan tana ta rizgan kuka har muryan ta yadena fita, sai hawaye da suka ƙi ƙafewa a idanun ta, ta jima a wajen tana son ko wani ne yazo yatashe ta yace mata “Mafarki ne Halwa”. Sai dai babu wanda yagibta tun zaman ta, haka tatashi takoma wajen gidan nasu tatsaya tana kallon gidan, idanun ta fal da hawaye, zuciyarta na wani irin bugawa kamar zai faso yafito
_”Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci, duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za’a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji”_
_Wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe kiiiiiii”_
_”Wato so kike yi ki dangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?_
_Ki tashi kiwuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida”_
Maganganun su ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwan ta, Wani abu ne yazo yatokare mata wuya batasan sanda taƙwallara ƙara ba tazube nan tana fashewa da sabon kuka, bata taɓa tunanin ita ɗin marainiya bace sai yau
“Wayyo Allana na shiga uku na lalace, meyasaka zakuyi min haka? Bakusan cewa wannan shine ƙaddara ta ba? Ya zan yi in kauce masa?” Meyasa? Meyasaka Yaya zaka juya min baya bayan kasan komi? Meyasaka ka aikata min haka duk da kasan abun da yafaru agaban ka akayi komi? Shin ko ka manta soyayyar dake tsakanin mu ne? Ka manta ni ce Halwa Halwan ka kuma ƙanwar ka? Dan Allah kafito kaban amsa Yaya, kazo kafaɗa min dalili”.
Wasa-wasa Halwa tazama tamkar mahaukaciya a wajen, gaba ɗaya tagama fita hayyacin ta, kuka kawai take yi, kukan da babu hawaye a yanzu bare kuma murya, ta jima anan wajen kuma ikon Allah babu wanda yafito suna can suna jajanta abun da yafaru