BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Congratulations, na gode sosai da taimakon ka gare Ni, haƙiƙa bazan taɓa mantawa da kai ba, thank you so much BARRISTER”.
Still yana murmusawa yace “Babu komi Fadila, yanzu yaushe zaki koma gida?”
Ɗan fari tayi da idanu tace “yanzu”.
“Ok sai kin kawo mana ziyara kenan?”.
Murmushi tayi tace “insha Allahu”.
Daga nan sallama sukayi kafin yanufi wajen motan sa inda su Sameer da su Mom tare da su Brr. Tahir suke jiran sa, yana isowa Sameer yaja kumatun sa yace
“Ɗan ƙanina na tayaka murna”.
Dariya gaba ɗayan su sukayi kafin sukayi sallama duk suka shiga motocin su ganin Ƴan Jarida na damun su, suka bar wajen.
[9/30/2020, 10:43 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~Wattspp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 33*
Halwa ce zaune saman gado kusa da na Saleema dake barci har yanzu bata farka ba, but yanzu babu Oxgyen da aka saka mata sabida Numfashin ta ya dai-daita
itama Halwan an sanya mata drip a hannun ta, Ummi dake zaune saman kujera tana yanka Lemo cikin plate, bayan ta gama sai taɓare ayaba shima duk tajera akan plate ɗin tamiƙa ma Halwa tace
“Riƙe kisha wannan nasan zai fi miki, bazaki zauna haka tun safe baki ci komi ba”.
Babu musu Halwa ta’amsa tasoma ɗauka tana sha, Nurse ce tashigo da sallaman ta taƙariso wajen su tana cewa
“Ya jikin naki? Da fatan yanzu kina jin ƙarfi sosai ajikin ko?”
Gyaɗa kai Halwa tayi tana kallon ta
“Ok gashi wannan maganin ki ne zaki riƙa sha a rana sau biyu, Allah yasauwaƙe”.
Ummi ne ta’amshi maganin tana cewa “Ameen mungode”.
Matsowa tayi tagyara mata ruwan kafin tafito da allura cikin aljihun ta tasoma haɗawa tana faɗin
“Har yanzu ita bata farka bane?”.
“Eh”. Ummi ta’amsa mata tana kallon Saleema”.
“Ok idan ta farka Sister Asma’u sai ki sanar da Doctor ɗin”.
Ummi tace “ok ba matsala”.
Alluran tatsira cikin Drip ɗin Halwa kana tayi musu sallama tafice, ruwa Ummi tamiƙo mata tare da ɓallo maganin shima tamiƙa mata tace
“Gashi kisha, amma kiyi sauri kishanye Fruits ɗin kinsan babu komi acikin ki”.
Gyaɗa kanta tayi ta’amsa maganin tazuba a baki tana runtse idanu kafin takora da ruwa, daƙyar ta iya haɗiyewa tana sakin nishi, murmushi Ummi tayi tace
“Da alamu bakison magani ko?”
Itama Halwa murmushin tayi tana sauke kanta ƙasa
“To yi sauri kishanye mana”.
Ci gaba tayi da shan Fuirts ɗin har tashanye, Ummi ta’amsa plate ɗin ta’ajiye, gyara zaman ta tayi tana kwanciya tare da rufe idanun ta, barci take ji sosai kasancewar Alluran da akayi mata cikin Drip ɗin na barci ne coz ana son tasamu hutu sosai, babu jimawa kuwa barci yayi awon gaba da ita, koda Ummi tayi magana taji shiru hakan yatabbatar mata da barci ya ɗauke ta, tashi tayi takoma saman kujerun dake ɗakin taɗau remote tana sauya tasha, a *ƳAN CI T.V* tabari tasoma kallon Labaran da ake nunawa na hukuncin da aka yanke akan su Alh. Mubarak, in banda girgiza kai babu abinda Ummi take yi.
Tsawon awa ɗaya kafin ruwan da aka saka ma Halwa yaƙare, har wannan lokacin kuma acikin su babu wacce tafarka, tashi Ummi tayi tacire mata Drip ɗin kana tashiga Toilet tayi alwala tafito, fita tayi babu jimawa tadawo riƙe da dadduma, sallan la’asar tayi, bayan ta idar tana zaune tana lazimi Abba yashigo, ƙarisowa yayi yazauna yana kallon ta, itama ɗago kanta tayi tai masa sannu da zuwa, amsawa yayi yace
“Yakamata ki koma gida sai in zauna dasu, tunda yau ba aiki zakiyi ba”.
Ummi tace “a’a Abban Saleema babu abinda zan yi ko na koma gida, nasan tunda akwai Larai zata kula da komi, kuma zata kawo mana abinci nan tunda tasan muna nan ɗin”.
Gyaɗa kansa yayi yace “ok shikenan, bari ni inje yanzu zan dawo insha Allah, idan ƴar Baba tatashi ki kira ni awaya idan ban dawo ba”.
“Toh”.
Daga nan tashi yayi yafice ita kuma taci gaba da lazimin ta.
***** ******* ***********
Shigowan sa kenan cikin gidan nasa, tun gama shari’an gaba ɗaya suka wuce gidan su sai yanzu yadawo, ahankali yabuɗe ɗakin nasa yashiga, aje komi yayi tare da cire kayan jikin sa yawuce cikin Toilet wanka yayi sannan yafito, ko mai be shafa ba yaɗauko kayan sa ƙaramar riga fara da dogon wando robber shima fari yasaka, fitowa Parlour yayi yazauna saman 3sitter, wayoyin sa da suke kashe duk ka biyun yaɗauka yakunna, saƙonni ne suka soma shigowa, sai da suka gama gaba ɗaya sannan yasoma buɗe wa yana gani, duk yawanci Abokan sa ne da waɗanda yasani suke tayasa murna, be fi guda goma yabuɗe ba yamayar da wayan ya’ajiye tare da kwanciya yana ɗaura hannun sa ɗaya saman fuskar sa yalumshe idanun sa, ya ɗau tsawon awanni yana ahaka, babu abinda yake yi sai tunani, sai da yaji kiraye-kirayen sallan Magriba kafin yamiƙe a kasalance yashiga Toilet ɗin dake parlour’n yaɗaura alwala yatafi masjid.
*** ***** **** ****
*BAYAN KWANA BIYU*
A kwana biyun nan sosai jikin Saleema yayi sauƙi, don haka aka sallame su suka koma gida, gaba ɗaya Ummi tahaɗa su tana basu kulawa kasancewar har alokacin itama Halwa sosai take fama da jikin ta, laulayi ya sako ta gaba ko abinci sai anyi dagaske take ci, gaba ɗaya ta rame sai haske da tayi, komawar su gida ma sai da Ummi tasake saka mata Drip sabida yawan aman da take yi.
Yanzun ma kwance take saman gado, duk ta ƙudundune jikinta cikin bargo tana ta rawan ɗari, Saleema kuma na zaune gefen ta tabuga uwar tagumi tana kallon ta, fuskarta ya nuna damuwa sosai kamar tayi mata kuka, cikin tsananin tausayawa tace
“Wai meyasaka baza’a cire cikin bane? Kina shan wahala da yawa..”
Ummi da shigowar ta ɗakin kenan taji maganar da Saleeman take yi tayi saurin katse ta
“Kull.. kar in sake jin kin bata wannan shawaran, bakisan haramun bane zub da ciki? Bana son in sake jin kin faɗa mata hakan kinji ni?”
Gyaɗa kanta Saleema tayi tace “Toh Ummi”.
Zama Ummin tayi tana ajiye Coolarn da tashigo dashi tare da plate tace
“Tashi kici abinci Halwa, Faten wake ne nasanya akayi miki nasan zakiji daɗin sa kinji? Tashi maza kici”.
Saleema tace “to Ummi kawo in zuba mata”.
“Ai har dake zakici, in kun gama sai kusha maganin ku ni zan tafi asibiti, sannan nasaka Larai tayi muku Farfesun kayan ciki, shima sai kuhaɗa dashi kuci, ni natafi ku kula da kanku sosai kunji?”.
Gyaɗa mata kai sukayi, daga nan ficewa tayi bayan Saleema tayi mata “adawo lafiya”. Tana fita Saleema tabuɗe Coolar’n tazuba musu Faten waken da yaji nama sai tashin ƙamshi yake yi, kallon Halwa da har yanzu take kwance tayi tace
“Tashi muci”.
Sai kuma ta’ajiye abincin a ƙasa tana matsowa kusa da ita tataimaka mata tasauko, zama sukayi a ƙasa suka soma ci, Halwa bata wani ci sosai ba tamatsa gefe tana ɗan sakin nishi, Saleema kallon ta tayi tana shirin yin mata magana sai taga tasoma kwarara amai, dasauri tamatsar da abincin tamiƙe tana riƙo ta ganin tana shirin faɗuwa, sai faman sannu take mata kamar zatayi mata kuka, sai da ta amayar da duk wani abinda ke cikin ta sannan tatsakaita tana numfarfashi cike da galabaita, taimaka mata Saleeman tayi suka shiga Toilet tawanke jikin ta kafin suka fito, zaunar da ita saman gadon tayi takoma Toilet ɗin taɗauko kayan Moping tawanke wajen tare da sharewa, sai tadawo tazauna tana kallon Halwan da itama tazuba mata idanu tana jingine jikin gadon, murmushi tasakar mata cikin sanyin murya tace