Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Na.. go..de”.

Waro idanu Saleema tayi tana mata alama da hannu “na mene?”

“Bansan da me zan saka miki ba, kin taimaki rayuwata sosai, kin zame min ƴar uwa alokacin da narasa kowa nawa, sannan kin kawo ni gidan ku kin maishe da ahalin ki ahalina, wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba, haƙiƙa bazan taɓa manta ki cikin rayuwata ba, daga yau kece komi nawa kuma insha Allahu zan ɗauke ki ƴar uwa kuma wacce zata maye min gurbin ƙawata Zainab”.

Runtse idanun ta tayi jin hawaye na son zubo mata, Sai kuma tabuɗe tana murmushi tace

“Daga yau bazan sake kewarta ba tunda har nasami madadin ta”.

Riƙo hannun ta Saleema tayi itama tana murmusawa tace

“Ki dena faɗan haka, Ni nayi ne duk sabida Allah, sannan naji daɗi da kika ɗauke Ni ƴar uwa ƙawa, dama na daɗe ina jiran ranan da zan sami tawa ƴar uwan, sai gashi Allah yabani ita har gida”.

Sai kuma tasaki dariya har haƙoran ta suna bayyana, tamiƙe tsaye tana faɗin

“Bari in amso mana ferfesun sai ki ƙara ci tunda kin amayar da wannan da kikaci, ina zuwa”.

Daga haka fita tayi dasauri, bata jima ba tadawo ta’ajiye musu a saman gadon, sai taɗauko maganin Halwan dake ajiye a kan drower tadawo tazauna, nata tabuɗe taɓalla tasha tare da korawa da ruwa, sai takalli Halwa tana sakar mata murmushi tace

“To kema kici sai kisha maganin ko?”

Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tashare hawayen da suka sulmiyo kan kuncin ta batare da Saleeman tagani ba, bayan ta ɗan ci kaɗan sai tasha maganin sannan taci gaba taci, Saleema kuwa cire hannun ta tayi tana yin gyatsa tare da faɗin

“Alhmadulillah Ni dai na cika cikina, saura ke”.

Kallon juna sukayi sai suka saki dariya gaba ɗayan su

“Kinsan me?” Cewar Saleema tana shafa cikin ta

Girgiza mata kai kawai tayi tana kallon ta

Cikin sakarci irin na yaran masu kuɗi tace “Idan kin haihu ko Ni zaki bama Baby, Ina son shi ni zan kular miki dashi, zamu riƙa wasa tare in koya masa karatu da komi da komi, kinji zaki bani ko?”

Saurin sauke kanta ƙasa Halwa tayi tana jin hawaye na zubowa daga idanun ta, sai tayi saurin tare hannun ta tasharce shi, hannu itama Saleeman takai tana sharo mata hawayen cikin sanyin murya tace

“Kuka kike yi? Ni ce ko? Kiyi haƙuri Don Allah”.

Ɗago kanta tayi tana kallon ta tare da girgiza mata kai, still tana hawayen tace

“A’a ba don ke nake yin kukan ba, kawai na tuna da gida ne, ina matuƙar kewar su Mama, ina matuƙar kewar su sosai..”

Sai tafashe da kuka, nan da nan jikin Saleema yasoma yin rawa sai itama tafashe da kukan

_”Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta ni da mahaifinta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine mu saka ta farin ciki..”_

Tunawa da maganganun Ummi ne yasaka Halwa saurin katse kukan ta tana kallon Saleeman da ita har yanzu bata dena nata kukan ba, dafa kafaɗunta tayi cikin murmushi tace

“Menene na kuka ke kuma? Kinsan da cewa baki da lafiya don Allah ki dena kar wani abu yasame ki”.

“Taya kike tunanin zan dena bayan na ganki cikin ƙunci? Ina matuƙar tausaya miki idan natuna labarin ki, bana jin daɗi ko kaɗan idan naganki cikin damuwa”.

Dariya Halwa tayi tace “to na daina ai, kuma Ni ina kuka ne sabida farin ciki, farin cikin na sami ƴar uwa me ƙaunata, wacce take ƙaunar abinda zan haifa tun kafin yazo duniya, insha Allahu idan har nahaife shi na baki shi kyauta, daga lokacin kece mahaifiyar duk abinda zan haifa”.

Itama dariya Saleema tayi tace “wayyo naji daɗi sosai, bari su Ummi su dawo zan sanar musu, amma kuma kinsan me Yakamata in saka masa a suna?”

Girgiza kanta Halwa tayi tana dariyan shirmen Saleema, wani lokacin in tana abu tamkar ƙaramar yarinya, kuma duk sangarta ne da yayi mata yawa, sai da ta ɗan yi tunani kana tawashe baki tace

“Idan mace ne zan saka mata sunan Ummi, idan kuma na miji ne sai in saka masa Abbana”.

Murmushi Halwa tayi tace “hakan yayi”.

Matsowa sosai Saleema tayi kusa da ita kana tace “yauwa yanzu ya jikin naki dasauƙi ko?”

Gyaɗa mata kai tayi, duk da tana jin ciwo amma bazata iya nuna mata ba coz yanda taga tana nuna damuwarta sosai

“Ok bari in baki labari, zan baki labarin school ɗin mu tare da ƙawaye na”.

Labarin tasoma bata suna ta dariya kamar basu ba, kuma duk kan su idan kakalle su zaka gane ba ishashshen lafiya ne dasu ba, sai dai ƙarfin hali kawai da suka ara suka yafa, daga ƙarshe ma barci ne yaɗauke su sakamakon maganin da suka sha akwai na barci aciki.

_Allah Sarki wannan shi ake cewa gamon jini, Allah yahaɗa mu da masu son mu fisabilillahi._❤️????????

[10/1/2020, 1:46 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

    *CHAPTER 34*

Kwance take saman gadon ta daga ita sai ƴar shimi fara ƙal, sai jan wando robber da yamatse ta sosai wanda da kaɗan yawuce gwiwarta, wayan ta dake ajiye saman gadon ne tasoma ringing sai tajawo tana kallon screan ɗin wayan, ganin sunan HONEY yafito ɓaro-ɓaro yasaka tayi peacking call ɗin tana kangawa a kunne, shiru tayi tana sauraron sa sai kuma ta’ajiye wayan tamiƙe tsaye tana ɗaukan Red colour Jaket ɗin dake ajiye saman gadon tasaka, Jaket ɗin irin me buɗaɗɗen gaba ne sai Belt da aka saka a iya tsakiya wajen cikin ta, iyakan cinyan ta yatsaya mata, sai taɗau Facing cap shima Red tasaka tafito, Ahmad ne kaɗai yake zaune Parlourn yana kallo takalle shi tace

“Idan Mami tafito kasanar mata nafita wajen Sharif”.

Ahmad yace “ok”.

Fita tayi tanufi inda yake tsaye jikin motan sa, tun fitowan ta yake kallon ta yana murmushi har ta’iso wajen

“My beautiful girl”. Yace hakan yana sake faɗaɗa fara’ar sa

Ɗan cije laɓɓanta tayi tana kallon sa itama cikin murmushi tace “ya kake?”

“Lafiya, kefa?”

“Lafiya lau”. Tayi maganar tana jingina da motar itama kamar yanda yayi, sai dai facing juna suke yi

“Kinsan me?”.

Girgiza kanta tayi still tana kallon sa

“Kullum sai in riƙa jin ƙaunar ki na ƙara zauta Ni, har yanzu nakasa sabawa da yanayin da nake ji a kanki”.

Sai ya ɗan yi murmushi yana shafa kwantaccen ƙasumban sa yaƙure ta da ido yace

“Na ƙosa Kausar kikasance mallakina, ina ji ajikina kamar in ban yi dagaske ba zan iya rasa ki”.

Kallon da take masa ne yasauya zuwa mamaki, amma sai batace komi ba taɗauke kai tana jin zuciyar ta na bugawa, kiran sunan ta Sharif ɗin yayi, sai taɗago kai kawai tana kallon sa

Yace “har yanzu baki bani amsa ba akan maganar da mukayi dake”.

“Wace magana kenan?” Tatambaye sa cike da rashin fahimta

Murmushi yayi yace “har kin manta maganar da mukayi lokacin da zamu dawo Nigeria? Haba Dear yakamata ki bama zance na muhimmanci, Ni nayi miki alƙawari wlh zan bar ki kici gaba da aikin ki koda munyi aure, be kamata mu zauna muna ɓata lokaci ba bayan kinsan da cewa mun fahimci juna, kuma iyayen mu sun san komi, to me muke jira?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button