Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Shiru kawai tayi tana sauraron sa har sanda yadasa aya, sai kawai tasaukar da kanta ƙasa tana tunani, gaba ɗaya murmushin dake fuskarta ya ɓace, sai damuwa da yamaye gurbin

“Kausar”.

Saurin ɗago kai tayi takalle sa

“Wai me ke damun ki ne? Na kula gaba ɗaya kin sauya yau meke faruwa?”

“Ban jin daɗi ne Honey”.

“Eyya shine baki sanar min ba? Kinsan bana Son abun da zai dame ki, yanzu meke miki ciwo?”

Yaƙe tayi tana kallon sa tace “kar ka damu kawai gajiya ne yahaddasa min ciwon kai”.

“Eyya sorry, kije gida to sai muyi maganar awaya, Allah yasawaƙe kinji?”

“Ameen”.

Sake sallama sukayi sannan tajuya tatafi, shi kuma yabi bayan ta da kallo har sanda tashige, ajiyan zuciya yasauke yana buɗe motan sa yashiga yabar gidan

Ita kuma tana shiga parlour tawuce ɗakin ta dasauri, akan gadon ta tafaɗa tana sauke numfashi, shiru tayi na ɗan wani lokaci kafin tajawo wayan ta tana latsawa, Numban Khalil talalubo sai tatsaya kawai tana kallo, daga ƙarshe sai tadanna masa kira, har yatsinke be ɗauka ba, akaro na biyu ma da takira be ɗaga ba sai tayi jifa da wayan tana kifa kanta tare da rufe idanu, kamar an tsikare ta kuma sai tamiƙe tafito parlour, har yanzu Ahmad ne kaɗai zaune, ficewa kawai tayi shi kuma yabi ta da ido.

Tana fitowa gidan su ta’isa bakin Gate ɗin gidan Khalil tasoma nocking, Me gadi ne yaleƙo da kansa yana ganin ta yabuɗe mata, murmushi tayi masa tace

“Yana nan ko?”

“Eh yana nan, yanzun nan yadawo”.

Shiga tayi tanufi cikin gidan, tana isa tasoma nocking sai dai shiru babu amsa, ta ɗan jima a wajen tana tunani sannan kuma sai tasaka hannun ta tamurɗa handle ɗin ƙofan yabuɗe, shiga tayi tana kallon parlour’n, babu kowa sai plasma dake aiki shi ƙadai, kan kujera tasamu tazauna sannan tasoma sallama

Khalil dake cikin ɗakin sa, fitowan sa kenan daga wanka yajiyo sallaman ta, ya gane ko wacece don haka kawai yaci gaba da shiryawan sa, bayan ya gama ne yafito parlour’n yasami wuri yazauna yana kallon ta, murmushi tayi masa tace

“Ashe kana lafiya? Na kira wayan ka naji shiru baka ɗauka ba shine nashigo in duba ka”.

Shima murmushin yayi mata yace “sorry ban jiba ne, to ya aikin naki?”

Still tana murmusawa tace “alhmadulillah, kai fa?”

Sai ya ɗan kwaɓe fuska sannan yace “ba daɗi”.

Dariya tayi sosai tana kallon sa yayinda shima ɗin ita yake kallo yana sakin murmushi, sosai take jinta cikin farin ciki ganin ta tare dashi

“Yunwa nake ji ko zaki dafa min abinci irin na ran nan?”

Tsayar da dariyan nata tayi tana kallon sa da murmushi a face ɗinta tace

“Me zai hana, ko me kake so zan yi maka ai”.

Sai tatashi kuma tana faɗin “kabani mintuna 20 yanzu zan gama maka”.

“Ok to muje nima in tayaki ko na koya nima”.

Kausar taji daɗi sosai ganin yanda Khalil yasaki jiki da ita a yau ɗin, atare suka gama abincin suka zubo kuma sukaci tare, duk kan su in kakalle su zaka gane suna matuƙar farin cikin kasancewar su tare, duk abun da ɗaya yayi sosai yake burge ɗayan, Kausar ba ita tabar gidan ba sai bayan la’asar.

***** ***** ***** ****

     “Zainab wai yaushe zaki dena wannan kukan ne? Tun sanda Halwa tatafi kullum cikin kuka kike yi, ko kukan naki ne zai dawo da ita?”

Shiru Zainab tayi sai dai har yanzu hawaye basu dena zuba cikin idanun ta ba

Umma tace “ki tashi kije ki ɗiba ruwa kiyi wanka tunda yanzu kin zama ƙazamiya wankan ma kin dena”.

“Umma Ni har yanzu na kasa yarda da abinda Mama da Nura suka faɗa mana, ta ya Halwa zata tafi tabar su lokaci ɗaya? Ya za’a yi Halwa tatafi batare da ta sanar min ba? Tunda muke da ita ban taɓa jin Halwa tayi maganar dangin mahaifin ta ba, ta ya zasu ce don sun zo ganin ta zata bi su tabar su?”

Sai kuma tafashe da kuka, cikin kukan take cewa

“Wlh Umma ƙarya ne, ƙarya suke yi suce Halwa tazaɓi dangin Mahaifin ta akan su, zuciyata takasa yarda da abinda suka faɗa, suna nufin kenan fa tatafi bazata sake dawowa ba? Ni na tabbata sai dai in wani abu ne yafaru amma Halwa baza ta taɓa tafiya ba”.

“To don ubanki tunda baki yarda dasu ba sai kiyi tayi, ko kuma kibi ta inda kikasan tatafi”. Umma tafaɗi hakan a zafafe domin Zainab ɗin tasoma kai ta maƙura akan zancen Halwan

Tashi Zainab ɗin tayi tashige ɗakin ta batare da tasake furta komi ba.

October 2020.

[10/19/2020, 7:48 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 35*

    Dad da Mom da Nazeefa ne zaune saman dainnig table suna yin luncing, baka jin ƙaran komi sai Spoons, ita Nazeefa kanta na ƙasa daƙyar take cakalan abincin, don har yau bata saba dasu ba, gwara-gwara Mom in suna tare su biyu.

Sameer ne yashigo cikin parlour’n yanufo su yana faɗin “wow nazo a sa’a domin yunwan nima nake ji”.

Mom da taɗago kai tana kallon sa tace “ba daga gida kake bane?”

“Eh naje wajen Friend ɗina ne, kuma daga nan muka wuce Hospital shine nabiyo ta nan”.

Gyaɗa kai kawai Mom tayi tamayar da hankalin ta ga abincin ta

“My Dad barka da rana”. Sameer ɗin yafaɗa yana dafa glass table ɗin da hannayen sa

Dad kaɗa masa kansa kawai yayi sakamakon ya sanya abinci a baki

sai lokacin Nazeefa taɗago kanta tace “sannu da zuwa Yaya”.

Sameer ɗaura hannun sa yayi akanta yana kallon ta yace “Yauwa ƙanwa ta, abinci kike ci ne haka babu tayi?”

Murmushi Nazeefa tayi tana Sad da kai ƙasa, zama yayi gefen ta kana yace

“To nima yi saving ɗina in tayaku”.

Plate tajawo tasoma saving ɗin shi

Dad yace “Sameer yau wai ya naji wayan Ibrahim be shiga lafiya dai? Kuma ban gansa ba kwana biyu”.

Ɗago kai yayi Sameer yana kallon sa yace “Dad wlh ban sani ba, nima dai tun yesterday rabona dashi kuma bamuyi waya ba”.

“Ok ƙara try Numban sa kaji yanzu”.

“Ok Dad”.

Wayan sa yaɗauka yasoma kiran Khalil, ringing ɗaya tashiga but babu answer, sai da yayi two missed calls kafin Dad yace masa “yaƙyale sa haka”. Abincin su sukaci gaba da ci, kamar 5mint kuma sai ga wayan tana ringing, Khalil ɗin ne yakira, ɗauka Sameer yayi zai miƙa ma Dad sai yace masa

“Ɗauka kawai kace masa ina kiran sa yanzu yazo yasame Ni”.

“Ok Dad”.

Peaking call ɗin yayi yace “Hello ɗan ƙanina”.

Khalil dake zaune bakin gado daga shi sai gajeren wando yaɓata fuska yana cewa “Bro bana so fa nace maka”.

Ɗan dariya Sameer yayi kana yace “ok na daina, kazo Dad na Kiran ka”.

Ɗan jimm Khalil ɗin yayi kana yace “ok ga ninan”.

Daga nan kashe wayan sukayi ya’ajiye tare da miƙewa tsaye yanufi wajen sif ɗin kayan sa yafito da wanda zai saka, bayan ya shirya as usual cikin ƙananan kaya farar riga da blue jeans, yasanya brown cover shoes yanufi gaban looking glass yabuɗe locker yafiddo car key yafice, a cikin ɗaya daga cikin motocin sa kalan ruwan zuma yashiga, be cika hawa motan ba sai yaga dama, yanzun ma yau yafiddo ta yasaka aka wanke masa, yana isa bakin Gate yadanna hon aka buɗe masa Gate ɗin yafice, ahankali yake tuƙin nasa har yakai gidan nasu yafito yashige cikin gidan, a lokacin su Mom sun dawo saman kujerun parlour’n suna zaune suna hira, in kaɗauke Nazeefa da bata wajen ta shiga ɗakinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button