BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Lokacin da ya’isa cikin parlour’n bayan ya gaishe da iyayen nashi zama yayi kusa da Sameer dake zaune kan Two sitter
Dad yace “yauwa ina maganar mu da muka yi, shin ka samo matar da zaka aura?”
Shiru Khalil yayi yana kallon Dad ɗin batare da yace komi ba, haka zalika su ma kallon sa suke yi suna son suji me zai faɗa, ganin shirun nasa yayi yawa Mom tace
“Auta kayi shiru, ko har yanzu baka samu matar bane?”
“Ai kuwa idan be samu ba Ni sai in nema masa tunda naga abun nasa yana ɗaukan sa da wasa ne”. Cewar Dad kenan
Khalil kuwa shafo gashin kansa yayi yajuya kai yana kallon Sameer Wanda shima ya kafe shi da nashi idanun yana kallon sa, alama yayi masa da ido sai yakau da kansa yana kallon Dad ɗin yace
“Dad na samu”.
“Masha Allah haka ake so, yanzu yarinyan aina take kuma ƴar wacece?”
“Suna zaune a Jan Bulow, mahaifinta sunan sa Alh. Ahmad Sofana”.
“To Alhmadulillah insha Allahu zamu je zuwa gobe ko jibi don gwara ayi a huta”.
Mom washe baki tayi tace “My Son na tayaka murna, Allah yatabbatar da alkhairi”.
Murmushi kawai yayi yana faman sosa kai, Sameer kuwa ɗan bugun kafaɗan sa yayi yace
“Congratulation My Lil Bro Allah yasanya alkhairi Allah yasa ayi damu, Burina dama kenan naga auren ka gashi komi yakusa zuwa”.
Mom itama cikin farin ciki ta karɓe zancen da cewa “wlh kuwa ai nima nafi kowa son ganin wannan ranan, amma Auta mene sunan surukar tawa? ya kamata kasanar min tun yanzu in sani sannan kakawo min ita in ganta don in tabbatar da cewa ka dace da yarinyan ko kuwa”.
Dariya Dad yayi yace “kai uwar yara wannan zumuɗi haka? Ai sai ki bari komi yakankama tukuna ko?”
Itama dariya tayi tace “Uhm baza ka gane bane amma Ni kaɗai nasan irin farin cikin da nake ji, Ni kaɗai nasan me na tanada a auren Autana”.
…… …….. …….. …….
Da gudu ta’isa kan gadon ta tafaɗa tana sakin kuka me ƙarfi, sosai take kuka sai kazata yanka ta ake yi, kukan baƙin ciki na jin hiran nasu, bata taɓa tunanin ƙaunar Khalil take yi ba sai a ɗan kwanakin nan tagane, hakan yasaka wani baƙin kishi yaturnuƙe ta jin ya sami wacce zai aura “shikenan yanzu ita ta rasa shi?” Tambayan da tayi ma kanta kenan tana sake kecewa da kuka, duk da tasan yafi ƙarfin ta amma sosai take matuƙar ƙaunar sa fiye da tunanin me karatu, batasan wani hali zata shiga ba idan har tarasa shi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba
Jin motsi kamar za’a shigo tayi saurin tsayar da kukan nata cak tana juyawa takalli ƙofan shigowa, dasauri takuma saka hannun ta tashare hawayen fuskarta dai-dai lokacin da Mom tabuɗo ƙofa tashigo, kallon ta tayi yayinda ita kuma tasad da kanta ƙasa tana murɗe yatsun hannunta
“Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa naga kamar kin yi kuka? Meke damun ki?” Mom tatambaye ta cike da kulawa
Shiru Nazeefa tayi sai kuma tabuɗe baki ahankali cike da rawan murya tace “ba..bu ko..mi Momy, wani abu ne yafaɗa min a idanu”.
“Subhanallah sannu, yanzun ya fita ko kuwa?” Still Mom ɗin tasake tambayar ta cike da nuna kulawan ta tana saka hannayen ta taɗago kan Nazeefan tana kallon idanun da suka sauya kala
“Eh ya fita”.
Mom tace “ok sannu ko? Allah yakyauta gaba”.
“Ameen”.
“To tashi yanzu kije Yayan ki na kiran ki zakuyi maganar School ɗin ki da zai saka ki”.
Nazeefa ta’amsa mata da “Toh”. Kana tatashi tanufi ƙofa, itama Mom bayan ta tabi suka fice atare.
****** ****** *******
A cikin satin ne Alhaji Abdurra’uf tare da abokin sa Alh. Mustapha sai kuma Yayar Mom Alh. Maddibo suka je nema ma Khalil auren Bilkisu, koda suka isa gidan kyakykyawar tarba suka samu wajen ƙanin Mahaifin ta kasancewar a wajen sa take zaune, bayan da su Dad suka gabatar da abinda suka zo nema, Alh. Umar wato ƙanin Mahaifin nata nan yasoma magana cikin dattako
“Alhmadulillah gaskiya naji daɗi sosai da akace kamar ku kun zo neman auren ƴata hakan ya faranta min rai matuƙa, sai dai matsalan da akwai wanda nayi mamaki matuƙa cewa ita yarinyan bata sanar muku ba sannan kuma nayi mamaki kan cewa ta turo wani don yanemi auren ta”.
Ɗan jan numfashi yayi yana kallon su yaci gaba da faɗin
“Zan baku haƙuri da cewa mun riga da munyi wa ƴar mu Miji tun tana ƙarama, wanda hakan shine abinda muka saba tun farkon dangin mu wato haɗa auren zumuncin, ina fata zaku fahimce Ni kuma hakan bazai ɓata muku rai ba?”
Alh. Maddibo ne yace “a’a wlh babu komi, ai kayi mana bayanin da zamu fahimta hakan ya gamsar damu, shikenan dama Allah yayi nufin ba matar sa bane Muna godiya sosai”.
Alh. Umar yace “ai Ni ne da godiya bisa abinda ƴar mu tayi, tunda da tasanar dashi duk hakan bazai faru ba”.
Daga nan dai tashi su Dad sukayi tare da yi masa sallama suka tafi, a hanya Alh. Maddibo yayi musu sallama suka rabu yayinda Dad da Alh. Mustapha suka wuce wajen aikin su.
Bilkisu asalin su Nufawa ne ƴan garin Minna, tana zaune wajen ƙanin Mahaifinta ne anan Katsina, babban Family ne dasu kuma sun saba yin auren zumunci ne, ita kanta Bilkisu akwai wanda aka haɗa ta dashi tun tana ƙarama, sai dai shi ɗin baya ƙasar ne yana zaune can Sudan yana aiki, daga zuwa karatu yazauna har yanzu yaƙi yadawo, Allah ne yasaka mata ƙaunar Khalil har takasa haƙuri dashi duk da tasan zai yi wuya ta aure shi, amma soyayya ya rufe mata idanu kwata-kwata ta manta da cewa akwai wanda iyayen ta zasu bata, kuma nan bada jimawa ba ake tunanin sanya ranan auren nasu.
[10/21/2020, 4:12 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
_wannan shafin naki ne ZEENAT, ina godiya da yanda kike ƙaunar Littafina, Allah yabar ƙauna_❤️
.
*CHAPTER 36*
Dad na zaune a parlour’n sa Khalil yashigo yazauna kan kujeran da ke Facing Dad ɗin, Dad ce masa yayi
“Ina fata kaji abinda ke faruwa ko?”
Gyaɗa kansa Khalil yayi
Dad yace “yanzu kana da wata ko kuwa?”
“Dad ni Banda wata, ni abar ma maganar sai zuwa nan gaba don ban shirya aure yanzu ba dama”.
Kallon sa Dad ɗin yake yi be ce komi ba, sai kuma can yabuɗi baki yace “Ibrahim ba maganar wasa muke yi da kai ba, aure nake so kayi kuma a wannan lokacin na gaji da ganin ka haka, idan har maganar neman mata kake yi to Ni na samo maka, akwai yarinyan Abokina da zaka je kanema domin yanzu mun riga da mun gama maganar da Alh. Mustapha”.
Ɓata fuska Khalil yayi yace “Dad meyasaka kake son kabani wacce bana so?”
Murmushi Dad ɗin yayi yace “har yanzu kai yaro ne Ibrahim, ba wai zan maka dole bane amma tunda naga matar ce kakasa nemowa shine Ni nayi maka gwanin ta nanemo maka, kaje wajen ta idan har kun dai-daita kanku shikenan”.
Khalil yace “Dad don Allah meyasaka baza’a janye maganar ba? infact ma Ni yanzu bani da lokacin aure sabida zan tafi England yin wani course, kuma One year zanyi acan”.