BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Dad yace “ok kana nufin Adena maganar auren ka har sai kaje kadawo?”
Gyaɗa kansa yayi yana kallon Dad ɗin tare da turo baki, daƙuwa Dad ɗin yayi masa yace
“Kaga naka Ibrahim babu inda zakaje sai kayi aure koda kuwa gobe ne zaka tafi”.
Cikin shagwaɓa Khalil ɗin yace ” Haba Dad please Mana kabari sai nadawo inyaso sai in auri ita yarinyan da kakeso”.
Shiru Dad ɗin yayi yana kallon sa kana yace “ok shikenan, dama itama yarinyan tana karatu kuma dama Mahaifin ta yace min zuwa nan da shekara ɗaya da rabi zata kammala, kaga idan kadawo sai asaka ranan auren hakan yayi?”
Jinjina kansa yayi yace “eh Dad”.
“Ok tashi kaje Allah yataimaka, yaushe ne zaka tafi?”
Khalil da yamiƙe tsaye yabashi amsa da cewa “nan da Three weeks”.
Dad yace “kana da lokaci ai Yakamata kaje wajen yarinyan kaganta, kuma bana son inji cewa bakaje ba”.
Gyaɗa masa kai yayi kafin yayi masa sallama yafice. Koda yafito babu kowa a palrour, kawai ficewa yayi batare da yashiga wajen Mom ba, motan sa yashiga yabar gidan, wayan sa yaɗauka yakira Brr. Tahir ringing biyu yaɗauka yace
“Ango ango”.
Ɓata fuska Khalil yayi yace “wanene Angon?”
Dariya Brr. Tahir ɗin yayi yace “ai naji komi wajen Dr. Sameer, yace “min anje nema maka auren Billy”.
Tsaki Khalil yaja cike da haushi da zaka gane cikin muryan sa yace “kabari dai kawai Tahir, yarinyan nan ashe yaudarana tayi”.
Brr. Tahir yace “bangane ba kamar ya yaudaran ka tayi?”
Daga nan Khalil yasanar masa da abinda yafaru da su Dad da sukaje kana yaƙara da cewa
“Dama abinda nake gudu kenan Tahir tun farko shiyasaka bana son yin soyayya bcoz yawancin matan mayaudara ne, and duk da bana wani son ta but naji haushi sosai ɓata min lokacina da tayi, gashi yanzu taja min Dad ya samo min wata”.
“To fa haka akayi? Gaskiya banji daɗi ba kuma Bilkisu bata kyauta ba, amma kayi mata uzuri mana don Ni banga laifin ta anan ba matsalan daga iyayen ta ne, meyasaka baza su bata wanda take so ba?”
Gajeren tsaki Khalil yayi yace “har kana da bakin kare ta anan? Ni Abokin wasan ta ne?”
Brr. Tahir yace “kayi haƙuri kabi abin a sannu, kuma don Allah karka ce zakayi mata wata magana da be dace ba”.
Shiru Khalil ɗin yayi don shi yariga da ya rufe shafin ta
“Yanzu to aina yarinyan da Dad ɗin yasamo maka take?” Brr. Tahir ɗin yatambaye sa
Taɓe baki Khalil yayi yace “wai ƴar Abokin sa ne, sai kace suna neman kai dani”.
Brr. Tahir dariya yayi yace “kai masha Allah Allah yasanya alkhairi, gaskiya naji daɗin wannan haɗin domin kuwa idan Dad yabiye taka baza kayi auren yanzu ba”.
Yamutsa fuskar sa yayi yace “kaga ni zan aje waya ina tuƙi ne sai anjima”.
Still dariya Brr. Tahir yayi yace “ok zuwa a anjiman zan kira ka bye”.
Daga nan ajiye wayan yayi yaci gaba da tuƙin sa.
**** ***** ****** *******
Ummi ce zaune kan Three sitter Saleema tayi matashi akan cinyan ta, gefe ɗaya kuma Abba ne zaune kan Two sitter suna hira
Abba ne yace “ƴar Baba tashi akwai maganar da zamuyi dake me muhimmanci”.
Amsa mishi Saleema tayi tana tashi zaune
“Shin kin tuna Abokina Alh. Abdurra’uf?”.
Kallon Abban tayi kana tace “eh Abba nasan shi, ko ba wanda ada kake yawan kai ni gidan ba?”
Murmushi Abba yayi yace “yauwa shi ƴar Baba, kinsan yaran sa ko?”
Gyaɗa kai tayi tace “nasan su Abba”.
“To ki saurare ni da kyau ƴar Baba, kinsan Burin mu shine mu aurar dake ga mutumin da zai kula dake kamar yanda muke kula dake, muna Son farin cikin ki Daughter wannan dalilin ne yasaka muka yanke shawara Ni da Mahaifiyar ki mu samo miki Miji wanda zai baki duk wani kulawa, ɗan gidan mutunci wanda zai iya riƙe mana ke bisa amana, akwai ɗan sa Ibrahim Khalil shine mahaifin sa yake nema masa auren ki, Ni kuma ganin haka yasa na’amince but duk da haka sai na tambayi ra’ayin ki, idan har kin amince zai zo wajen ki don ku dai-daita, kiyi tunani da kyau My Daughter don baza mu taɓa baki abinda baki so ba, zaɓin ki shine namu”.
Saleema kallon Abban nata kawai take yi har yadire maganar kafin cikin zaƙuwa tace
“Abba wai kana Nufin Yaya Barrister?”
“Eh Shi ƴar Baba”.
Rufe bakin ta tayi tana waro idanu cike da wani irin farin ciki tace “Kaiiiii..”
Ummi tace “lafiya Daughter me yafaru?”
Dariya tasaki tana yarfe hannayen ta sai kuma tasake rufe bakin ta tana kallon iyayen cike da tsananin farin ciki, su kuwa kallon ta kawai suke yi suna tunanin “meyasaka ta farin ciki haka lokaci ɗaya?” Muryan ta suka tsinkaya tana cewa
“Anya Abba Yaya Barrister shine Wanda mahaifin sa ke nema masa aure na? Ina mamaki Abba taya?”
Murmushi Abban yayi yace “Ƴar Baba kenan ki dena mamaki ai komi ba yanda Allah baya nuna ikon sa, yanzu menene ra’ayin ki akai? shin kin amince ne?”
Saurin gyaɗa kanta tayi tana me tsananin farin ciki, riƙo hannun ta Ummi tayi tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace
“Wai farin cikin na menene da alamun dai kina son sa kenan?”
Saleema har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi saurin rufewa don baza ta iya yin musu bayanin abinda ke ranta ba, illa tashi da tayi da gudu tanufi hanyan ɗakin su tana ci gaba da dariya, bin bayan ta sukayi da idanu cike da tsananin mamakin ta kana Abba yace
“Ikon Allah wai lafiyan ƴar Baba ƙalau?”
Ummi cike da farin ciki tace “ai inaga Abban Saleema da alamun ƴar mu ta daɗe tana ƙaunar sa ne, domin Ni sheda ne abaya sanda kake yawan ɗaukan ta kuje gidan kullum idan tadawo bata da magana sai na Yaya Barrister, Kai har dai na gaji daji don idan tazauna labarin kenan, to tun sanda tayi ciwon nan sosai aka kwantar da ita asibiti kadena kaita to ban sake jin tayi maganar ba, amma Ni ina da tabbaci son sa take yi kuma ina ganin tana cikin mamakin abun ne”.
“Kai amma idan ko hakane zamuyi farin ciki sosai ai dama fatar mu kenan, burin mu shine tasami miji na gari kuma ina da yaƙini ta samu, domin Khalil be da wani matsala yaro ne me tsananin kirki da biyayya na tabbata bazai taɓa wulaƙanta mana ƴa ba, wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin haɗa wannan auren”.
Ummi jinjina kanta tayi cike da gamsuwar bayanin mijin ta kana tace “to Allah yatabbatar da alkhairi Allah yasa ayi damu”.
“Ameen ameen”. Cewar Abba still yana me nuna farin cikin sa
“Amma ina tunanin ba yanzu za’a yi auren ba sabida yaron zai yi tafiya, kin ga har sai ta gama school ma anan, sai kiyi mata bayani yanda zata fahimta”.
“To babu matsala ai hakan yayi ma”. Cewar Ummi kenan
Daga nan hira sukaci gaba dayi suna tattaunawa akan maganar.
[ad_2]