BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Kamar an tsikare ta kuma tatashi dasauri tana saka bayan hannun ta tana share hawaye, nufan hanya tayi tana tafiya tana tangaɗi kamar wacce tasha wu, dai-dai lokacin da ta’iso ƙofar gidan su Zainab tanufi gidan, tana saka ƙafa a zauren sai taja tatsaya, maganganun Baba ne suka dawo mata cikin kunnin ta
_”Kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari, sai gashi ace za’a haifi ɗan Shege a gidana_”
_”Ki tashi kije ki haɗo kayan ki tun kafin wasu suji”_
“Kenan sun gunmaci ni nabar su akan ƙimar su da mutuncin su yazube? Shin bakusan ƙaddara bace? Ashe dama zaku iya korata akan laifin da na aikata bada son raina ba?” Meyasa zakuyi haka?” Tafaɗa afili cikin dashashshiyar muryan ta tana runtse idanu wasu sabbin zafafan hawaye suna gangaro mata
Still hannu tasaka tashare hawayen, tajuya da sauri tatafi, tafiya take yi ahankali har ta’isa bakin titi, tadoshi hanya tasoma tafiya a gefen titin batare da tasan takamaiman inda zataje ba, don ko alokacin ba cikin hayyacinta take ba tafiyan kawai take yi, tana juya baya tawuce sai ga Zainab ta ɗaya side ɗin an wuce da ita a cikin keke Napep.
_Shin ina kuke tunanin Halwa zata je?_
_wani irin hali zata faɗa?_
_mene yasaka Nura yayi mata wannan abun?_
_Shin ko ya manta da ita wacece a gare shi yayi mata hakan?_
_amsan ku na wajena kubi ni asannu don jin Me zai faru hmmmm._
[9/23/2020, 10:00 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 27*
Tayi tafiyan da yakai kusan awanni biyu batare da ta gajiya ba, kuma bata da alaman tsayawa tafiyan kawai take yi but batasan inda take tsulmiya ƙafafuwan ta ba, har sai da taji ƙafafun nata sun soma nauyi suna takawa daƙyar kafin tasamu gefen wani shago tazauna tana sakin nishi, kallo ɗaya kayi mata zaka gane tana cikin wani mawuyacin hali da baza ka iya fassara shi ba, idanunta gaba ɗaya sun wani jeme sun yi luhu-luhu, har alokacin kuma basu gama washe wa daga canza kalan da suka yi ba, hannun ta tasanya tariƙe goshin ta tana runtse idanu, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta da yanzu yaƙara hauhawa kamar zai faso ƙirjin ta sabida wani irin bugawa da yake yi
Takun takalmi taji da gudu-gudu, hakan yasaka tabuɗe idanun ta tasauke akan sa, shima ɗin itan yake kallo har ya’iso wajen ta, sai yashiga wani lungu da shaguna biyu suka rufe wajen, bata sauke idanun ta a wajen ba kuma bata motsa ba har sai da tajiyo takun wasu mutanen, hakan yasaka tajuya tana kallon su, mutane uku ne da baƙaƙen kaya sun sha Suit, hannun su na cikin rigan su da alamun dai akwai abinda suka ɓoye, har sun gibta ta sai ɗaya yadawo da baya yana kallon ta da fuskar shi a ɗaure yace
“Keee ƴan mata bakiga wani yawuce tanan ba? Ina kikaga yabi?”
Ɗauke idanun ta tayi akan sa tamayar inda taga mutumin nan ya ɓoye, sai taga yaleƙo kan sa suka sake haɗa idanu, kallon ta kawai yake yi da idanun sa masu bala’in kyawu ko ƙyaftawa baya yi batare da ko yayi mata alaman kar tatona shi ba
“Ke magana muke miki fa? Baki ga wani yawuce tanan ba?”
Gyaɗa kan ta kawai tayi tana sauke idanun ta ƙasa, wucewa sukayi batare da sun sake magana ba, sai da sukayi nisa da tafiya kafin yafito, ita kuma taɗago idanu tana kallon sa still shima kallon ta yake yi, sai da sukayi 2min suna kallon juna kafin yajuya dasauri yawuce, kau da kai tayi tana tunanin abinda yasaka mutanen suke neman sa? Sai kuma taruntse idanuwan ta tana jin damuwan ta na dawo mata, hawaye ne suka soma zuba cikin idanun suna gangarowa saman kuncin ta
“Ya zan yi?” Tafaɗa a fili tana wurwurga idanu a hanya
“Wayyo Allah Ni Halwa, Allah na roƙe ka Allah kakawo min agaji, Allah na roƙe ka ya Allah kataimake ni, kataimaki rayuwata, Allah ina buƙatan taimako”. Sai tafashe da kuka me ban tausayi
Ɗaura kanta akan ƙafafunta tayi tasoma rerawa, kai daga jin kukan kasan na ƙunci da baƙin ciki ne, ta jima a wannan yanayin kafin tamiƙe tasoma tafiya, alokacin hankalin ta baya jikin ta tana can tana tunanin kalaman Nura tana yi tana sharan hawaye, sosai tadamu ƙwaƙwalwan ta da son sanin meyasaka ya’aikata mata hakan? sai jinta tayi a ƙasa batare da tasan abinda yasame ta ba
“Subhanallah.. don Allah baiwar Allah kiyi haƙuri, wlh bansan kin taho ba nabige ki da motata”.
Sai alokacin Halwa taɗago kanta tasauke shanyayyun idanunta kan matashiyar budurwan da aƙalla zata bata shekara ɗaya zuwa da rabi
“Don Allah kiyi haƙuri, muje chemis ayi miki dress ɗin ƙafan kinji don Allah?”.
Hakan yasaka halwa tamayar da idanunta kan ƙafanta dake zubo da jini sakamakon ƙurjewan da tayi, but ko kaɗan bataji zafi ba bare tasan taji ciwon, bcoz zafin da take ji cikin zuciyarta da jikinta ya hana taji zafin ciwon, yarinyan taɗago ta suka nufi Motan ta, tabuɗe mata gaba tashiga sannan itama tazagaya tashiga taja motan, Chemis ɗin takaita akayi mata dressing ƙafan sannan suka fito, kallonta yarinyan tayi tace
“Ina ne gidan ku sai in Kai ki ko?”
Shiru Halwa tayi batare da takalli yarinyan ba, kuma bata da alaman bata amsa, ita kuma yarinyan sai kallon ta take yi da alamun tagane tana cikin wata damuwa sakamakon yanda fuskarta yanuna, ga kuma yanayinta, dafa kafaɗanta tayi tace
“Ƴar uwa don Allah kifaɗa min ko wani abu na damunki ne zan iya taimaka miki? Haƙiƙa duk wanda yakalle ki yasan da cewa akwai wani babban al’amari dake damunki, don Allah kisanar dani kamar yanda natambaye ki?”
Sai alokacin Halwa tasake ɗago kai takalle ta a karo na biyu tun haɗuwan su, still dai batace komi ba tasake sad da kanta ƙasa tana jin hawaye na son zubo mata
“Ko baki yarda dani bane?”
Yarinyan tafaɗa tana ɗago haɓan ta, dai-dai da lokacin da hawayen da suka taru a cikin kwarmin idanun nata suka gangaro izuwa saman kuncin ta
“Subhanallah.. kuka kuma? Me yayi zafi ƴar uwa? Don Allah kifaɗa min damuwar ki?” Tafaɗi maganar itama tana son yin kukan
Hakan da Halwa tagani ne yasanya ta motsa baki kaɗan, sai dai yarinyan batasan me tafaɗa ba, don haka tariƙo hannun ta taja ta suka shiga mota, kana tayi wa motan keey tasoma tafiya, shiru babu wanda yayi magana ciki, ita kuma atunanin yarinyan Halwa zata faɗa mata inda zata kaita, saɓanin haka sai taji shiru, hakan yasaka kawai tayanke shawaran tafiya gidan su da ita, don sosai Halwa ɗin taba ta tausayi, haka kawai kuma taji ta kwanta mata arai, kuma nan take tagane tabbas akwai abinda yakorota daga gidan su, ba kuma ƙarami bane babban abu ne
A wani gida me ɗankaren kyau da yalwa yarinyan tatsaya tare da yin hon, babu jimawa aka buɗe mata Gate ɗin takutsa motan ciki, bayan tayi parcking ne tajuyo tana kallon Halwa da itama tabaza idanu tana kallon gidan, ita tun sanda tasaka ta cikin motan tarasa tunanin da zatayi, kawai tatsaya ne taga ikon Allah ina zata kaita, kuma ko kaɗan babu tsoro a fuskarta, domin ita yanzu duk abinda zai same ta idan har wanda zai rabata da duniyar ta ne to tana maraba dashi