BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Muje ko?” Yarinyan tafaɗa tana buɗe motan tafita
Babu musu Halwa itama tabuɗe tafito, tabi yarinyan abaya kamar yanda taga ta doshi cikin gidan, bayan sun shiga parlour’n ne yarinyan takalle ta da murmushi a fuskarta tace
“Kizauna bari in Kira Ummina”.
Daga haka tajuya tanufi wani ƙofa tana kwaɗa ma Ummin nata kira
Halwa kuwa ƙyam tayi anan tsaye bata da alamun zama, kuma kanta a ƙasa yake batare da taɗago shi ba, babu jimawa yarinyan suka fito tare da wata babban mata me kama da ita sak, sai kuma wani babban mutum da shima suke yanayi da yarinyan, don hasken shi ma tabiyo, atare suka iso cikin parlour’n suna kallon Halwa da itama taɗago idanunta tasauke akan su
“Baki zauna ba? Kizauna don Allah?” Yarinyan tace hakan lokacin da ta’iso wajen Halwa takama hannun ta suka zauna kan 2sitter, su ma iyayen nata zama sukayi duk fuskar su cike da mamaki duk da sun san halin ƴar tasu, Mahaifin nata ne yasoma magana da cewa
“Saleema ina kika samo wannan yarinyan kuma?”
“Abba wlh a hanya ne nabige ta da zan dawo daga school, shine nakaita akayi mata dress”.
Sai tamarairaice fuska taci gaba da faɗin
“Kuma Abba naganta cikin damuwa ne shiyasa nace bari in taimaka mata”.
Ummee tace “kuma banda abinki Saleema, kinganta cikin damuwa kina son taimaka mata ai gidan su zaki kaita ba nan ba”.
Abba murmushi yayi yace
“Ina ruwan ƴar Baba, kinsan halinta da son taimako”.
Saleema tace “to Abba ai na tambaye ta inane gidan su bata sanar min ba, shine nakawo ta nan”.
Jinjina kansu gaba ɗayan su sukayi suna kallon Halwa da kanta ke ƙasa tana sauraron su
“To ke kuwa Baiwar Allah Aina kike? Ina ne gidan ku?” Cewar Ummi kenan
Shiru Halwa tayi tana wasa da hannun ta don batasan me zatace ba, Abba shima kallon ta yayi yace
“Yarinya ki sanar damu mana, zan saka amayar dake har gida insha Allahu”.
Cikin dashashshiyar muryan ta da ba’a ji sosai tace
“Iyayena sun kore ni”.
“Saleema me tace ne? Mu bamu ji ba”. Ummi tafaɗi hakan
“Wai iyayen ta sun kore ta”. Saleeman tafaɗa cike da tausayi
“Subhanallah.. kora kuma?” Abba da Ummi suka faɗa atare
“To me kikayi musu?” Ummi tasake tambayar ta
Sheshsheƙan kuka Halwa tasoma yi tare da rufe fuskarta da Hijab, cike da tausayin ta Ummi tace
“Baiwar Allah kisanar damu abinda ke damun ki, inda hali kibamu tarihin ki, muna Son musan meysaka iyayen ki suka kore ki sabida musan ta inda zamu taimaka miki kinji? Kidena kuka kifaɗa mana damuwar ki”.
Riƙo ta Saleema tayi tasoma rarrashinta kamar zatayi kuka, duk fuskarta ya nuna tsananin damuwa, sai da tayi shiru tukun tasoma basu labari kamar haka, tanayi tana kuka.
Ni sunana Halwa, kuma Ni marainiya ce, tun ina ƙarama Mamana da Babana suka rasu, shine dangin Babana da suke garin Gombe suka ɗauke Ni, na taso a hannun su cikin baƙar azaba har izuwa sanda nasoma girma, shine lokacin da ƙanwar Mahaifiyata tazo ganina taga wahalan da nake sha a hannun su taɗauke ni tadawo dani hannun ta, daga nan naci gaba da zama a wajen ta har suka saka ni makaranta, sun ɗauke ni ita da mijinta tamkar ƴar su, sun bani gatan da ko iyayena ne iyakacin abinda zasu bani kenan”.
Fashewa tayi da kuka me tsananin gaske, daga nan taci gaba da basu labarin zamanta a gidan da rayuwan da tayi har soyayyarta da Yaya Nura, zuwa iftila’in da yafaɗa mata da abinda yafaru da ita a yau ɗin.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..” atare Ummi da Abba suka faɗa cike da tsananin mamaki da al’ajabi
“Dama har yanzu akwai irin waɗannan iyayen da zasu kore yaran su akan ƙaddara ta faɗa musu? Ashe har yanzu akwai marasa imani irin su? Basu tunanin abinda zai faru da ita yarinyan idan har sun kore ta? Meyasa wasu iyayen jahilai ne? Me zai saka su kori yarinyan su don kawai wani iftila’i ta afka mata? Basu tunanin kuma taje tafaɗa hannun ɓata gari? Ko kuma abinda suke gudu na zubewar mutunci taje taci gaba da aikata wa? Sannan kuma daga ƙarshe tadawo musu da abun kunyan da suke gudu? Gaskiya su Mamanki sunyi ganganci sun yi wauta, sun maye ladan su da babban zunubi, Allah bazai bar su ba wlh sai sun yi dana sanin abinda suka aikata miki”. Ummi ce take faɗan hakan cike da ɓacin rai
Saleema kuwa me saurin kuka tuni tasoma hawaye sabida tsananin tausayin Halwa
Abba dake ta faman girgiza kai sabida al’ajabi yace
“Tabbas sun yi ganganci sun aikata babban kuskure, amma Allah ai ba azzalumin bawan sa bane kuma shi ke kare duk wanda yaso, sun kore ki don kawai mutuncin su kar yazube, sun gunmaci ke ki wulaƙanta don kawai taki ƙaddaran kenan, amma insha Allahu bazamu taɓa bari ki wulaƙanta ba, mu zamu maye miki gurbin iyayen ki, zamu zame miki haske cikin rayuwan ki, a kuma shirye muke muɗau duk wani ƙaddaran da Allah yaɗaura miki, zamu tayaki yaƙi don kici jarabawan ki, haƙiƙa Allah shi yasan yanda yayi yahaɗa ki da ƴar mu don mutaimake ki, idan har muka bari kika bar gidan nan to tabbas sai Allah ya tambaye mu, ƴata zaki zauna tare damu zamuci gaba da kula dake kamar yanda muke ma ɗiyar mu, kuma insha Allahu duk abinda kike nema bazaki rasa shi agidan nan ba, kiɗauke mu tamkar iyayen ki waɗanda suka zuƙuna suka yahaife ki, mu nan munyi alƙawari zamu share miki hawayen ki”.
Ahankali Halwa dake ta faman rusa kuka tazamo ƙasa, cikin kukan take faɗin
“Haƙiƙa kun cika iyaye na gari waɗanda basusan suga na wasu sun wulaƙanta, Nagode Allah da yahaɗa ni daku, wlh koda iya haka kuka bar ni da kalaman ku bazan taɓa manta ku cikin rayuwata ba, Nagode Allah yasaka da mafificin Alkhairin sa, Nagode Nagode..”
Kukan da yaci ƙarfin ta ne yasaka ta yin shiru, dasauri Saleema tasauko tarungume ta tana nata hawayen tana rarrashinta
Abba yace “Saleema kamata kuje ɗaki sai ki rarrashe ta acan”.
“To Abba”.
Miƙe wa tayi taruƙo ta suka nufi ɗakin ta, yayinda su kuma suka bi bayan su da kallo har suka shige, atare suka sauke ajiyan zuciya sannan suka dawo da fuskokin su izuwa junan su.
.
_Yanzu Labarin yasoma muje zuwa FAN’S._????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️
[9/24/2020, 4:49 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 28*
Ringing tune ɗin wayan sa ne yadawo dashi cikin nutsuwar sa, ahankali yasaka hannun sa yaɗau wayan yana duba wanda ke kiran sa, sai kuma yayi peacking call ɗin yana karawa a kunne, shiru yayi don haka Brr. Tahir yace
“Ya man meke faruwa ne wai? Nafita nazo na tarar da missed calls ɗin ka, I’m so surprised da naga kiran ka har 5missed call, ina fata lafiya dai?”
Numfashi Khalil yasauke a hankali kana yace
“Brr. Tahir yau fa daƙyar nasha hannun wasu mutane”.