Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Subhanallah.. wasu mutane kenan? Me kayi musu?” Brr. Tahir ɗin yafaɗa cike da firgici

“Hmm wasu mutane kasani in banda mutanen da muke Shari’a dasu, kasan da cewa kwanaki nafaɗa maka suna bibiyana but duk da haka ban yi tunanin abun ya kai hakan ba, nafita zuwa wajen Mr. Abdullah, lokacin nafito daga gidan sa sai natsaya nan Resturent inci abinci, bayan nafito nagan su sun biyo ni, wlh naji tsoro sosai coz suna ɗauke da bindiga, daƙyar nasha ina faɗa maka, ƙarshe dai can nabaro motan sai dai na’aika drever yaɗauko min”.

Brr. Tahir yace “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. Ib ina tsoron fa mutanen nan su cutar da kai, why not mu sanar da Police????? sannan yakamata kabar gidan nan zuwa lokacin da za’a gama, hankalina be kwanta ba maybe su biyo ka har gida”.

Shiru Khalil yayi naɗan wasu sakonni kafin yace

“Nima hakan ne araina, but nariga da nayi ma DPO magana, yace “zai turo yaran sa suyi gadina”.

Ajiyan zuciya me ƙarfi Brr. Tahir yasauke kana yace

“But duk da haka dai hankalina be kwanta ba wlh”.

Murmushi Khalil yayi yace “babu abinda zai faru sai alkhairi, insha Allahu gobe komi zai wuce”.

“Hakane.. Allah yakaimu to”.

“Ameen” Khalil ya’amsa masa

Daga nan sai da suka daɗe suna tattaunawa akan aikin nasu kafin suyi sallama, ya’ajiye wayan yana sakin ajiyan zuciya, kana yaɗan kwantar da kan sa saman pilow yana rufe idanun sa, fuskar ta ne yabayyana acikin ƙwayan idanun nasa, dasauri yabuɗe yana jin zuciyar sa na bugawa

“Meyasaka yarinyan taƙi ɓace masa?” Yatambayi kan sa yana dafe kan sa dake sara masa a hankali

Tun da yadawo gida yake tunanin ta, da zaran yarufe idanun sa kuma fuskar ta yake hangowa, kuma sosai yake ganin tsananin damuwa a fuskar nata, afili yafurta

“Wacece ita? Meyasaka tataimake ni? Meke damun ta?”

Sai yatallabo kumatun sa yana tsira wa waje ɗaya ido, ya jima ahaka yana tunanin da besan na menene ba kafin yamiƙe yashige toilet, alwala yayi yafito yashinfiɗa sallaya yagabatar da sallan magriba, yau be jin zai iya zuwa ko ina, don haka tun da yashigo ma yasanar da ma’aikatan sa kar wanda yafita, sannan yabada umarnin a kulle masa gida, yana nan zaune har aka kira isha’i yagabatar sannan yamiƙe yafita, kichen yawuce yahaɗa Coffee yazauna nan yashanye kana yakoma ɗaki, wanka yasoma yi yasauya kaya izuwa na barci, yakashe wuta yahaye gado, addu’a yayi yashafa tare da rufe idanun sa, ya jima kafin barci yaɗauke sa

Can cikin dare yatashi afirgice yana salati, gaba ɗaya yahaɗa gumi sakamakon mafarkin da yayi da ita, runtse idanun sa yayi yana tuna kukan da take masa cikin mafarkin kuma tana neman taimako a wajen sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, sai yadafe kan sa da duk ka hannayen sa yana sake runtse idanun, ya jima ahaka kafin ahankali yazuro ƙafafun sa ƙasa yasauka saman gadon, sai da yayi kusan mintuna biyar a tsaye yana tunani kafin yataka yashige toilet, alwala yaɗauro yafito yasauya kayan sa zuwa jallabiya yasoma gabatar da nafila.

             _*****_

Alhaji Mubarak mai Kuɗi wani babban attajiri ne da yayi ƙaurin suna a faɗin garin Katsina da kewaye, matar sa ɗaya da ƴaƴan sa biyu, Hassana ita ce Babba tana aure a ƙasan England, sai A’isha da take zaune a wajen ta tana karatun ta acan ɗin.

Mutum ne shi me taimako wajen mutanen gari, kuma kowa ya shaida hakan domin sosai ake girmama sa sabida ana ganin sa me ƙaunar talakawa, sai dai abinda basu sani ba na daga halin sa, shi mutum ne da ko kaɗan baya da imani baya da tausayi abaɗini, sana’ar sa shine kasuwan ci, sai dai babu wanda yasan da cewa yana safaran ƴan mata zuwa wani ƙasa, sannan yana harƙallan sai da Coken, yana kuma gudanar da sana’ar tasa ne batare da kowa ya sani ba.

         Dr. Sabit shine wanda yake taimaka masa, kuma tare suke harƙallan tasu, babban Likita ne shi da yayi fice sosai kuma wanda ake ji dashi cikin garin Katsina, Shine Doctorn da yake ma duk wasu yara da suka samu operation yazuba musu Coken ɗin sabida afita dashi waje batare da an gano su ba.

Akwai wani Doctor Salis abokin aikin Doctor Sabit ne, shi yafara gano abinda suke aikatawa, har yayi yunƙurin kai su ƙara don yatona musu asiri, but daga ƙarshe sai dai aka nemi Doctor Salis aka rasa ya ɓace ɓat, kuma ba’a san me yafaru dashi ba.

Alhaji Mubarak ba iya mutanen gari kaɗai yake ma kirki ba, har ta da ƴan aikin gidan sa, don haka sosai suka saki jiki agidan, sai dai abinda basu sani ba yana amfani da hakan ne don cin ma burin sa, coz sau da dama yawancin masu aikin suna da yara, sannan kuma akwai ƴan mata acikin su, babu wanda yasan meyasaka masu aikin gidan sa mata basu daɗewa, sai dai lokaci kaɗan za’a neme su a rasa.

Hajjo tana ɗaya daga cikin masu aikin gidan, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka daɗe sosai suna aiki a gidan, asalin ta bafulatana ce mazauna ƙauye, sun zo tare da mijinta da yarinyan su ɗaya Nazeefa cikin birni, wata mata ce tayi ma Hajjo hanya har tasami aiki agidan, sosai take jin daɗin aiki a gidan Alhj. Mubarak me kuɗi kuma suna samun duk abinda suke so

Bayan wasu shekaru ne mijinta yarasu don haka taɗauki Nazeefa suka taho gidan Alhj. M. Me kuɗi don tanemi alfarma wajen sa don yaba su waje agidan nasa su zauna tunda ya saba yin haka, lokacin da tagabatar masa da alfarman ta gare sa babu musu ya amince, Hajjo tayi murna sosai sai dai batasan cewa Alhj. M. Me kuɗi ya amince ne don ganin Nazeefa da yayi, yasan da cewa idan suka zauna agidan sa hakan zai basa daman cikan burin sa akan ita Nazeefan.

Rayuwa taci gaba da gudana, lokaci ɗaya Allah yajarabbi Hajjo da ciwo, ashe ciwon ajali ne, don batayi sati ɗaya ba tarasu, Nazeefa tayi kuka sosai sabida tasan bata da wasu ƴan uwa kuma da suka rage mata, sannan batasan ma ina ne ƙauyen su ba bare takoma, ana haka Alhj. Mubarak yakira ta har parlourn sa bayan yayi mata ta’aziya yace

“Nazeefa sunan ki ko?”

Kanta a ƙasa ta’amsa mishi

“Ok zakici gaba da zama anan idan kinaso, sai ki maye gurbin Mahaifiyarki, sannan duk abinda kike nema ki sanar dani ko ki sanar da Hajiya, daga yau karki ɗauki kan ki marainiya tunda har kina damu”.

Sosai Nazeefa tayi murna da jin maganar sa, don haka tayi masa godiya tafice, shi kuwa murmushi yayi yaɗau Jaridan sa yasoma karantawa, yasan da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan zai cika burin sa akanta

Ana nan wata rana Hajiya ta aiki Nazeefa gidan ƙawar ta ta’amaso mata saƙo, kasancewar babu nisa da gidan su a ƙasa tatafi, bayan taje ta dawo ne a hanyan ta na dawowa gida sai ga Motan Alhj. Mubarak ya tsaya tare da zuge glass ɗin motan yana kallon ta da murmushi a face ɗin sa, ita kuwa tayi mamaki sosai ganin sa shi kaɗai babu drever, umarni yabata tashigo motan babu musu kuwa tashiga, don shi mutum ne me tsananin kwarjini da babu yanda za’ayi kayi masa musu a matsayin sa na babba, lokacin da suka iso gidan sai taga sun wuce but bata iya ce mishi komi ba, sai dai sosai tayi mamaki kuma tana son tatambaye shi sai dai babu dama, har suka isa wani babban gida yace da ita tajira sa bari yazo, fita yayi yashiga gidan, ita kuma gaban ta sai faɗuwa yake yi, tasan da cewa shi ɗin mutum ne me sauƙin kai, amma babu abinda yahaɗa ta dashi a matsayin ta na ƴar aikin gidan sa bare yaɗauko ta cikin motan sa, that’s why gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya, duk tsoro ya cika ta, tana nan zaune wani mutum yazo yace mata tashigo inji shi, babu musu tafito tabiyo bayan mutumin suka shiga gidan, lokacin da suka shiga babu kowa, a lokacin ne taji kamar ana buga mata guduma a ƙirjinta, tsinkayan muryan mutumin tayi yana faɗin “tabiyo shi” wani ƙofa taga yabuɗe yashiga sai tabi bayan sa, suna shiga tatsaya tana kallon tsarin ɗakin da babu komi sai gado da sif taji ƙaran rufe ƙofa, kallon ƙofar tayi sannan kuma tawur-wurga ido cikin ɗakin taga babu mutumin da suke tare, a sukwane tanufi ƙofan da yake a kulle tasoma taɓawa tana son buɗewa, sai dai da alamun an rufeta ta baya ne, wani irin bugawa zuciyarta tayi batasan sanda tasoma jijjiga ƙofan ba tana ɓarkewa da kuka, cikin kukan take faɗin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button