BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Don Allah kabuɗe, ina ne nan ina kakawo Ni? Na shiga uku Ni Nazeefa, wayyo Allana Wayyo Mamana”.
Kuka take yi sosai tana jijjiga ƙofan da ko motsi baya yi, daga ƙarshe zubewa nan ƙasa tayi tasoma rusa kuka tana shushshura ƙafafu, ta jima ahaka tana kukan wanda har muryan ta yadena fita sai hawaye dake ta zirara.
[9/25/2020, 11:26 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 29*
Wasa wasa sai da Nazeefa tayi kwanaki bakwai a wannan gidan batare da tasan takamaiman inda take ba, tayi kukan duniya tayi ihun duniya babu wanda yazo wajen ta, sai dai da zaran tayi barci ta farka zata tashi taga an ajiye mata abinci, tun bata taɓawa da taga alamun kanta take cuta sai tasoma ci, sau da dama tayi yunƙurin kwana ido biyu don tasami nasaran guduwa idan akazo kawo mata abinci, but bata taba samun sa’a ba, abinda bata sani ba akwai Camera cikin ɗakin, idan har sukaga batayi barci ba to bazasu kawo mata abinci ba, haka zata ƙariki zamanta babu su babu alamun su, daga ƙarshe har tacire rai da samun daman fita, jira kawai take yi ranan da zasu kawo ƙarshen rayuwanta, domin a tunanin ta gidan cin kai take.
Wata rana tana zaune taga wannan mutumin da yashigo da ita yabuɗe ƙofan yashigo, zabura tayi tayi kansa da gudu tana ƙoƙarin guduwa yayi saurin cafko ta da hannu ɗaya, abinku da wacce bata da ƙarfi ko na sisin kwabo nan tadawo baya tafaɗa jikin sa, kuka tafashe dashi tana faɗin
“Don girman Allah kataimake ni kabar ni in tafi, wayyo Allana me kuke so dani ne..?”
Bata rufe baki ba Doctor Sabit da Alhj. Mubarak suka shigo, duk kan su face ɗin su a ɗaure ne babu alaman wasa, doctor Sabit ne yanufo ta riƙe da wani allura a hannun sa, ita bata kula da alluran ba sai kallon Alhj. Mubarak take yi tana kuka don takasa magana, so take yi taroƙe shi yafitar da ita amma ina, kafin ma tagama tunanin zucin ta har taji an sanƙama mata allura, batasan sanda takurma ihu ba tana riƙe hannun doctor ɗin, kallon shi take yi idanun ta cike da hawaye tana motsa baki, sai kuma tatafi luuuuuu tafaɗi nan ƙasa.
Alokacin da tafarka alluran be gama sakin jikin ta ba, ga wani zafi da yaziyarci ƙwaƙwalwanta, nan take taɗaura hannun ta saman maranta tana sakin kuka mara sauti, tayi tsawon mintuna 5 ahaka kafin tayi yunƙurin miƙewa, daƙyar talallaɓa tatashi zaune tana jin kanta na sara mata, ga wani irin jiri dake ɗiban ta tana ganin abubuwa bibbiyu, ɗakin take bi da kallo sai dai ba wanda aka ajiye ta bane, wannan cike yake da mata Sa’annin ta da waɗanda suka girme ta, su ma da alamun dai abinda akayi mata shi akayi musu, sai dai su basu farka ba saɓanin ita, Allura ne da akayi musu na tsawon awanni but abun mamaki ita be yi tasiri ajikin ta ba, mintuna 20 kenan da yin mata sannan tafarka, kuma anyi musu ne har sai an fita dasu zuwa ƙasashen da za’a kai su sannan su farka
Miƙewa tayi cikin yanayin rashin hankali tasoma tafiya aduƙe tana tangal-tangal kamar wacce zata kife ƙasa, tariƙe cikin ta dake mata bala’in zafi, ƙofa tabuɗe tafice sai gata cikin parlour, babu kowa ciki suna can suna shirin yanda zasu fitar da ƴan matan bayan sun dawo cikin hankalin su na mintuna ƙalilan, domin alokacin da suke zuwa Airport dasu a farke suke kai su har sanda zasu shiga jirgi, sai dai hankalin su da tunanin su sun riga sun gushe, duk yanda akayi dasu haka zasuyi
Direct wani ƙofa tanufa tabuɗe tafice, Allah yabata Sa’a ashe waje ne, haka tafita gidan batare da taga kowa ba, tafiya take tayi batasan inda take saka ƙafarta ba, tayi tafiyan da ita kanta batasan awanni nawa yaɗauke ta ba, sai faɗi tayi ƙasa a sume batare da tasan inda kanta yake ba.
Lokacin da tafarka garin yayi duhu sosai kuma babu wanda yaganta, kasancewar anguwan na masu kuɗi ne zai yi wuya kaga mutum a waje, zuwa lokacin tsananin azaba take ji a cikin ta, a lokacin kuma ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya, sai tariƙe cikin ta tana ta kuka tana burgima awajen, tsawon lokaci kafin tayunƙura daƙyar tamiƙe taci gaba da tafiya tana kuka, a wannan lokacin ne Brr. Ibrahim Khalil yazo wucewa yabige ta batare da yasani ba, yana fitowa yaganta yashe a ƙasa da alamun ta sume ne, ɗaukan ta yayi yasaka ta a mota yanufi da ita asibiti, lokacin Dr. Sameer be riga ya tafi ba, shi ya’amshe ta yakira abokin sa Dr. Hashim, babu jimawa kuwa yazo yasoma dubata, duk Brr. Khalil yadamu yakasa zama waje ɗaya sai zagaye yake yi, sai da Dr. Sameer yabashi ƙwarin gwiwa tukun hankalin sa yakwanta
Sai da akayi 2 hours ana duba ta kafin Likitocin dake kan ta su fito, Dr. Hashim ne yayi musu bayanin da yaɗaga musu hankali, sosai suka shiga damuwa jin cewa Coken ne acikin ta, kuma ya kai tsawon lokacin da Yakamata acire mata but ba’a cire ba, don haka har yasoma narkewa yataɓa mata hanji dole sai anyi mata aiki an cire, sannan kuma sai anyi mata dashen hanji, Khalil ne yasaka hannu aka shiga da ita Theater, tsawon awa biyu kafin aka fito da ita, sai alokacin suka tafi gida bayan da suka tabbatar komi normal.
Watan ta biyu kafin tafarfaɗo, kuma duk alokacin tana ƙarƙashin kulawan Khalil ne tare da Doctor Hashim da Doc. Sameer, sosai take jin jiki duk da an samu nasaran aikin, ko magana bata iyayi bare tashi, komi sai dai ayi mata
Khalil sosai yadamu da halin da take ciki haka kawai yake jinta tamkar ƙanwar sa, kuma yayi imani cewa yarinyan zaluntar ta akayi, don haka alokacin ne yasoma bincike akan ta, kuma ya yi ƙudirin sai ya ƙwato mata haƙƙinta, tsawon wata yana bincike sannan yagano inda take zaune, wato gidan Alh. Mubarak, a ranan da yashirya yaje yayi hira da me gadi har yagano labarin ta a wajen sa, bayan ya dawo ne a ranan wasu suka zo kashe ta cikin asibitin, abinda be sani ba Khalil yana tafiya me gadin yasanar da Alh. Mubarak, tunda dama neman ta ake yi ana tunanin ɓata tayi, Dr. Sameer ne yashigo cikin ɗakin lokacin da mutumin da zai kashe ta yaso kashetan, shine yagudu batare da yayi abinda yazo yi ba, wannan dalilin ne yasaka suka yanke shawaran afitar da ita daga asibitin, don sun gano kasheta ake da ninyan yi, Shine Khalil yakaita gidan Baaba Talatu, anan akaci gaba da kula da ita sannan shi kuma yaci gaba da bincike kan lamarin, har sanda yagano komi akan Alhj. Mubarak tare da Doc. Sabit, babu ɓata lokaci yashigar dasu ƙara zuwa kotu
A lokacin hankalin su Ahj. Mubarak be wani tashi ba, domin acewar su babu yanda za’a yi akama su da laifi, sannan kuma su ɗin masu hannu da shuni ne waɗanda sukayi fice kuma kowa yasan halin su, babu yanda za’a yi yayi nasara, but zaman farko a kotu sai ido yaraina fata, yanda Brr. Khalil yayi takawo shaidu hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, anan Alƙali yabada hutun wata ɗaya da sati biyu bayan da kowa yagama kawo shedun sa, kuma ya bada umarnin ranan da za’a dawo yakasance Nazeefa ta hallara, sakamakon hujjojin da Brr. Khalil yaba da ne aka tsare Ahj. Mubarak tunda an gano yana da laifi