BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Wannan shari’ar ya ja cece kuce sosai a wajen jama’a, sosai mutane suka ƙosa suga ranan da za’a dawo don yanke hukuncin, kuma duk alokacin mutane basu yarda cewa Alh. Mubarak yana da laifi ba, sai dai mujira ranan dawowan kamar yanda yakasance gobe da ƙarfe 02:00pm.
_Hmmm masu karatu ku ma sai kushirya don jin Me zai wakana a Court._ ????
_ina gayyatar Masoya Brr. Ibrahim Khalil da Nazeefa, kuzo kugani da idanun ku._????????????????
[9/29/2020, 12:44 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What’sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 30*
Washe gari ƙarfe 07:15am. Saleema tagama shirin ta na zuwa school, tana shirin ɗaukan jakan ta taji cikin ta yasoma murɗa mata, dasauri tariƙe tana runtse idanun ta, lokacin ne Halwa tafito daga Toilet tana kallon ta, ganin tana riƙe da ciki taƙi jirgawa yasa tamatso kusa da ita cikin sanyin murya take tambayan ta “ko wani abun na damun ta?” Murmushi Saleema taƙaƙalo tare da girgiza mata kai, sai dai har alokacin tana riƙe da cikin nata ne, hannu tasanya taɗau jakan kafin takalle ta tace
“Ni natafi school sai na daw..”
Bata ƙarisa maganar ba tadurƙushe nan ƙasa tana faɗin
“Wayyo cikina wayyo Allana”.
A ruɗe Halwa tabi ta ƙasan tana kiran sunan ta tare da tambayan ta abinda ke damunta, ganin tasoma kuka sosai tana sake riƙe cikin ta yasaka tamiƙe dasauri tafita, ɗakin Ummi tashiga dasauri, tana tsaye kuwa itama tagama shirin ta nazuwa Hospital kasancewar ita ɗin Nurse ce, taburmo ɗakin tana kiran sunan ta, Ummi kallon ta tayi tace
“Lafiya Halwa meke faruwa?”
Cikin rawan murya kamar zatayi kuka tace “Saleema ce babu lafiya”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Ummi tafaɗa cikin tashin hankali kafin tanufo wajen ta tana faɗin
“Tana ina? Ina take?”
“Tana ɗaki”.
Atare suka isa ɗakin lokacin gaba ɗaya Saleema tafita hayyacin ta sai kuka take yi, ga duk kan alamu tana jin jiki sosai, riƙo ta Ummi tayi tana kiran sunan ta tare da tambayan ta “Ina ke mata ciwo?” Duk hankalin Ummi atashe yake tarasa ma me zatayi
Halwa tace “Ummi ko za’a kira Abba akaita asibiti?”.
Sai alokacin tunanin hakan ma yazo ma Ummi, tayi saurin cicciɓan ta Halwa tatayata suka fito da ita, suna fita waje Drever yazo da gudu yabuɗe musu mota suka saka ta, Ummi tashiga baya kusa da Saleema, ita kuma Halwa tashiga gaba tare da drever suka tafi, sai acikin motan Ummi ta’ari wayan drevern takira Abba tasanar masa.
Lokacin da suka isa asibitin tuni an amshe ta kasancewar ba yau suka saba zuwa ba, kuma dama tana da Doctorn da yake duba ta na musamman acikin asibitin, ana shiga da ita Abba shima ya’iso duk hankalin sa atashe, Halwa yanda taga su Ummi sun tashi hankalin su sosai itama sai taji duk ta damu, haka tazauna waje ɗaya tatakure tana tuna ɗan zaman da sukayi daga jiya zuwa yau, sosai tafahimci ita ɗin yarinya ce me tausayi da son mutane, sannan kuma ta fahimci akwai ƙauna sosai a tsakanin ta da iyayenta, take taji hawaye ya zubo mata tayi saurin saka hannu tana sharewa.
Koda aka fito da ita Abba ne yanufi wajen doctor, Ummi da Halwa kuma suka shiga ɗakin da aka kwantar da Saleema, tana kwance ne asaman gado, abun tausayi kamar ba itace lafiyan ta lau yanzu ba, amma Allah da ikon sa numfashi ma bata iya yi sai da taimakon Oxygen, Ummi hawaye tasoma zubarwa da ganin tilon ƴarta a irin wannan yanayin, takawa tayi taƙarisa wajen gadon, itama Halwa ahankali ta’isa jikin gadon tana ƙure Saleeman da idanu, zama Ummi tayi tariƙo hannun ta ɗaya wanda ba’a saka mata drip ba tana ƙare mata kallo, cikin zub da hawaye tace
“Allah Sarki Saleema, Allah yabaki lafiya, haƙiƙa kinga jarabawa a rayuwan ki, ko yaushe ne zakiji daɗi kamar kowa?”
Cikin tsananin tausayi da jin kalaman Ummin Halwa tazame nan gefen gadon tazauna, share hawayen ta Ummi tayi taɗago kanta tana kallon Halwa tace
“Tun tana ƙarama Allah yajarabce ta da ciwon zuciya, dashi tataso har girman ta, duk iya maganin da muka nema akan ta Allah be sa an dace ba, tasha baƙar wahala kamar bazata rayu ba, acikin shekaru biyu da suka wuce akayi mata aiki a ƙasan OXFORD, Allah yasa an dace, duk da haka muna gudun ɓacin ranta domin da zaran ranta ya ɓaci ciwon ta yana ƙoƙarin tashi ne, sai dai ba’a rufa watanni biyu ba tasoma ciwon ciki me tsanani, koda muka kaita asibiti aka gano tana ɗauke da ciwon hanta ne”.
Cikin sheshsheƙan kuka Ummi taci gaba da faɗin
“Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta Ni da mahaifin ta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine musaka ta farin ciki, duk abinda take so shi muke yi, sai dai fargaban mu wanene zai ci gaba da kula mana da ita idan har takoma ƙarƙashin sa, wani namiji ne zai iya zama da ƴar mu yasaka ta farin ciki kamar yanda Likitoci suka sanar mana? yah Allah gamu gare ka, ya Allah kasauƙaƙa ma wannan baiwa taka, Allah yabaki lafiya Saleema”.
Halwa batasan tana zirarar da hawaye ba sai da taji danshin su akan hannun ta, cikin rawan murya ta’amsa ma Ummi da “Ameen”. Tana saka hannu tashare hawayen, Abba ne yashigo cikin ɗakin, dasauri Ummi tamiƙe tana kallon sa tace
“Abban Saleema me likitan yace? Da fatan babu abinda yasami ƴar mu? Ya Allah..”. Sai tafashe da kuka tana saka hannu tarufe idanun ta
Ahankali yasaka hannun sa yana bubbuga kafaɗan ta, cikin ƙarfin hali yace
“Kiyi shiru don Allah, babu abinda zai sami ƴar mu insha Allahu, Doctor yace ciwon ta ne kawai yatashi but zata sami sauƙi very soon”.
Ummi tace “Ina jin tsoro sosai Abban Saleema, ina jin tsoro kar mu rasa ta”.
“Baza mu rasa ta ba Asma’u, ki dena faɗan haka kinji?”
Rarrashinta yayi sosai, sai da yaga tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kafin yamayar da kan sa zuwa ga Halwa da har yanzu take zuban hawaye, gaba ɗaya ta takure waje ɗaya ta duƙar da kanta ƙasa, kiran sunan ta Abba yayi kana yace
“Kema ya dace kiga likita coz ɗazu kafin nafita Saleema tafaɗa min da zazzafan zazzaɓi kika kwana, kuma dama Yakamata aduba lafiyan ki da abinda ke cikin ki, be kamata abarki haka da ciwo ba, bari nafita nayi ma Doctor ɗin magana”.
Daga haka Abba fita yayi ita kuma Ummi takoma tazauna tare da riƙo hannun Saleema tana kallon ta.
***** ****** ******
Ƙarfe 01:10pm. Brr. Khalil yagama Shirin sa, ya saka riga da wando white colour, sannan yaɗau rigan aikin sa tare da hulan yariƙo briafcase ɗin sa yafito, Direct wajen farar motan sa yanufa yabuɗe yashiga yazauna, ya kai wajen five minutes kafin yatada motan yanufi bakin Gate, hon yadanna Gate man yazo yabuɗe masa yaja motan ahankali yafice, sai da yadaidaita motan saman kwalta kafin yaɗau wayan sa yakira Sameer