Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“Hello Bro”.

Daga can Sameer ya’amsa mishi da faɗin

“Kana gida ne ko ka tafi?”

“No gani a hanya, zan wuce gidan Mom”.

“Ok shikenan, dama tambayan ka zanyi don mu mun riga mun isa”. Sameer ɗin yafaɗi hakan

“Ok nima bazan daɗe ba, yanzu insha Allahu zan ƙariso”.

Daga haka sallama sukayi ya’ajiye wayan, sannan yamayar da hankalin sa ga tuƙin sa, be ɗau lokaci ba ya’isa gidan su Kasancewar yau ɗin ya ɗan taka motan da gudu, yana yin parcking yafito yanufi cikin gidan, a Parlour yatarar da Mom tana zaune tana shan Fuirt, ƙarisawa yayi yazauna gefen ta yana riƙo hannunta yayi mata peck a bayan hannu kana yace

“Sannu da hutawa Mom”.

Murmushi tasakar masa tace

“Yauwa My Son, har ka iso?”

Gyaɗa mata kai yayi yana ɗaukan Apple yasoma gutsira yana taunawa a hankali

“Masha Allah.. yanzu itama Nazeefan tashiga ɗaki taje shiryawa, nima wannan karon dani za’a je, bari inje in shirya”.

“Yakamata kam, but ina Dad yake?”

“Oh Dad ɗin ka yafita tun safe akwai meating ɗin da yake dashi, but yace “idan sun gama da wuri zai same mu acan”.

Nazeefa ce tafito cikin shirin ta na riga da wando farare, sai taɗaura Coffee ɗin Hijab, sosai tayi kyau kasancewarta fara, tana hango Khalil shima da fararen kayan sai wani irin farin ciki Yakamata, ko ba komi sun yi anko yau, kuma hakan yayi mata daɗi

“Ƙariso mana kin tsaya, me kike tunani?” Muryan Mom yadawo da ita hayyacin ta

Sai alokacin Khalil yakalli inda take tahowa, idanun sa kawai yaƙura mata har ta’iso wajen kanta a ƙasa tagaishe sa, amsa mata yayi yana tauna Apple ɗin dake bakin sa har yanzu kuma yaƙi kau da idanun nasa kanta

Mom tace “bari inje in shirya”.

Tashi tayi tawuce ɗakinta, shima kuma Khalil dake kallon Nazeefa yayi mata alama da ido alaman tazauna gefen sa, babu musu tazauna cike da kunya, sauran tufan dake hannun sa yamiƙa mata, hakan yasaka taɗago kanta tana kallon sa don bata fahimci abinda yake nufi ba

“Ki ci”. Yabata umarni yana kawar da kansa

Ahankali tasanya hannu ta’amsa takai bakin ta idanun ta akan sa, gutsira tayi tana lumshe idanuwanta cike da wani irin daɗi da yaziyarci zuciyarta, shi kuma hakan yabashi daman sake maida idanun sa kanta yana ƙare mata kallo, har sanda tabuɗe idanun ta tasauke acikin nasa, sai tayi saurin Sad da kai ƙasa tana murmusawa

kiran sunan ta yayi, bata amsa ba sai ɗago kai da tayi tana kallon sa

“Kina jina ina son in sanar dake, kikasance me juriya ga duk tambayoyin da za’a yi miki a Court, bana son ki nuna tsoro ko firgita a wajen, ina son ki amsa duk wasu tambayoyi da za’a miki batare da fargaba ko tsoro ba, Nazeefa kina dani a wajen don haka kiɗaura wa kanki ƙwarin gwiwa kinji?” Yayi maganar cikin tausasa murya still yana kallon ta

Gyaɗa masa kai tayi, kana tace “insha Allahu Yaya zan amsa duk wata tambaya batare da na nuna tsorona a fili ba”.

Murmusawa yayi kawai yana kau da kan sa, lokacin ne kuma Mom ta’iso wajen tana cewa

“Kutashi Muje to na shirya”

Gaba ɗaya suka tashi suka fice, motan Khalil ɗin suka shiga yaja yafice a gidan.

[9/29/2020, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 31*

Lokacin da suka isa, gaba ɗaya haraban court ɗin cike yake da mutane, Khalil ce musu yayi “su shiga ciki”. Don haka suka fice suka bar sa cikin motan yaɗau wayan sa yana neman layin Brr. Tahir.

       *20 minutes*

Shigowan Alƙali yasaka kowa yayi shiru, duk kan su tashi sukayi har sai da Alƙali yazauna kafin kowa ma yazauna, daga nan Maga-takarda yamiƙe yasoma bayani kamar haka:

“Ayau 26 September 2020 zamu ci gaba da gabatar da shari’ar Alhaji Mubarak Mai kuɗi da Nazeefa Shehu”.

Sannan yamiƙa takardun ga Alƙali, shi kuma ya’amsa yana gyara glass ɗin sa yasoma dubawa, sannan yaɗago kansa yana cewa

“Lauyoyi zaku iya farawa”.

Khalil ne yatashi yasoma gabatar da kan sa

“Ni sunana “`BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA’UF.“` lauya me kare wacce takawo ƙara, tare dani kuma akwai abokan aikina..”.

“Brr. Tahir .A. Tahir”. Cewar Brr. Tahir kenan da shima yatashi yagabatar da sunan shi

“Tare dani Brr. Bilkisu Ahmad Sofana”.

Zama sukayi gaba ɗayan su.

“Ni kuma ni ne Brr. Mahmud Sudais, lauya me kare wanda ake ƙara, tare dani akwai..”.

“Brr. Shamsudden Munir”.

Su ma zama sukayi, Alƙali duƙar da kansa yayi yaɗan yi rubutu tukun yaɗago kai yana kallon su, hakan yasaka Brr. Khalil yamiƙe yasoma magana

“Ya me girma me Shari’a, ina son agabatar min da Nazeefa Shehu don in mata tambayoyi”.

“Kotu ta baka dama”. Alƙali yafaɗi hakan yana aje Bairo ɗin hannun sa

Maga-takarda yamiƙe yace “idan akwai Nazeefa Shehu anan tafito”.

Nazeefa da jikin ta yayi mugun sanyi, gaba ɗaya sai taji cikin ta yasoma rugugu ƙafanta kuma sai faman rawa suke yi don bata taɓa tsayawa cikin taron mutane ba, Mom dake kusa da ita tace

“Tashi kije mana, ki cire tsoro aran ki kinji”.

Gyaɗa kai kawai tayi taɗago tana kallon mutane nan idanun ta yafaɗa akan na Khalil, kafe ta da idanu yayi ko ƙiftawa baya yi hakan yasaka tamiƙe tafara nufo shi, tana isowa wani ɗan sanda yace tashiga nan”. Babu musu kuwa tashiga tatsaya kanta a ƙasa, takowa Khalil yayi ya’iso gaban ta

“Kotu zataso taji cikakken sunan ki”.

Bata ɗago kai ba tace “sunana Nazeefa Shehu”.

“To Nazeefa Shehu zan so in san menene alaƙan ki da wanda kika kawo ƙara, ina nufin Alh. Mubarak me kuɗi”.

Sai alokacin taɗago kanta tana kallon Khalil, yayi mata alama da ido, hakan yasaka tamayar da idanun ta kan jama’a sai kuma tasauke kanta tasoma bayani

“Muna aiki ne a ƙarƙashin sa”.

“Kenan kina nufin ke ƴar aikin gidan sa ne?”

Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace “Eh”.

“Ok zan so ki bama kotu taƙaitaccen labarin ki, da yanda har kuka zauna a gidan Alh. Mubarak”.

“Ni bansan sanda muka soma aiki a gidan sa ba, sabida alokacin bani da wayau sosai, sai dai a sanda mahaifina yarasu nasan sanda muka koma gidan sa da zama”.

Daga nan tasoma bada labari tiryan-tiryan abun da yafaru da ita a gidan, har sanda yaɗauke ta yakaita wani gida, zuwa taimakon da Khalil yayi mata har kawo iyanzu, tanayi tana kuka, sai da tagama bada labarin surutun mutane yasoma tashi, sai da Alƙali yabuga guduma kafin sukayi shiru

“Ya me girma me Shari’a iya tambayoyin da zan iya mata kenan” Khalil yafaɗi hakan kana yaje yazauna

Brr. Mahmoud ne yatashi

“Ya me girma me Shari’a ina so nayi ma Nazeefa Shehu tambayoyi”.

“Kotu ta baka dama”.

Ƙarisawa wajen ta yayi yana ƙare mata kallo, ita kam har yanzu kanta a ƙasa yake tana share hawaye, don haka batasan ma yanayi ba

“Malama Nazeefa zaki iya faɗa min iya adadin mutanen da suke aiki a ƙarƙashin Alh. Mubarak?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button