BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

Ɗago kanta tayi takalle sa sai tace “Eh zan iya, zamu kai mu Goma ne”.
Jinjina kansa yayi kana yace “A sanda Alhj. Mubarak yafita cikin motan yabaki umarnin kijira sa, meyasaka kika fito?”
“Wani ne yace min in zo yana kira na”.
“Kina nufin wani ne yajagoran ce ki zuwa ciki? Meysaka to kika bishi? Alamu sun nuna kenan ta yiwu wasu ne suka aikata miki hakan?”
“Ya me Shari’a Brr. Mahmoud yana ƙoƙarin canza mata tunani sannan yatilasta ta tafaɗa abinda bashi ne ba”.
Alƙali yace “kagyara tambayoyinka Barrister Mahmoud”.
“Ok ya Me Sharia”.
Sannan yamayar da kallon sa gare ta yaci gaba
“Ina jinki, kin tabbatar kinga Alh. Mubarak a wannan gidan koda kika shiga?”
“Eh na gansa alokacin da suka shigo shi da wani mutum har sukayi min allura”.
Jinjina kansa yayi kafin yajuyo yana kallon Alƙali yace
“Iya abinda zan iya tambayan ta kenan”. Sannan yaje yazauna
Miƙewa Khalil yayi yace “zan so a gabatar min da Alh. Mubarak Me kuɗi don amsa tambayoyina”.
“Kotu ta baka dama”.
Fito da Alh. Mubarak akayi, wasu ƴan sanda suka tsaya bayan sa
“Alh. Mubarak shin kasan wancan yarinyan?”.
Kallon Nazeefa yayi sannan yace “Eh na santa”.
“Menene alaƙan ka da ita?”.
“Babu wata alaƙa da nake da ita, illa ita ɗin ƴar aikin gidana ne”.
Jinjina kan sa Khalil yayi kana yace
“To yanzu ka yarda da abinda tafaɗa ko har yanzu kana tantama?”
“Ni ban yarda da abinda tafaɗa ba, coz ni ba mutumin banza bane da har zan yi wannan mummunan harƙallan”.
Murmushi Khalil yayi yace “kenan duk kanaso kace mana abinda ake zargin ka ba Gaskiya bane?”
“Eh ba Gaskiya bane, don Ni taimakon ta kawai nayi shine take so ta saka min da sharri”.
“Kamar ya taimakon ta kayi?”
“Eh lokacin da naganta a hanya shine naɗauke ta nakaita gida, shikenan iya abinda yahaɗa ni da ita”.
Khalil yace “a matsayin ka na babban mutum ka taho ka ganta a hanya, sannan kuma babu nisa da gidan ka da inda take, meysaka kayi sha’awan kaɗauke ta a mota ka ƙariso da ita gidan ka?”
“Kasan taimako ajinina yake don haka don na ɗauke ta na kawo ta gida wannan bazai saka a zarge Ni ba, sannan kuma ina tausayin ta ne saboda Mahaifiyar ta a gidana ta rasu”.
“Ya me girma me Shari’a iya tambayoyin da zan masa kenan,, sannan zan so abani dama nasake yin ma Nazeefa tambayoyi”. Khalil yafaɗa hakan sannan yakoma wajen zaman sa
Alƙali da yagama rubutu yaɗago kansa yace “ko lauyan da yake kare wanda ake zargi yana da abin cewa?”
Miƙe wa Brr. Mahmud yayi yace “A’a ya me Shari’a, sannan yakoma yazauna
“Kotu ta baka dama”.
Tashi Khalil yayi ya’isa gaban Nazeefa yace “zan so ki sanar dani tun sanda kika taso da wayon ki kika ganki agidan Alh. Mubarak masu aiki nawa ne aka sanja agidan? Ko waɗanda kika sani iya su ne agidan har tafiyan ki?”
Cikin sanyin murya Nazeefa tace “gaskiya tun zuwana gidan har sanda natafi masu aikin gidan waɗanda aka sauya bazan iya ƙirgawa ba, amma suna da yawa sosai”.
“Kenan kina nufin a gidan Alh. Mubarak ansha sauya masu aiki batare da wasu dalili ba?..”
Miƙe wa Brr. Mahmoud yayi yace “Of jection my Lord Brr. Ibrahim Khalil yana neman yaɗaura wacce yake karewa akan hanya”.
“Kakula Brr. Ibrahim”. Cewar Alƙali
“Nagode ya me Shari’a, ok ina jin ki, ko zaki faɗa min akwai wani laifi da kikasan suna yi ake sauya su?”
“A’a Ni bansani ba, haka kawai muke neman su mu rasa sai akawo sabbi”.
“Ok zaki iya komawa kizauna”.
Sannan yajuya ga alƙali yace “ya me Shari’a ina son nayi ma Malam Umaru tambayoyi”.
“Kotu ta baka dama”.
Maga-takarda yatashi yayi kiran sa sannan yafito
“Malam Umaru abaya na tambaye ka wasu tambayoyi, sannan nace idan da buƙatar nasake kiran ka zan sake”.
Gyaɗa kansa Malam Umaru yayi
“Yauwa a lokacin da Nazeefa tafita gidan Alh. Mubarak a matsayin ka na me gadi kana ina?”
“Ina bakin Gate ɗin tazo tafita”.
Kaɗa kansa Khalil yayi kana yaƙure sa da idanu yace “to kaga dawowan su kamar yanda Alh. Mubarak yafaɗa shine yadawo da ita?”
Hannu Malam Umaru yasanya yagoge zufan da yake tsatstsafo mishi kana yace
“Eh na gani”.
“Kana nufin sun dawo tare ɗin?”
“Eh tare suka dawo a motar sa bayan mituna ƙadan da fitan ta”.
Murmushi Khalil yayi yana sake tsare sa da idanu yace
“Ok to idan har kaga dawowar ta cikin gidan, to da yaushe kenan takuma fita?”
Malam Umaru yace “gaskiya ban sani ba”.
“A matsayin ka na me gadi ya akayi har mutum yafita cikin gidan baka sani ba?”.
“Eh.. uhm naje zagayawa ne ai, don haka bansan ta fita ba”.
“To a yaushe kafara jin ana cigiyar ta?”.
“Bayan sa’o’i uku da dawowar ta, sai Hajiya tazo tasame Ni take tambayana “har yanzu Nazeefa bata shigo bane?” Shine nace mata ai tun ɗazu Tawuce”.
Daga nan Brr. Kahlil zama yayi, sai Brr. Mahmoud yatashi shima yayi masa tambayoyi, Kana Brr. Kahlil yasake tashi yace
“Ina son inyi wa Hajiya Asiya Tambayoyi”.
“Idan akwai Hajiya Asiya tafito”.
“Zan so insan alaƙan ki da Alh. Mubarak”.
“Mijina ne”.
“Kun kai shekaru nawa dashi?”
“Mun kai shekaru 32yrs dashi”.
“Ok kin taɓa fuskantar wata matsala dashi? Kamar kina zargin sa da yana aikata wani abu a ɓoye batare da sanin ki ba?”
Kallon inda Alh. Mubarak yake tayi, sai tayuyo da kanta tare da sad da kan ƙasa tace
“Ni ban taɓa zargin sa ba, kuma Mijina baya ɓoye min komi”.
“Ok lokacin da kika ji shiru Nazeefa bata dawo miki aike ba, me kikayi akai?”.
“Nazo na tambayi me gadi sai yace min “tariga da tawuce ai”.
“Sannan kuma da kika koma nemanta kika yi ko me?” Khalil yafaɗa yana tsare ta da idanu
Yawu tahaɗiye kana tace “eh naje na neme ta ciki amma ban ganta ba”.
Murmushi Khalil yayi yajuya yana kallon Alƙali yace
“Ya me girma me Shari’a ko da wannan jawaban da Malam Umaru da Hajiya Asiya sukayi zai tabbatar da ƙarya suke yi, coz inda Nazeefa ta dawo gida kamar yanda sukace ya akayi aka rasa ta lokaci guda? Taya har zata fice gidan batare da wani ya ganta ba idan akayi duba da gidan na mutane ne, sannan idan akayi la’akari da Labarin da Nazeefa ta bayar za’a gane gaskiya take faɗa, sannan kuma ansha neman masu aikin gidan Alh. Mubarak ana rasa su lokaci ɗaya batare da wasu dalili na laifi da suka aikata ba, sai dai aga an kawo sabbi, ko anan ya me Shari’a yakamata asan cewa Alh. Mubarak yana amfani da wannan daman ne wajen ɗaukan yaran mutane yana safaran su zuwa wani ƙasa, Nagode ya me Shari’a”.
Komawa yayi yazauna, sai da Alƙali yayi rubutu kana yace
“Brr. Mahmoud ko kana da tambayan da zakayi?”
“A’a ya me Shari’a”.
Rubutu yasake yi sannan yaɗago yana kallon Brr. Khalil yace
“Zaka iya ci gaba da bada shaidun ka”.
Miƙewa Khalil yayi yana sakin wani kyakykyawar murmushi kana yace
“Ya me Shari’a abani dama Brr. Tahir zai je yazo da shedata ta gaba”.
“An baka dama”.
Miƙewa Brr. Tahir yayi yafita, bayan kamar mituna 3 sai gasu sun shigo da wani mutum, dasauri Alh. Mubarak dake tsaye tsakankanin ƴan sanda yaɗago idanun sa kamar wanda zasu fito waje yana kallon mutumin.
_To fa wanene wannan mutumin?_
[9/29/2020, 1:10 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*