BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 21 to 30

“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 32*
Alh. Mubarak murmushi yasaki, coz yasan da cewa babu abinda Brr. Khalil zai samu a wajen mutumin, sabida sun riga da sun biya sa zunzurutun kuɗi kuma yayi musu alƙawarin bazai taɓa tona musu asiri ba
Ƙarisawa gaban sa Brr. Khalil yayi yace “kotu zata so tasan ainihin sunan ka da sana’ar ka?”
“Sunana Aliyu Gusau, amma amfi sanina da Gadanga, kuma sana’a ta shine gadi”.
“Madalla.. to zan so kafaɗa min wa kake ma gadi?”
“Ina yiwa Alh. Mubarak da Dr. Sabit gadi ne”.
“Ma’ana kana nufin kana aiki a gidan Alh. Mubarak sannan kuma kana aiki gidan Dr. Sabit?”
Girgiza kan sa yayi kana yace “ina musu gadi ne a wani gidan su dake Sabon layi G.R.A”.
Brr. Khalil yace “to zan so kasanar da kotu abinda kasani a waɗannan mutanen biyu da ka lissafo”.
“Da farko dai Ni me gadin gidan ne, kuma shekaruna 20 ina tare da waɗannan mutanen, abinda nasani shine suna kawo mata gidan suna ajiye su, kuma Ni ne jagoran da nake taimaka musu wajen tsare musu Matan da suke kawo wa, sannan Ni ke basu abinci a ko yaushe”.
Murmushi Brr. Khalil yayi yace “ina jin ka, daga nan kuma ya ake yi dasu?”
“Dr. Sabit shi ke musu allura sannan yasaka musu Coken acikin su, bayan kamar mintuna 20-30 za’a zo da motoci a tafi dasu, suna safaran su zuwa wasu ƙasashe ne, Ni iyakan abinda nasani kenan”.
Still Murmushi Brr. Khalil yayi kana yace “ita kuma Nazeefa ya akayi tabar gidan batare da sanin ku ba?”
“A lokacin Dr. Sabit ya aike Ni zuwa gidan sa don naɗauko wasu yara, to ina tunanin a lokacin ne tafita don basuyi zaton zata iya farkawa a time ɗin ba”.
Gaba ɗaya kotun ne yahargitse da surutu sai hayaniya ake yi, shi kuwa Alh. Mubarak tun sanda yaji Gadanga yana zayyano bayani yarufe idanun sa yana jin wani baƙin ciki a ransa, saɓanin Dr. Sabit dake zaune cikin mutane, be taɓa tunanin asirin sa zai tonu ba da be zo wajen ba, sosai yashiga firgici don yasan yau kashin su ya bushe tasu ta ƙare
Brr. Khalil yace “ina son kotu tabani dama zan kira Dr sabit don amsa tambayoyi”.
“Dr. Sabit zaka iya fitowa gaban kotu”.
Jiki a sanyaye yafito yana gyara glass ɗin idanun sa duk zufa ya jiƙa masa fuska, matsowa kusa dashi Khalil yayi yace
“Dr. Sabit shin me zaka iya cewa game da bayanin Gadanga?”
Shiru yayi yana sad da kai ƙasa, gaba ɗaya hannayen sa rawa suke yi don be san kuma abinda zai iya cewa ba, “shin yaƙaryata abinda aka faɗa akansa ne ko ya?”
“Dr. Sabit kai muke sauraro, kana da abin cewa ko kuwa ka yarda da zargin da ake muku?”
“Eh.. eh na amince mun aikata duk abinda ake zargin mu dashi..”
“Ƙarya ne wlh ƙarya yake min ni dai, Ni ban amince da abinda yafaɗa ba”. Cewar Alh. Mubarak gaba ɗaya yazama tamkar zararre, sai ƙara maimaita abinda yafaɗa yake yi
Buga guduma Alƙali yayi yace “ya isa Alh. Mubarak, nan kotu ne Yakamata kanutsu kasan me kake yi”.
Sai alokacin yayi shiru yana share zufan dake keto masa, mutane kuwa sai faɗin albarkacin bakin su suke yi, sai da Alƙali yasake buga guduma sannan suka nutsu, takowa Brr. Khalil yayi zuwa tsakiyan kotun yana cewa
“Ya me girma me Shari’a sai kuma Shaidata ta ƙarshe, abani dama in gabatar da Fadila Muhammad”.
“Idan da Fadila Muhammad tafito”.
Baby Dil dake zaune can baya tamiƙe tataho, sai da idanun kowa yakoma kanta coz yanda take tafiya cike da yanga, wanda kallo ɗaya zakayi mata kagane ita ɗin ba ƙaramar gogaggiyar ƴar duniya bace, duk a yanzu ɗin tayi shigan mutunci, but hakan be hana bayyanuwan Tatue ɗin dake zane a jikin ta ba, ƙarisawa tayi tasaya kamar yanda kowa ke yi, sannan shi kuma yatako kusa da ita yana faɗin
“Fadila zan so kisanar da Kotu sunan ki da inda kike?”
Murmushi tasakar masa kana takalli dandazon mutanen wajen tace
“Sunana Fadila kuma Ni ɗin ƴar garin Kano ce, but ina zaune a EGYPT yanzu, kuma daga can nadawo nan”.
“Ok shin ko kinsan Alh. Mubarak me kuɗi?”
“Ƙwarai kuwa nasan shi tun shekaru 7 da suka wuce, yana yawan zuwa EGYPT wajen uban gidan mu”.
“Shin menene alaƙan shi da uban gidan naku? Kuma kinsan me yake zuwa yi?”
“Eh na sani, yana siyar wa da Mr. Jay pitter ƴan mata, shi kuma sai yazamar dasu karuwai”.
Murmushi Brr. Khalil yayi yace “mun gode Fadila, zaki iya komawa kizauna”.
Sannan yajuya ga wajen zaman sa, kallon Brr. Bilkisu yayi yai mata alama da ido, sai tamiƙo masa wasu Files, amsa yayi yadawo tsakiyar kotun yana cewa
“Waɗannan Files ɗi su ne duk wani shaidu da ke kan Alh. Mubarak me kuɗi na zuwan sa EGYPT da safaran ƴan mata da yake yi duk suna cikin nan”.
Sannan yamiƙa ma Maga-takarda yaci gaba da faɗin
“Da wannan nake roƙon kotu da tayanke wa Alh. Mubarak da Dr. Sabit da duk wasu waɗanda suke da hannu aciki hukunci dai-dai da abinda suke aikatawa, Nagode ya Me Shari’a”.
Zama yayi, Alƙali yakalli Brr. Mahmoud yace
“Kana da abin cewa Brr. Mahmoud?”
Miƙe wa yayi yace “a’a ya me Shari’a, sannan yakoma yazauna
Rubutu yasoma yi Alƙalin kafin yaɗago kansa yana kallon mutanen wajen yace
“Abisa zargin da ake ma Alh. Mubarak me kuɗi tare da abokan aikin sa bisa ga tarin hujjoji da aka gabatar, kotu ta gamsu kuma ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Alh. Mubarak me kuɗi tare da Dr. Sabit, sakamon kama su da yin babban laifi na safaran mata tare da raba su da iyayen su amaishe su karuwai, sannan tare da laifin siyar da Coken, zasu ƙare rayuwan su cikin Jail tare da horo me tsanani, sannan kuma zasu biya taran Miliyan biyar ko wannen su, sannan kotu ta yanke ma Aliyu Gadanga ɗaurin gidan kaso na shekara 10 sakamakon da hannun sa cikin aikata laifin, wannan shine sakamakon hukuncin da suka aikata”.
Daga nan Alƙali yabuga guduman sa yamiƙe tsaye, gaba ɗaya mutanen wajen suka miƙe suna me faɗin “Kooooooootuuuuuuu”.
Hayaniya wajen yakaure dashi yayinda mutane ke ta turuwan ficewa, alokacin ne kuma ƴan sanda suka taso ƙeyan su Alh. Mubarak zasu tafi dasu, iyalan su in banda kuka babu abinda suke yi
Brr. Khalil kuwa tun aciki yasoma gaisawa da mutane ana masa murna sai zuba murmushi yake yi, koda suka fito waje nan ƴan jarida sukayi masa caaa, dasauri Kausar tature mutane tamatso kusa dashi tana cewa
“Brr. Zamu so kasanar mana wani irin farin ciki kake ji yayinda kayi nasara a wannan gagarumar shari’ar?”
Murmushi yasakar mata kana yace “Farin ciki mara misaltuwa, ko ba komi yau na kawo ƙarshen wasu daga cikin mugayen ƙasar mu, kuma ina roƙon Allah yatona asirin duk waɗanda suke da hannu a ɗaukan ƴaƴan mutane suna fita dasu wasu ƙasan don karuwanci”.
“To wani jan hankali kake dashi a gare su?”
“Su tuna cewa su ma suna da ƴaƴa, idan hakan tafaru dasu bazasu ji daɗi ba, idan har basu tuba sun dena wannan banzan harƙallan ba to da sannu zasu girbe abinda suka yi sannan ƙarshen su bazai taɓa kyau ba”.
Wasu tambayoyin suka soma mishi amma yayi gaba abin sa batare da ya amsa musu ba
“BARRISTER”.
Yaji an kira sunan sa daga bayan sa, juyowa yayi yana kallon ta sai yasakar mata murmushi, ƙarisowa tayi wajen itama tana murmusawa tace