Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Tana shiga ɗakin tafaɗa kan Halwa dake barci, hakan yasaka Halwan tafarka tana kallon ta da idanuwanta da sukayi ja, cike da tsananin farin ciki Saleema tace”Wayyo Allana yau ina farin ciki sosai kitashi ki tayani murna”.

Ahankali Halwan tatashi zaune tana ci gaba da kallon ta tace “me yafaru ne Sister?”

Murmushin da yabayyana haƙoran ta tayi tace “kinsan me Abba yazo da maganar aure na Ni da ɗan Abokin sa”.

Waro idanu Halwa tayi tana kallon ta, sai kuma tayi dariya tace “shine yasaka ki farin ciki?”

Gyaɗa kanta tayi tana sake washe bakin ta tace “eh mana abin ne ya matuƙar bani mamaki, ban taɓa tunanin wannan ranan ba, ban taɓa tunanin Ni Saleema ina da matsayin da zai sa ace yau zan zama matar Barrister ba, Mutumin da ko magana ban taɓa samu ya haɗani dashi ba, ada nayi burin ace Barrister ya zama nawa but ko kaɗan babu hanyan da naga yiwuwar hakan, amma yanzu kiji abin mamaki sai gashi lokaci ɗaya Allah ke ikon sa wai ni ce yau ake son haɗa ni dashi, abun sai kace amafarki wlh”.

Yanda taƙarike maganar nata ne yaba Halwa dariya, sai da tadara kafin tace “to menene aciki? Ni a ganina banga Namijin da yafi ƙarfin ki ba, kar ki manta kema fa kina da kyau da haɗuwar da ko wani namiji zai yi fatar samun ki, ki dena zuzuta shi da yawa don nasan bazai fi ki da komi ba”.

Saleema tace “uhmmm baza ki gane bane Sister, ko wace mace idan har tagan shi zata so yazama shine Mijin ta, ba wai don haɗuwan sa ko kyawun sa ba amma yana da nagartan da idan har kin ganshi kema wlh sai kin so shi, domin bakiga yanda mata suke rushing akan shi bane”.

Taɓe baki Halwa tayi tana kallon ta tace “da alamu dai kina son sa da yawa, amma to kina ganin shima yana ciki?”

Zaro idanu Saleema tayi tace “hmm mutumin da ban taɓa magana dashi ba taya kike tunanin yana sona? I Think ko sanina be yi ba”.

Shiru kawai Halwa tayi tare da tunanin Nura aran ta

“Burina a rayuwa shine in Sami Miji tamkar Barrister sai gashi shi ɗin na samu, nasan ko baya so na watarana zai ƙaunace ni domin kuwa zan yi duk abinda yake so”. Saleema taƙarike maganar tana rufe fuskarta cike da farin ciki

Buɗe fuskar tayi tana kallon Halwa da tafaɗa tunani, sai tataɓo ta tana cewa “Sister lafiya tunanin me kike yi?”

Ajiyan zuciya Halwa tasauke kana tace “Babu”.

Murmushi tayi tace “to faɗa min kema, menene burin ki a rayuwa?”

Shiru Halwa tayi tana kallon ta batare da tace komi ba

“Sister kisanar min mana kinji?”

Duƙar da kanta tayi tana murza ƴan yatsun hannayen ta masu tsawo da burgewa kana taɗago kanta tana kallon Saleema da murmushi a fuskarta tace “ada bani da wani buri a rayuwa sama da inyi aure in ganni gidan Yaya Nura amma..”

Shiru tayi tana kawar da kanta kana taci gaba da cewa “amma a yanzu Burina inyi karatu me zurfi in zama lauya ko dan naɗau fansar abinda Haris yayi min”.

Ɗaura hannun ta Saleema tayi akan na Halwan tana cewa “meyasaka kike Son ɗaukan fansa? Meyasaka baza ki barshi da Allah ki manta dashi cikin rayuwan ki ba? Idan har kikace zaki ɗau fansa hakan na nufin kenan zaki riƙa tuna sa har zuwa wani lokaci?”

Halwa tace ” Ni kaina nayi tunanin barin shi da Allah kamar yanda tun farko nabar shi, amma yanzu wani tunani yazo min arai saboda shigan ciki a gare ni, idan har nahaifi abinda ke cikina dole ne watarana yatambaye Ni “ina Mahaifin sa?” kina tunanin wani amsa zan bashi?”

Taƙarike maganar hawaye na cikowa cikin idanun ta, kana taci gaba da cewa

“Wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin na zama lauya don nan gaba na kaisu ƙara kotu domin hakan ne kaɗai zai saka gidan su Haris su amshi abinda nahaifa, baza su taɓa amsan abinda zan haifa ta daɗin rai ba dole sai ta wannan hanyan”.

Numfashi taja me ƙarfi still taci gaba da faɗin

“Burina na biyu shine in San meyasaka Yaya Nura yajuya min baya? Ina son in San dalili ina son insan meyasa?..”

Sai kuma tasaki kuka me ƙarfi, cikin rawan murya tace “na.. na kasa yarda cewa Ya..ya Nura zai juya min ba..ya, zuciyata takasa amince wa da hakan..”

Kasa ci gaba tayi da magana dole yasaka tayi shiru, rungume ta Saleema tayi cike da tsananin tausayin ta tace

“Kiyi shiru don Allah Sister ki dena kuka kinji? Ni nan zan taimake ki wajen cika burin ki, in Allah ya yarda zaki cika burin ki, zanyi wa Abbana magana zai saka ki aduk makarantar da kike so a faɗin duniya domin cikar burin ki, please ki dena kuka”.

Shiru Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya, ɗago kanta Saleema tayi tasaka hannu tasoma share mata hawaye.

               *****  

     *TWO WEEKS*

Khalil ne zaune ƙasar Roll ɗin parlour’n sa, daga shi sai gajeren wando fari da baƙin t.shirt, gaban sa takardu ne masu yawan gaske yake dubawa, gefe kuma Kausar ne kan kujeran da yajingina bayan sa tana ɓare maggi dake cikin Vowel

A ɗan wannan lokacin sosai suka shaƙu da juna kullum Kausar tana gidan, ita take mishi girki da gyaran gidan, su zauna suyi ta hira kamar wanda suka daɗe da sanin juna, yanzun ma hiran suke yi aciki yasako mata maganar auren sa da zai yi

Ɗan kallon ta yayi yana smile yace “kin kusa hutawa dai duk ranan da akace nayi aure, babu ke babu ɗawainiya dani”.

Tsayar da abinda take yi tayi tana ɗago kanta takalle shi, kana cikin rashin fahimta tace “ban gane ba?”

Ɗan taɓe bakin sa yayi yana kawar da kai yace “nan ba da jimawa ba zanyi aure..”

Ɗif Kausar tayi gaba ɗaya tadena jin abinda yake cewa, maggin kawai take ɓarewa amma batasan ma takamaiman a halin da take ciki ba, sai da yagama maganar sa kana yajuyo yana kallon ta, ganin kamar tayi nisa a tunani sai yakau da kansa yaci gaba da abinda yake yi

Ita kuwa sosai tashiga ruɗu da jin abinda yafaɗa, ba don komi ba sai don ƙaunar da tatsinci kanta dumu-dumu aciki tana yi masa

Nocking ɗin da akeyi ne yadawo da ita hankalin ta

Khalil yace “Yes Come in”.

Brr. Tahir ne yashigo ciki da sallama, sauke idanun sa yayi akan su yana bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo cike da tsananin mamaki da al’ajabi, Kausar itama shi take kallo sai dai kawai kallon nasa take yi but tunanin ta yana wani wajen daban, maganar Khalil ne kawai ke mata yawo a tsakar kai

“Lafiya katsaya nan? Kashigo mana”. Cewar Khalil kenan yana kallon sa

Ahankali Brr. Tahir yasoma takowa yana shigowa, sai da ya’iso wajen yazauna saman sofa kana Kausar tamiƙe tsaye da hanzari tana ajiye Vowel ɗin hannun ta asaman Centre table, kallon Khalil tayi fuskarta babu walwala tace

“Zan je gida”.

Shima ɗin kallon ta yake yi cike da mamaki, sai kuma bai iya cewa komi ba in banda gyaɗa mata kai da yayi, ita kuma tajuya tayi hanyan ƙofa dasauri yayinda Brr. Tahir yaraka ta da idanu, sai da tafice kana yamayar da kallon sa ga Khalil yace

“Kai Man ina kasamo wannan Babe ɗin? Shin anya ba idanuna bane ke min gizau?”

“Kamar ya?” Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗago kansa yakalle sa

_plz Share????????_

[11/1/2020, 9:10 AM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

⚖

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button