BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

“Yauwa Nazeefa bakije kinga Amarya ba ga ta can an kawo ta?”.
Murmushi Nazeefa tayi tasauke kai ƙasa tace “Mom banji bane barci ya soma ɗauka na”.
“To tashi kije wajen ta tana nan aɗaki sai ki tayata zama ko”.
Batayi musu ba tatashi sai dai bada son ranta ba tafito tanufi ɗakin Mom ɗin, ita kuma Mom tanufi wajen Dangin ta
Sallama tayi tatura ƙofan tashiga, Saleema dake zaune saman gado ta’amsa mata tana ɗan jan Hijabin ta baya da tarufe idanun ta dashi, kallon kallo sukai ma juna ko wacce da tunanin dake ranta
Ita Nazeefa tana kallon Amaryan Yayan nata ne cike da jin haushi duk da kuwa ta burge ta don kyakkyawa ce sosai wacce kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa ba ƙaramar ƴar jindaɗi da hutu bane, coz ko kaɗan ma batayi yanayi da ƴar talakawa ba
Ita kuma Saleema tana mata kallon rashin sani ne don tasan dai ba ƴar gidan bace, sai dai ko ƴar uwan shi ne duk da babu wani kama da sukayi
Zama tayi akan kujeran dake ɗakin tana ci gaba da kallon Saleeman sannan taƙaƙalo murmushi tace “sannu Amaryan mu, kinzo lafiya?”
Murmushi itama Saleema tayi ta’amsa mata cike da sakin fuska kasancewar ta me yawan fara’a ga kowa
Daga haka shiru ne yabiyo baya dan Nazeefa batasan me zatace mata ba saboda ita ba me yawan surutu bane, itama kuma Saleeman bata sake furta komi ba tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, ahaka har Mom tashigo da wasu baƙi tatarar dasu haka, baƙin sun zo ganin Amarya ne, haka Saleema tagaishe su cike da kunya su kuma suna ta yaba mata suna sanya alkhairi, hakan ba ƙaramin sake ƙular da Nazeefa yayi ba har takasa jurewa tatashi tasulale ɗaki batare da sanin Mom ba
koda Mom suka tashi fita bata kula ba haka suka fita ɗakin aka bar Saleema ita kaɗai tana ta zaune, daga ƙarshe kwanciya tayi sabida yanda take jin zazzaɓin jikin ta yana ƙara yawa, lokaci ƙanƙani ciwo yarufe ta ga sanyi da take ji sosai, haka ta ƙudundune jikinta sai faman maƙyarƙyata take yi
Ahaka Mom tashigo taganta, hankalin ta idan yayi dubu ya tashi nan tasoma neman wayan ta, sai tatuna tabar wayan a palrour, fita tayi dasauri babu jimawa sai gata ta dawo tare da wasu mata su biyu, su ma duk hankalin su ya tashi ganin yanda jikin Saleeman yai zafi zauuu
Mom Kiran Khalil tayi tabashi umarnin yai maza-maza yazo matar sa tana gidan ta babu lafiya.
[11/7/2020, 3:33 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 44*
Lokacin da Khalil yazo har su Mom sun fito da ita parlour, babu ɓata lokaci yariƙe ta suka fito waje inda motan sa yake, Mom tace mishi “yakai ta asibiti” amma ita Saleeman tace “tana da maganin ta a agida” don haka gida kawai yanufa
Suna zuwa yayi parcking yafito yabuɗe mata motan yariƙo ta tafito, duk da a halin ciwo take amma sosai taji daɗin kusancin sa gare ta, har wani sanyi take ji aranta tana jin kamar ciwon na son tafiya
Tana jingine da jikin sa har suka isa parlour yataimaka mata tazauna sannan yakalle ta cike da tausayi yace
“Ina kika ajiye maganin in ɗauko miki?”
Cikin muryan marasa lafiya tace “yana cikin trolly na Wanda nazo dashi daga gida”.
Gyaɗa kai kawai yayi yanufi ɗakin nata, yana shiga yasoma wurwurga idanu, can yahangi akwatunan da yayi mata guda shida, sai yamaida idanun sa kan wani babba kalan sa daban, yana da tabbacin shine wanda take nufi
Wajen yanufa yabuɗe, duk abubuwan amfanin ta ne da tazo dashi daga gida, yana soma bincika wa yaga ledan maganin, ɗauka yayi yanufi parlour’n
Zama yayi gefen ta yabuɗe tare da nuna mata alamun tayi masa bayani, nuna masa waɗanda zata sha ɗin tayi yaciro yamiƙa mata sannan yatashi yaje yaɗauko ruwa a Fridge yabata
Har tagama sha yana ta kallon ta kamar wanda zai haɗiye ta, hakan yasa taji kunya tana sad da kanta ƙasa, be san sanda yasaki guntun murmushi ba yamiƙe tsaye yanufi kichen ita kuma tabi bayan sa da kallo cike da tsananin ƙaunarsa a ranta
Be wani jima ba yadawo riƙe da Cup a hannun sa, miƙa mata yayi yana tsaye a kanta, ita kuma tasaka hannu ta’amsa tana kallon abinda ke ciki, Tea ne yahaɗo mata, be ce mata komi ba sai dai kallon ta da yake yi har tashanye tatashi da ninyan kai Cup ɗin
“No kawo cup ɗin, je ki kwanta idan an kira sallah zan tashe ki”.
Babu musu tanufi ɗakin ta tashige, shi kuma bayan ya kai Cup ɗin kichen yadawo yanufi ɗakin sa, ɗakin karatun sa yashige (Library) yasoma binciken abinda yakawo sa, har aka kira sallan azahar yatashi yagabatar yakoma yaci gaba da aikin sa, yana tune da Saleema sai dai yaƙi tashin ta ne saboda bata daɗe ba aka kira sallan, don haka yabari zuwa sallan Asar yatashe ta
Sai da aka kira sallah yafito yashiga Toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yana warware hannun rigan sa da yanannaɗe wajen yin alwalan, yafito daga ɗakin nasa yashiga ɗakin Saleema, yana shiga ya’isa bakin gadon yatsaya yana kallon ta, barcin ta take yi cikin kwanciyan hankali, sai dai yanda take fitar da numfashi da ƙarfi hakan zai sa kagane ba lafiya ba
Ya daɗe atsaye a wajen yana kallon ta cike da tsananin tausayin ta, yasan da cewa tana fama da ciwo tunda lokacin gab da za’ayi auren su Abbanta yakira sa musamman don su tattauna matsalan Saleeman, anan yake faɗa masa komi kuma yaɗaura da roƙon sa akan don Allah yariƙe masa ƴa bisa amana
Ajiyan zuciya yasauke kana yasaka zara-zaran hannun sa me yalwataccen gashi a kwance yasoma tadata, pilon yake ɗan ja ahankali yanda zata iya tashi, kasancewar bata da nauyin barci hakan yasa yana soma taɓa wa tabuɗe idanunta da sukayi ja alamun barcin yayi nisa sosai, suna haɗa idanu tayi saurin yunƙurin tashi amma yanda jikinta be da ƙarfi dole takoma takwanta tana sake rufe idanunta
“Ya jikin naki?” Yafaɗa ahankali cike da kulawa kuma har alokacin idanun sa na yawo a jikinta
Bata buɗe idanun ta ba tace “da sauƙi”.
Gyaɗa kansa yayi kafin yace “ki tashi kiyi sallah”.
Daga haka yajuya yafita batare da yajira me zatace ba
Sai da tatabbatar ya fita kafin tabuɗe idanun nata cike da kasala tatashi zaune tana riƙe kanta, babu ƙarfi ko kaɗan ajikin ta ga kuma kanta dake faman ciwo baya ga haka babu komi yanzu dake damun ta, waigawa tayi taɗauki wayan ta dake kan drowan Gadon taduba lokaci, zaro ido tayi tana kallon wayan cike da mamaki, batayi tunanin har tayi barci me nisa haka ba tunda har gashi ƙarfe 04:07pm.
Ajiye wayan tayi tazuro ƙafafuwan ta ƙasa tasauko, Toilet tanufa taɗauro alwala tafito tasanya Hijab ta tada sallah, azahar da la’asar tayi sannan tacire Hijabin ta’ajiye, wanka tashiga tayi don tasami ƙarfin jikin ta, tana fitowa tashirya cikin jan atamfa me ratsin baƙi da fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yayi mata kyau sosai sai zuba ƙamshi take yi, ɗankwali kawai taɗaura tafito Parlour