Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Yana zaune saman kujera yana latsa wayan sa, ƙamshin turaren ta yasa shi ɗago kai yana kallon ta, sosai yake bin ta da idanu sabida tayi masa kyau ainun

Ita kuwa bata kula dashi ba sai faman gyara zaman ɗankwalin ta take yi da be gama zama da kyau ba, sai da ta’iso cikin parlour’n kafin taɗago kanta su haɗa idanu, yanda yake kallon ta ne yasa ta jin kamar tajuya takoma amma babu hali dole ta’iso tazauna can kujeran da ke gefen sa, hakan yasa babu yanda za’ayi yaganta dole sai idan ya juya kansa

Ɗan lumshe idanun sa yayi yabuɗe yaci gaba da latsa wayan sa, amma yanda turaren ta ke shiga masa ƙofofin hanci hakan yasa duk yarasa tunanin sa, sosai turaren yayi masa daɗi, sai lumshe idanu yake yi yana buɗewa, daga ƙarshe yaɗago kai yana kallonta yace

“Kin sha maganin ki?”

Ita da taɗan buga tagumi tana tunani nan taji saukar muryan sa a kunnen ta, tayi saurin ɗagowa tana kallon sa kafin tace “a’a sai anjima ne lokacin sha”.

Be ce komi ba yakau da kansa yaci gaba da latsa wayan, dama chatting yake yi da Brr. Tahir, ganin dai turaren duk ya ishe sa da ƙamshi hakan yasa yatashi yanufi ƙofa yafice

Tabi bayan sa da kallo tana tunanin inda zai je

Yana fita Garden ɗin gidan yanufa yazauna kan fararen kujerun dake wajen, lumshe kyawawan idanun sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, hannu yasaka yana dafe setting zuciyar sa tare da faɗa wa duniyar tunani

Har yau ya gaza gane meke damun sa, meyasa yake shiga damuwa akan abinda baya tunanin zai sake gani, kullum zuciyar sa ƙulafucin ranan da yakasa mantawa yake yi tare da fatan sake ganin makamancin ta

Numfashi yaja tare da fesarwa yana ci gaba da latsa wayan sa, be tashi a wajen ba sai da yaji kiran sallah, miƙe wa yayi yasaka wayan sa a aljihu yanufi wajen Me gadi, anan yayi alwala yafita masjid, sai da akayi isha’i kafin yadawo gida

Tana nan zaune a parlour’n, sallah kawai taje tayi tadawo tasake zama, sai dai yanzu kallo take yi, yana shigowa ta’amsa masa sallaman sa tare da yin masa “sannu da zuwa”

Amsa mata yayi yana kallon ta kafin yanufi ɗakin sa yaɗauko car keey yafito yafice

Mintuna goma da fitan sa yadawo riƙe da Ledoji, miƙa mata yayi yace “tasake abincin dake cikin Take-away ɗin a plate” ta’amsa tayi yanda yace sannan tadawo takawo masa, umartan ta yayi tazauna su ci, babu musu tazauna suka ci abincin suka gama sannan tatashi takwashe komi takai kichen, dawowa tayi tazauna taci gaba da kallon ta yayinda shi kuma yana ƙasa har yanzu yana danna waya, babu jimawa kuma yamiƙe yashiga ɗakin sa yaɗauko computer’n sa yadawo yazauna kan kujera yasoma aiki aciki

Har barci yakwashe Saleema a wajen yana nan yana aikin sa, sai wajen ƙarfe 11:00pm. Sannan yadakata yana kallon ta, hakan yasaka yamiƙe ba don ya gama aikin ba yatattara kayan sa yamayar ɗaki yadawo yatashe ta yace “su je su kwanta”. Bayan shi tabi suka shige ɗakin sa yarufo ƙofa.

.

***** ****** ****** ****

Yau a makare suka tashi sai ƙarfe 11:30am. Sannan Khalil yasoma farkawa, wanka yayi yafito yana tsane jikinsa, alokacin ne Saleema tafarka itama sai dai taƙi tashi bare tanuna alamun ta farka, har yagama shiryawa yafita parlour yazauna, Kallo yakunna yasaka tashan CCT.V NEWS yana kallon labarai, jefi-jefi kuma yana latsa wayan sa

Ƙaramar wayan sa dake ajiye ne tayi ƙara yaɗauka yana karawa a kunne tare da yin sallama

Brr. Tahir amsa mishi sallaman yayi yana faɗin “Ango Ango kasha ƙamshi”.

Murmushi Khalil yayi yana shafo kwantaccen gashin kansa yace “zaka fara ko?”

Dariya Brr. Tahir yaƙyalƙyale dashi yana cewa “iyeee Ango uhmm Ango Mijin Amarya..”

Katse shi Khalil yayi yana ɗaure fuska

“Wai kai meye haka ne kanka ɗaya kuwa?”

“Uhmm ai baza ka gane kaina ɗaya ba sai idan nazo ganin Amarya”. Cewar Brr. Tahir Yana sake sakin dariya me sauti

Shiru Khalil yayi be sake ce masa komi ba sai yamayar da hankalin sa kan kallon sa

“Hello kana jina kuwa?”

Guntun tsaki Khalil yaja yana faɗin “ina jinka mana idan ka gama zan kashe wayana”.

Brr. Tahir murmushi yayi yace “sorry Man akwai magana fa, kasan narigada naga gidan da mutumin nan yake zaune sai dai be bani dama har yanzu mun tattauna ba”.

Khalil ɗan tattaro naman goshin sa yayi cike da takaici yace “yana son Raina mana wayau ne fa, but bari dai in taho sai mu tattauna don nima na samu ƙwaƙwƙwaran hujjan da dole sai ya saurare mu”.

“Ok sai ka zo”.

Daga haka sukayi sallama yaciro wayan daga kunnen sa yana miƙe wa tsaye yakoma ɗakin sa, abubuwan da zai buƙata yaɗauka sannan yanufi wajen gadon sa yana kallon Saleema da har yanzu tana nannaɗe acikin bargo taƙi tashi, yasan da cewa tun ɗazu ba barci take yi ba don haka yamatso gab da ita yaraɗa mata

“Ni na fita bazan daɗe ba zan dawo, ki kula da kanki uhmm?”

Tun sanda yasoma mata magana tabuɗe idanu tana kallon sa, sai tasaki murmushin da yakufce mata batare da ta shirya yin sa ba tayi saurin gyaɗa masa kai

Shima murmushin yayi bece komi ba yajuya yafice tabi bayan sa da kallo.

[11/7/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 45*

Minti goma da fitan shi kafin tamiƙe tasauko daga gadon, Toilet ɗin sa tashiga tayi wanka tasaka towel ɗin sa tafito tanufi ɗakinta, akan stool tazauna gaban dressing mirror tasoma shafa Lotions a tattausar farar skin ɗinta, shafa Lotions ɗin take yi but hankalin ta baya wajen, sai faman zuba murmushi take yi cike da tsananin nishaɗi da kallo ɗaya kayi mata zaka fahimta, har tagama batasan a wani duniyar take ba, hakan yasa tashafe fiye da awa ɗaya tana abu ɗaya, daga ƙarshe tamiƙe tanufi wajen kayan ta tazaɓo wanda zata saka

Jan Material Less me stone ajikin sa, ɗinkin doguwar riga pitted, yayi mata kyau sosai ya kamata cif-cif cike da sha’awa, tayi wannan ɗaurin na ture gaka tsiya sai ƙamshin amarci take zabgawa

Fitowa tayi takoma ɗakinsa tagyara tasaka air freshener, har toilet sai da tawanke kafin tafito tazauna aparlour takunna t.v

Zaman ta babu daɗewa tajiyo Nocking, miƙewa tayi tanufi ƙofan don tasan ba Khalil bane, tana buɗe ƙofan idanuwan ta suka faɗa cikin na Halwa dake tsaye tana zabga mata murmushi, tana riƙe da Husna da hannu ɗaya rungume ajikinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ɗan ƙaramin trolly

Cike da tsananin murna Saleema tatarbe ta tana rungume ta daga ita har Husnan dake barci

Daga ƙarshe shigowa sukayi suka yada zango a parlour’n bayan Saleema ta amshi Husna ta shimfiɗe ta akan kujera

“Sister kinga yanda kika sauya kuwa? Sai ƙyallin amarci kike yi sai dai fa kin rame”. Cewar Halwa da tazuba mata idanu tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button