Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Itama Saleema dake faman zabga murmushin tace “Hmm Ni dai bana son sharri, duka yaushe nayi auren da zakice ina ƙyallin amarci”.

“Allah kuwa dagaske my Sister kin sauya sosai, gani nake kamar na shekara ban ganki ba saboda tsaban kyau da kikai min, gaskiya aure rahma ce”.

Dariya Saleema tayi wannan karon tace “Allah ko ƴar uwa?”

Ɗage gira ɗaya Halwa tayi tace “dagaske My Sister”.

“To kice kema kin kusa motsawa musha biki?”

Ɓata fuska Halwa tayi tana sauya zancen da faɗin “ƴar uwa nifa ba zama zanyi ba don tare da drever nake zai kai ni School, ƙarfe 02:30pm nake da Exams, Ina Mijin naki mu gaisa kafin in tafi?”

Saleema tace “ya fita yanzu”.

Murmushi Halwa tayi tana kama haɓa tace “har ya gama cin amarcin ne ya soma fita?”

Hararan ta kaɗai Saleema tayi tana wani irin murmushi da bakinta yaƙi rufuwa

“To sister zan tafi kinga lokaci ya ja da yawa, akwai saƙon Ummi cikin jakan nan tabani in kawo miki, tace tana gaishe ki tare da Abba ma”.

Saleema kamar zatayi kuka tace “Allah Sarki ina amsawa nayi kewar su sosai”.

Dariya Halwa tayi tamiƙe tana faɗin “ko dai zakiyi kuka ne?”

Hararan ta tayi itama tatashi tana cewa “Sister ko ruwa baki sha ba fa? Bari in ɗauko miki”.

Taƙarike maganar tana nufan wajen Fridge batare da tajira cewar Halwan ba, ɗauko ruwan tayi tadawo tana cewa

“Sai yaushe kuma sister?”

Wulla idanuwan ta tayi alamun tunani tace “uhmm sai dai idan nagama Exams ɗin nan sai in zo inyi miki wuni ko?”

Turo baki Saleema tayi kamar zatayi kuka tace “kai sister kenan har sai na jira kin gama Exams zaki sake zuwa?”

Murmusawa Halwa tayi tace “ke dai karki damu zuwa gidan ki ai sai kin gaji da ganina, yaushe ma akayi auren ne? Ki kwantar da hankalin ki”.

Dariya Saleema tayi tace “to shikenan muje in raka ki”.

Har wajen mota Saleema taraka ta, anan suka gaisa da Drever, Halwan tashiga mota yaja suka bar gidan

Sai ɗaga musu hannu take yi har Me gadi yarufe Gate ɗin kafin tasauke hannun ta tajuya cikin gidan cike da kewar ƴar uwan nata

Tana shiga parlour’n ta’iske Husna ta farka sai wutsil-wutsil take yi tana son sauko wa, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tana dariya cike da ƙaunar ta tasoma yin mata rawa tana mata wasa

“Iyeee Mamana kin tashi? Yau kin dawo wajena ko? Oh i miss You so much”.

Tamanna mata peck a baki, ita kuma sai faman ɓangale mata bakin take yi tana yarfe hannayen ta tare da tsalle jikin ta

Dariya Saleema tayi tana sake riƙe ta dakyau ganin yanda take ta zillewa wai adole tana wasa

“My dear ki dena karki suɓuce min kinsan girma ne dake”.

Ita kuma kamar tana jinta taci gaba da zillewa tana tsallen murna sai ɓangale baki take yi, Allah ya zuba mata wayau gata kuma bata da ƙyuya ko kaɗan, duk wanda yaɗauke ta haka zatai ta ɓangale masa baki kamar tasan shi

Tana nan zaune tana ta jijjiga yarinyan tana mata wasa kamar ta sami sa’ar ta sai faman yin mata hira take yi da surutu

Khalil yaturo ƙofan yashigo da sallama a bakin sa

Ɗago kai tayi tana kallon sa kamar yanda shima ɗin yaƙure su da nashi idanun me tsananin kyawu da kaifi

Gaban Saleema ne yafaɗi, sai Lokacin tatuna bata sanar masa da maganar dawowar Husnan ba, daƙyar takawar da fargaban nata tana amsa mishi sallaman

Takowa yayi yashigo ciki still idanun sa na kansu, yarinyan kawai yake kallo cike da sha’awa, shi me son yara ne sosai suna matuƙar burge sa

Matsowa kusa da ita yayi yana faɗin “wannan yarinyan wacece?”

Yaƙarike maganar yana duƙowa gaban ta ya’amshi yarinyan yana sake ƙure ta da idanu, sosai yarinyan tayi masa kama da wacce yasani, lokaci ɗaya kuma yaji ta shiga ran sa har be san sanda yasakar mata kyakkyawar murmushin sa yana wasa da hannun ta ba, itama ɗin sai ɓangale masa baki take yi kamar yanda tasaba tana kallon sa

Mai da idanun sa kan Saleema da taduƙar da kanta ƙasa yayi

Har alokacin bata iya basa amsar tambayan da yayi mata ba

cikin murmushin sa yace “Ya sunan ta?”

Cike da sanyin murya tace “Husna”.

Kallon yarinyan yasake yi sai kuma yamiƙe tsaye yana zama kan kujera ya’ajiye ta a cinyan sa yaci gaba da mata wasa

Ita dai Saleema na zaune tana jin su tare da satan kallon su, sosai taji daɗin yanda yanuna son yarinyan duk da kuwa be san ita wacece ba

“Ina Maman ta ne?” Yajeho mata tambayar yana kallon ta

Cike da fargaba Saleema tace “tana gida”.

Ɗan waro idanun sa yayi cike da mamaki yace “kenan kawo miki ita akayi?”

“Eh zata zauna a wajena ne”.

Kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan mamaki, be kai ga magana ba yahangi ɗan kyakykyawar Trolly ɗin dake ajiye gefe

“Kayi haƙuri don Allah nasa an kawo min ita ban tambaye ka ba, wlh na manta ne”. Tayi maganar cikin ladabi da sanyin murya

Still kallon ta yasake yi sai kuma yamaida idanun sa kan yarinyan

Shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma yace “yanzu har kin warke da zaki iya raino?”

Murmusawa tayi bata iya cewa komi ba sai ɗauke ganin ta da tayi daga kansa

Ajiyan zuciya kawai yasauke be sake cewa komi ba kuma be bata yarinyan ba, aransa kuma tunani yake yi yanda ita Saleeman take son yara har da zata ɗauko yaran mutane da sunan riƙe wa, sai kuma tsananin mamakin uwar yarinyan da ta’iya rabuwa da ƙaramar yarinya kamar wannan, yana son yayi mata tambayan ya zatayi idan zata shayar da ita amma kunya ya hana sa tambayan ta, baya ga haka akwai tarin tambayoyi da yake son yin mata

Saleema ganin shirun dai yayi yawa sai tamiƙe taja Trolly ɗin tanufi ɗakin ta.

.

***** ***** ******* ****

 *BAYAN SATI BIYU*

       A cikin wannan kwanakin shaƙuwa ne sosai yashiga tsakanin Khalil da Saleema, sun yi kwanakin ne cikin nuna kulawan junan su tare da girmama juna

Duk wani kulawa Khalil yana nuna mata tare da tausayin ta me tsanani da yake yi cikin ransa, baza ka taɓa tunanin su ɗin ba masoya bane domin yanda suke gudanar da zamantakewar su ko masoyan asali albarka

A yanzu soyayyar Khalil sosai yaginu a zuciyar Saleema, tasan da cewa tayi dace ga miji na gari don Khalil ɗan halak ne kuma ya haifu

Shi kuma har alokacin ya kasa jin soyayyar ta cikin ransa, sai dai yasan yayi dace da mata na gari kuma yana ji aransa zai iya zama da ita har ƙarshen rayuwan sa batare da yayi dana sani ba

Zan iya cewa tare suke rainon Husna sabida yanda Khalil ke nuna kulawan sa agare ta, idan har yana gida ko baya aikin komi yarinyan ko yaushe tana hannun sa, sosai yarinyan tashiga cikin ransa.

Jikin Saleema alhmadulillah yanzu ta warke sumul babu abinda ke damunta, tattalin mijinta kawai tasaka agaba sai kuma rainon Husna.

       *******

Yau ce ranan da Halwa tace zata zo don haka da sassafe Saleema tatashi cikin ɗoki tasoma aiyukan ta, babu laifi yanzu ta saba da duk wani hidiman gidan duk da ba wani aiki me yawa take yi ba

Shi kansa Khalil yasan da zuwan Maman Husna don tun jiya da sukai ta waya da Halwa yaga tana ɗoki yatambaye ta take faɗa masa Mamar Husna ce zatazo

Shirin Office yayi cikin Ash colour ɗin Suit da yayi masa kyau matuƙa yawuce wajen aiki bayan yayi musu solfie su ukun cike da nishaɗi.

Har tagama abinci da duk abinda yakamata kafin Halwa ta’iso.

_Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen BOOK ONE sai ku tara a BOOK TWO don jin me zai faru._

.

_ya zaman Khalil da Saleema sai kaya, kuna ganin tausayin da yake mata zai iya juye wa yazama ƙauna?_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button