BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

_Shin kuna ganin Halwa zata cika burin ta?_
_me zai faru idan ta mayar da Husna ga Mahaifin ta?_
_ya Maganar Haris da be san yana da ƴa ba?_
_kuna ganin Zainab zata amince da soyayyar Nura?_
_Ya maganar Nazeefa da takamu da soyayyan wanda be san ma tana yi ba?_
_kuna ganin idan har Mom tagane zata aura mata shi kamar yanda tayi alƙawarin gano meke damunta kuma tashare mata hawaye?_
_Shin kuna ganin Halwa zata koma ga Iyayen ta?_
_Shin ya za su karɓe ta?_
_duk a Two ne zaku samu amsar tambayan ku da dalilin da Nura yajuya wa Halwa baya?._
_sai ku biyo NI don ji amsoshin ku_
_Nafisat Jikar Lawal ce_✍️
Ba_byeee ????????????????????????????????????????????♀️????????♀️????????♀️
[11/9/2020, 9:13 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*???? _WhatsApp Number 07065334256_
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
““Allah ya dawo dani mu tsunduma cikin labarin
Na gode masoyana.“`
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER One*
________????Suna zaune su Biyu akan dainning table suna cin abinci
Halwa kai abincin bakin ta tayi tana lumshe idanun ta cike da jindaɗi, sai kuma tabuɗe idanun taɗaura akan Saleema da itama tamayar da hankali wajen cin abincin ta, murmushi me sauti Halwa tasaki still tana kallon ta tace
“Sister gaskiya abincin nan kamar zai tsinke min kunnuwa, kina gani fa har rawa suke yi sabida tsaban daɗin abincin nan”.
Dariya Saleema tasaki tana kallon Halwa da taƙara ɗibo wani abincin takai bakin ta tana faman lumshe idanu
“Bari dai in tashi in ɗauko pilow in tare ki dashi, idan ba haka ba babu me iya tare ki nan gaba in kikaci gaba da wannan santin”.
“Allah Sister ba santi bane, kinji yanda abincin yake da matuƙar daɗi ne sai kace wacce tadaɗe da ƙwarewa, wlh ko Ni bazan iya rin wannan ba”.
Murmushi Saleema tayi cike da jindaɗi sai dai bata iya cewa komi ba
“Ƙara min miyan”. Halwa tace hakan tana miƙo mata plate ɗin shinkafan
Zuba mata miyan tayi tana faɗin “Kinsan jiya da Zazzaɓi Husna ta kwana, wlh duk na ruɗe sabida yanda naga tana yi, da ba don Yaya Barrister ba bansan yanda zan yi ba, shi yatashi yayi ta rarrashin ta har yana cewa in koma in kwanta”. Taƙarishe maganar nata tana wani irin murmushi me ma’anoni da yawa wanda Ni kaina bangane mata ba
Shiru Halwa tayi bata ce komi ba illa kai abinci bakin ta da take yi
Ɗago kanta Saleema tayi takalli Halwan sai kuma tamayar da kanta kan abincin tana sake yin murmushi
Tasan da cewa baza ta taɓa tankawa ba, halin ko in kula shi Halwa ke nuna wa Husna, tunda tahaife ta ko ɗaukan ta idan ba ya zama dole bane to ko kallo bata ishe ta ba, baza ka taɓa tunanin itace uwarta ba
Basu sake magana ba har sanda suka gama cin abincin suka koma parlour, Hira suka ɓarke dashi cike da nishaɗi, sai da aka kira sallah kafin Saleema tashige ɗaki don yin Sallah, ita kuma Halwa tadasa Kallo kasancewar bata sallah
Khalil ne yaturo ƙofan da sallama a bakin sa hakan yasa Halwa ɗago idanuwan ta tasauke acikin nashi idanun wanda yayi dai-dai da yankewar gaban su a lokaci ɗaya
Kallon kallo suke ma juna cike da wani irin yanayi me wuyan fassara
Khalil sandarewa yayi a tsaye a wajen kakkaifan idanun sa akanta, ganin abun yake yi tamkar a mafarki yau yarinyan da tahana zuciyarsa sukuni tsawon lokaci itace agaban sa a kuma cikin gidan sa, kullum cikin tunanin ta a barci kuma mafarkin ta
Janye idanunta Halwa tayi daga kallon sa, ko kaɗan kuma bata gane sa ba sai dai idanun sa sun mata kama da wanda tataɓa gani
Be jirga daga wajen da yake ba illa zuba mata idanuwa kawai yayi kuma ya kasa ɗauke wa
Fitowar Saleema daga ɗakin ta tahange sa tsaye ya kafe Halwa da kanta ke ƙasa da kallo, irin kallon da yake mata shi yasaka gabanta yayanke yafaɗi, take taji wani abu ya soke ta a ƙahon zuciya da yasaka tayi saurin ɗaura hannunta a ƙirjin ta tana runtse idanu
Halwa da har yanzu take jin idanuwan sa masu tsananin kaifi suna yawo ajikin ta, dai-dai tana ɗago kanta tahangi Saleema tsaye dafe da ƙirji, dasauri tamiƙe tana faɗin “Sis lafiya kuwa?”
Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon ta sai kuma tamaida ga Khalil da maganar Halwan shima yadawo dashi hayyacin sa, haɗa idanuwan da sukayi yasaka shi sakar mata kyakkyawar murmushin sa yana takowa cikin parlour’n
Wannan murmushin da yayi mata shi yasaka taji sanyi aranta, takalli Halwa dake nufo ta a yanzu ɗin taƙirƙiro murmushi tace
“Babu komi”.
“Anya kuwa? Ko dai wani abun ke damun ki?” Halwa tasake tambayar ta cikin damuwa don bata yarda babu komi ɗin ba
Still Saleema tana murmushi tariƙo hannun Halwan suka nufi kan kujera tana faɗin
“Yaya sannu da zuwa”.
Idanun sa akan su ya’amsa mata cike da kulawa
Zuciyar Halwa har alokacin bugawa yake yi kuma ta rasa dalili, har a time ɗin kuma bata iya ɗago kai ta sake kallon sa ba, zama kawai tayi tana sake mayar da idanun ta kan t.v
Cike da son kawar da abinda ke cikin zuciyarsa yayi hanyan ɗakin sa cikin takunsa me burgewa da cikan mazan taka
“Yaya baku gaisa da Maman Husna ba”. Saleema tafaɗi hakan tana kallon bayan sa
Cakk yatsaya zuciyar sa na wani irin bugawa dasauri-dasauri
“Ina yini”. Cewar Halwa itama da taɗago kanta tana kallon bayan nasa
Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana sake danne abun da yake ji, cikin wani irin murya da dole kagane akwai wata matsala ya’amsa mata da “lafiya”. Sannan yawuce ciki da sassarfa
Basu kawo komi akai ba illa mayar da hankalin su ga juna da sukayi
Cikin murmushi Halwa tace “baza ki bi bayan sa bane?”
Hararan wasa Saleema tasakar mata tana murmushi da son kawar da abinda take ji cikin zuciyarta, domin kallon da Khalil yayi wa Halwa sosai yatsaya mata arai har tana son dasa zargi cikin zuciyarta, bata iya cewa komi ba sai murmushin da take faman yi
Matsowa Halwa tayi taraɗa mata magana a kunne, dariya suka fashe dashi suna tafawa.
____________________
Cike da sanyin jiki yaƙarisa kan gadon sa yazube yana ɗaura kansa akan pilow, sosai zuciyarsa yake faman bugawa kamar zai faso ƙirjin sa ba don komi ba sai maganar da Saleema tafaɗa masa Halwa itace Mamar Husna, numfashi yasoma fesarwa yana son dai-dai ta nutsuwar sa dake son gushe wa, hannun sa yaɗaura akansa yariƙe yana lumshe idanuwan sa sabida jin yana faman sara masa, baya son ko kaɗan zargin sa yazama gaskiya
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..”
Abinda yake ta faman maimaita wa kenan har yasoma jin nutsuwarsa na dawo masa tare da sassaucin bugun zuciyar sa
Dantsen hannun sa yaɗaura akan kyakykyawar face ɗin sa yayi shiru kamar ruwa ya cinye sa
Har Saleema tashigo be motsa ba
Maganar abinci tayi masa amma sai yagirgiza mata kai alaman bazai ci ba
Shiru tayi kamar zata yi masa magana sai kuma takasa tajuya tafita