Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Parlour takoma sukaci gaba da hiran su da Halwa, har sanda tajiyo kukan Husna dake barci a ɗakin ta, zuwa tayi taɗauko ta tadawo parlour’n tahaɗa mata abincin ta tasoma bata

Khalil har akayi sallan la’asar be tashi daga inda yake shingiɗe ba, abun duniya duk yayi masa yawa, sai daga baya daƙyar yamiƙe yasoma cire kayan jikin sa, zuwa yanzu kuma kansa sosai yake mishi ciwo kamar zai fashe

Toilet yashiga yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya yazura yafito parlour’n fuskarsa duk babu walwala, kallo ɗaya yayi musu yaɗauke kansa saboda haɗa idanun da sukayi da Halwa

Itama dai sauke kanta ƙasa tayi tana me mamakin kanta da wannan mutumin, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda haɗa idanun da sukayi yahaddasa mata hakan

Miƙewa Saleeema tayi da Husna a hannun ta tace “bari inyi sallah sister”.

“Ok muje nima in shirya tafiya zanyi”. Halwan tafaɗa tana tashi tsaye

Hararan ta Saleema tayi tace “tun yanzu? Ai ba haka mukayi dake ba”.

Dariya kawai Halwa tayi tazo tawuce ta tayi gaba

Itama tabi bayan ta tana ƙorafi

Suna shiga ɗakin Saleema tashimfiɗe Husna da takoma barcin ta, ita tasoma shiga Toilet ɗin taɗauro alwala kafin tafito Halwa tashiga

Bata jima ba tafito tazauna akan drowan Gadon taɗau wayan ta tana neman layin Drever, sai dai wayan tasa akashe ne, tsaki taja tamiƙe tanufi kan stool dake gaban mirror tazauna tasoma shafa Powder tana gyara fuskarta

Tana nan zaune har Saleema ta’idar da sallan ta tajuyo tana kallon ta tace

“Wai don Allah dagaske yanzu zaki tafi? Please ki bari sai dare mana”.

Murmushi Halwa tayi tana kallonta ta cikin mirror tace “kina son gobe in ƙi zuwa miki kenan?”

Girgiza kanta Saleema tayi itama idanun ta akanta, sai kuma tace “amma dagaske zaki zo ɗin gobe?”

Cike da son riƙe dariyan ta dake son kufce wa tace “sosai ma sister gobe zan dawo shiyasa zan tafi yau da wuri”.

Gyaɗa kanta tayi sannan tamiƙe tana cire Hijabin ta tace “to shikenan na yarda ki tafi amma goben ki zo da wuri”.

Halwa bata iya bata amsa ba saboda dariya da yacika cikin ta sosai ƙiris yarage tasaki dariyan, ɗaga mata kai tayi tana sauke kanta ƙasa tasoma dariyan ta yanda baza ta ganta ba

Saleema kuwa kan gado tanufa batare da ta kula da ita ba, sai zayyano mata saƙon gaisuwa da zata kai ma su Ummi da Abba take yi

Ɗago da kanta Halwa tayi tajuyo gaba ɗaya tana kallon Saleema cike da murmushin da yabayyana haƙoran ta tace “amma fa na kira drever wayan sa be shiga ba kuma gashi ban fito da kuɗi ba”.

Saleema tace “to nima ai bani da kuɗi gaskiya, amma bari in duba ko Yaya Barrister ya dawo sai ince yayi ma Drever magana yakai ki”.

Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi

Ita kuma tatashi tafita tashiga ɗakin Khalil

Yana tsaye ne agaban mirror ya sauya kayan jikin sa zuwa ƙananan kaya, yana fece suman sa da Cumb tashigo

Takowa tayi tazo inda yake tana kallon sa cike da ƙauna, sosai yayi mata mugun kyau har ta manta abinda yashigo da ita ta shagala wajen kallon sa

Ajiye cumb ɗin yayi yajuyo yana kallon ta, tayi saurin duƙar da kanta cike da kunyan kamata da yayi tana kallon sa

Be ce komi ba yamatsa gaban gadon sa yaɗau Wrest watch ɗin sa yana ɗaurawa a tsintsiyan hannun sa

“Uhm dama Halwa ce zata tafi gida shine nace ko zakayi ma drever magana yakai ta?”. Tayi maganar a hankali tana kallon sa

Tsayar da abinda yake yi yayi yana juyowa yakalle ta, ganin sun haɗa idanu sai yagyaɗa mata kansa tare da ci gaba da ɗaure Wrest watch ɗin

Murmushi tayi tajuya zata fice, har ta kai bakin ƙofa tajiyo muryan sa

“Tafito sai in sauke ta”.

Kallon sa tayi shi kuma yaɗauke kai yana takawa yanufi wajen takalman sa

Cikin sanyin murya ta’amsa mishi sannan tafice.

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button