BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 38*
Brr. Tahir yace “abin ne da mamaki mace nake gani agidan ka? Taya hakan zai faru? Meye alaƙan ka da ita?”
Gajeran tsaki Khalil yasaki yana kawar da kansa, domin shi a tunanin sa ko wani abun yagani don har ya tsorata shi
“Kayi min bayani mana meye alaƙan ka da ita? Kar dai ace..”
Wani kallo da Khalil yasakar masa ne yakasa ƙarisa abinda yayi ninya, sai yatsaya kawai yana kallon sa batare da ya ɗauke idanun sa akan sa ba, Khalil kuma juyar da kai yayi yaci gaba da abinda yake yi kana yace
“Ba abinda kake tunani bane, maƙociya ta ce”.
“Maƙociyar ka?”
Brr. Tahir yamaimaita maganar kamar be fahimta ba, sai kuma yasaki murmushin gefen baki yana cewa
“Kayi min bayani yanda zan gane har yanzu ban fahimce ka ba?”
Tsaki Khalil yaja yana hararan sa, nan dai yabashi labari yanda suka haɗu da alaƙan sa da ita
dariya Brr. Tahir yakece dashi yana cewa “Cab ɗi.. wai dama ka iya sakewa da mata har haka?”
Kallon banza Khalil yayi masa yace “me kaɗauke ni to?”
Ɗage hannu Brr. Tahir yayi yace “No babu”.
“Kafaɗa karta kashe ka, ai nasan duk abinda kake tunani”.
Shi dai Brr. Tahir dariya kawai yake yi, sai da yagama dariyan sa son ransa Khalil be sake kula sa ba, sannan daga baya yace
“Kasan me? na samo maka shawara, me zai hana kawai kakai ma Dad ita a matsayin wacce kake so tunda naga taku tazo ɗaya”.
Idanun Khalil kamar zai faɗo ƙasa sabida kallon da yake yi masa, Brr. Tahir da yabuɗe baki zai ci gaba da magana Khalil yayi saurin katse sa da cewa
“Banso don Allah kadena wannan maganar, ce maka akayi ina son ta? ko ce maka akayi ita tana so na? Babu wani abu da zai haɗa mace da namiji ne sai soyayya? Ni kawai burge Ni take yi ba wani abu ba”.
“To ai hakan shi ke kawo ƙauna, don me zata burge ka idan har babu ƙauna aciki?”
Ɗaure fuska Khalil yayi yakawar da kai don bazai iya biye masa ba, kuma yasan halin Brr. Tahir idan yakama abu to baya jin bari
“Uhm Ni kawai shawara nake baka, idan kuma kafison wacce Dad zai baka ai shikenan , ta yiwu ma kaje kaganta batayi maka ba”.
Shiru dai Khalil yayi be ce komi ba, amma tunanin maganar Brr. Tahir ɗin yake yi da yayi a ƙarshe
Brr. Tahir yakatse masa tunanin sa da cewa “katashi kashirya mana mutafi, in kuma ka fasa ne sai nayi tafiyana don ina da abin yi”.
Miƙe wa Khalil yayi still be ce masa komi ba yanufi ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin wani farin Gezna da yayi masa kyau ainun, yasaka baƙar hula me ƙube tare da baƙin Sandal shoes, babu abinda ke tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi, car key yaɗauka tare da wayoyin sa yafito parlour, Brr. Tahir kallon sa kawai yake yi ganin yanda yayi masa mugun kyau
“Kai Abokina kaga yanda kayi kyau? Ni namiji kenan ina ga mace ta ganka? wannan wanka gaskiya Amarya dole tabiya mu”.
Tsaki Khalil kawai yaja yanufi ƙofa batare da ya tanka sa ba, shi kuwa Brr. Tahir biyo sa yayi yana ta tsokanar sa yana faman dariya
A cikin motan Khalil ɗin suka fita, mintuna ashirin yakaisu gidan Alh. Mustapha, suna yin hon aka buɗe musu Gate don dama gateman ɗin yasan da zuwan su, lokacin da sukayi parcking duk kan su suka fito alokaci ɗaya, Brr. Tahir sai gyara wuyan rigan sa yake yi yana faman doka murmushi sai kace shine aka rako, Khalil kuwa in banda harara da yake aika masa babu abinda yake yi, ahaka akayi musu iso har zuwa Parlour’n Alh. Mustapha inda anan ne aka sauke su, me aiki aka saka takawo musu abin motsa baki, babu abinda suka taɓa sai hira da Brr. Tahir yake jan Khalil dashi, shi kuwa sai latsa wayan sa yake yi ko kula sa be yi ba
A ciki kuwa Saleema ce taci uban kwalliya cikin wani tsadadden less me ruwan toka, ɗinkin riga da sket ne da yayi mata kyau matuƙa, tayi ma fuskarta Light makeup Wanda yaƙara fito da tsantsan kyau ɗin ta, dama Saleema ba baya ba wajen kyawu, Halwa na zaune tana kallon ta har tagama shiryawa tayafa gyale fari ƙal me kwalliyan stone, haka ma flat shoes ɗin da tasaka a ƙafafun ta fari ne, murmushi kawai Halwa take zubawa kafin tace
“Gaskiya kinyi kyau My sister, anya baza ki zautar da Angon nan naki ba yakasa manta ki?”
Washe baki kawai Saleema take yi cike da farin ciki, kana tace “dagaske nayi kyau Sis?”
Halwa tace “wlh sosai kinyi kyau Sister, kuma ina da yaƙini dole ki shiga ran sa alokaci guda, don babu wanda zai ganki be yi fatan ki zamo matar sa ba”.
Dariya Saleema tayi tace “Thank you My Sister, bari inje kar suji Ni shiru tunda nace kizo muje kinƙi”.
Girgiza kanta Halwa tayi tana murmushi tace “O’o Ni bazan iya zuwa ba, ke dai kawai kije ke kaɗai, idan yasake dawowa watarana sai mu gaisa”.
“To na tafi, sai na dawo Sis”.
Daga nan fita tayi ita kuma Halwa kwanciya tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da tunani a ranta, Saleema tana shiga Parlour’n da sallama Brr. Tahir da yatsare ƙofan da idanu ya’amsa mata yana sakin murmushi, a ransa kawai “masha Allah yake faɗa”. Don ba ƙarya Abokin nasa ya dace da zaɓi, Saleema kanta a ƙasa ta’iso tazauna kan sofa me facing nasu, sai tagaishe su alokaci ɗaya tana ɗago kai tana kallon su, dai-dai da shima Khalil ya ɗago kai yasauke idanu kanta suka haɗa idanu, sauke kanta ƙasa tayi cike da tsananin kunya tare da zallan farin ciki, shi kuwa taɓe baki kawai yake yi amma yakasa ɗauke idanun sa akanta, Brr. Tahir kuwa cikin murmushi ya’amsa mata tare da tambayan ta “ya take da ƴan gidan?” Amsa mishi tayi, sai Brr. Tahir ɗin yakalli Khalil dake faman ƙare mata kallo, hakan yabashi dariya yayi saurin ƙumshe bakin sa yana cewa
“To Abokina ga fa Amarya ta iso, Ni bari in fice in baku space don kutattauna ko?”
Sai lokacin Khalil yaɗauke kansa yamayar ga Brr. Tahir, be ce masa komi ba hakan yasaka Brr. Tahir yatashi yafice
Shiru ne yabiyo bayan fitan Brr. Tahir, ita Saleema tunani kawai take yi yanda Khalil ɗin yasauya mata sosai fiye da yanda tasan shi, wani irin kyau da kwarjini yasake yi tare da wani irin gogewa yasake ƙiba, kai da gani kasan hutu da kwanciyan hankali tare da kuɗi sun zauna masa, so take yi tasake ɗago kai takalle sa amma ta kasa domin yanda take jin idanun sa masu matuƙar kaifi suna yawo ajikin ta, shi kuwa a nashi fannin zuba mata idanuwa yayi yana ta kallon ta, a haƙiƙanin gaskiya dogon tunani yafaɗa har be san iya adadin mintocin da suka wuce ba, Saleema dai har ta gaji taɗago kanta tana kallon kyakykyawar fuskar sa da yatsare ta da kallo, cikin sanyin murya tace
“Ko in Kira Abokin ka ku fara cin abincin ne?”
Sai alokacin yaɗan ƙifta idanun sa da alamun yadawo tunanin sa, kallon ta yayi yana ɗan jije leɓe, ba ƙarya ayanda yafahimta yarinyan zatayi sauƙin kai, duk da ba wai tayi masa yanda yake so bane kuma ba wai yaji ta a ransa bane, but ta kwanta masa arai kuma zai iya zama da ita a matsayin matar sa, ajiyan zuciya yasauke kafin yace
“Kina lafiya?”
Saleema da har tagaji da shirun nasa tasad da kai ƙasa tana wasa da yatsun ta, jin sassanyan muryan sa me daɗi yasaka ta ɗago kai tana kallon sa kana ta’amsa mishi cikin biyayya da son burge shi