BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

“Nasan kinsan me yakawo ni nan ɗin don nasan an riga da an miki bayani? Any way ni sunana Brr. Ibrahim Khalil Abdurra’uf, ina fata..”
Shiru yayi don be san me zai faɗa ba, ita kuwa kallon sa kawai take yi tana jin yanda muryan sa me tsananin daɗi yake shiga kunnuwan ta, kamar an matse bakin sa sai yace mata
“Me kike karanta a School?”
Cike da farin ciki ta’amsa masa da “Pharmacy”.
Gyaɗa kansa yayi sai kuma sai kuma yayi shiru yana ajiyan zuciya, wayan sa yaɗauka kana yaɗago kai yana kallon ta yace “kiyi haƙuri ni ba gwanin iya soyayya bane Thats why ban iya hiran ba”.
Murmusawa tayi kawai tana sunkuyar da kai, sosai yaburge ta hakan na nufin kenan be taɓa budurwa ba kamar yanda itama bata taɓa yi ba? Duk kallon da take masa bata taɓa tunanin yana da sauƙin kai irin haka ba
Brr. Tahir yakira yace masa “yashigo”. Babu jimawa kuwa yashigo yana kallon su yana murmushi yace
“Har an gama hiran?”
Khalil be basa amsa ba sai miƙewa da yayi yana saka wayan sa a aljihu hakan yasa Brr. Tahir cewa
“To Amarya mu zamu tafi, sai kuma gani na gaba”.
“To bakuci komi ba”.
“No karki damu next time idan muka zo zamuci yanzu muna sauri ne”.
Gyaɗa kanta tayi tana tashi tsaye, daga nan raka su tayi har wajen motan su kafin suka sake sallama tataho gida.
.
_More Comments More post._????????♀️????????♀️????????♀️
[11/1/2020, 9:23 AM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 39*
*AFTER SEVEN MONTH*
A wannan watannin da suka shuɗe abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da haihuwar da Halwa tayi, ta haifi yarinyan ta kyakykyawa me ban sha’awa, sosai yarinyan take kama da ita, sai dai kuma ta ɗakko abubuwa da dama na mahaifin ta wanda idan kakalle ta tabbas zakasan ƴar sa ce, sunan Ummi aka saka mata kamar yanda Saleema tabuƙaci asaka, wato Asma’u suna kiran ta da Husna, duk wani hidima kama daga kan kayan Baby zuwa na uwar Babyn babu abinda Abba be siya musu ba, komi ya wadata su dashi tamkar tana gaban iyayen ta, tun sanda tahaihu kuma Ummi tace “baza ta shayar da yarinyan ba”. Don haka da madaran kanti ake shayar da ita, Halwa sosai taji daɗin hakan ko ba komi an ɗauke mata wani nauyi kuma an taimake ta, duk wani hidiman yarinyan Saleema ce me yi, kullum yarinyan tana hannun ta ita take kula da ita, ita take mata komi sai dai wanka da Larai ƴar aikin su take mata, ita kuwa Halwa sai dai taci tasha takwanta hakan yasaka gaba ɗaya tasauya tasake ƙiba tayi kyau gunun sha’awa, dama gashi tana tsaka da jego ne kuma ga hutu da yayi mata yawa
Yanzun ma zaune take agaban madubi tana shafa lipstick a ƙananun laɓɓan ta, fuskarta babu wani kwalliya illa powder da tashafa sannan tazizara kwalli cikin idanuwanta, miƙe wa tayi tana gyara zaman rigan ta, doguwar riga ce na atamfa tasaka Milk and Coffee colour, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau duk da kasancewar ta bata da hasken skin, Halwa irin Chocolate Colour ɗin nan ce me ɗan haske, tana da kyau na ban sha’awa da burgewa, idan har zaka ganta to dole sai ka sake kallon ta coz yanayin ta da komi nata yana da kyan kallo, bata da wani tsayi amma tana da ɗan kauri kaɗan tare da sura me kyau da ɗaukan hankalin me kallon ta, duk da kuwa ita ɗin ba ma’abociyar son cin abinci bane, kallo ɗaya idan kayi mata zaka fassara ta da me sanyi don ko a maganarta ne cikin sanyi sosai zakaji muryan ta, sai dai kuma akwai ta da tsiwa sannan tana da surutu matuƙa sai dai idan bata sami wajen yi ba
Tana cikin ɗaura ɗankwali Saleema tashigo ɗakin, itama ɗin doguwar riga tasaka iri ɗaya da na Halwa har ɗinkin da komi, Ummi taba da aka ɗinka musu wajen kala bakwai lokacin da Halwan tahaihu, itama ɗin sosai yayi mata kyau kasancewar ta fara ce, murmushi tasakar wa Halwa kana tace
“Kinyi kyau Sister”.
Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace “Thanks”.
“Ok Ina kayan Husna? Larai ta gama mata wankan za’a shirya ta”.
“Ban ciro mata ba”. Halwa tabata amsa tana saka Room Slippers a ƙafafuwan ta da suka sha lalli ja da baƙi
Saleema wajen kayan Husna tanufa tana cewa “but sai da nace miki ki ciro kafin in dawo fa”
Ƙarisawa kusa da ita Halwa tayi tana taya ta cirowa tace “I’m sorry Sis, ban gama shiryawa bane shiyasa”.
“Ok”.
Fita sukayi gaba ɗayan su bayan sun gama ɗaukan abinda zasu ɗauka, suna fita parlour Halwa zama tayi akan sofa ita kuma Saleema tawuce da kayan ɗakin Larai, can kuma sai gata tafito ɗauke da Husnan a hannu, an shirya ta tsaf-tsaf cikin kayan ta masu kyau, zuwa tayi tazauna gefen Halwa tana cewa
“Kinga Babyna yau tayi kyau sosai, har carbing mukayi mata”.
Halwa kallon yarinyan tayi sai kuma taɗauke kai tana yamutsa fuska kamar yanda tasaba
Kallonta Saleema tayi tace “Yauwa Sis idan nayi aure kema zaki dawo gidana ko? Sai mu zauna tare”.
Murmushi Halwa tayi tace “to sai mu bar Ummi da wane? Kinga ke kin tafi dole zasuyi kewarki”.
Gyaɗa kai Saleema tayi kana kuma tace “but duk da haka dai zaki riƙa zuwa kina min sati ko fiye da hakan, kinga kuma Ni ban ma iya girki ba idan naje wanene zai min?”.
Halwa tace “zaki sami House girl ne sai tayi miki”.
Kwaɓe fuska Saleema tayi tace “no bana son ƴar aiki sai dai muje muriƙa yi tare dake”.
“To ai nima ban iyaba wlh”. Halwa tafaɗa tana dariya
Dariya itama Saleema tayi tace “haba dai? Kice duk jirgi ɗaya taɗauko mu?”
“Eh mana, ko Mama tasaka Ni bana yi har ma ta saba ta dena cewa inyi, sabida Ni dai gani nake yi tunda bana cin abincin to bazan koya ba”.
Still dariya Saleema tayi tace “tabb ai kuwa dole mu saka Larai gaba takoya mana”.
Ummi ce tayi sallama tashigo
“Oyoyo Ummi”. Cewar Saleema tana miƙe wa ta’isa wajen ta
Ummi kuma amsan Husna tayi tana dariya tace “iyeee ga takwarata ga takwara ta”.
Sannu da zuwa sukayi mata sannan tazauna tana cewa “Abban ku be dawo ba?”
Saleema tace “ya dawo ya fita ne”.
“Ok”.
Yarinyan tamiƙa wa Saleema sannan taɗau jakan ta, ita kuma Halwa lokacin tadawo ɗauko ma Ummi ruwa tace
“Ummi ga ruwa kisha”.
Murmushi Ummi tayi tace “Yauwa na gode”.
Har ta juya Ummi tasake cewa “zo riƙe wannan ledan”.
Halwa amsan ledan tayi tana kallo
“Magani ne idan Larai zatayi miki wanka sai ki riƙa Using dashi”.
Gyaɗa kai Halwa tayi tana komawa tazauna, ita kuma Ummi miƙe wa tayi tanufi ɗakin ta, sai da tashige sannan Saleema tace
“Menene acikin ledan?”
Kallon ta tayi taɗage kafaɗa alamun bata sani ba, sai kuma tace “ki tambayi Ummi”.
Ɗan waro idanu Saleema tayi sai kuma tasaki dariya tace “ai bazan iya bane wlh”.
Harara Halwa tayi mata tace “ashe kin sani kenan kike tambaya?”
.
**** ***** ***** ******