BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Wani irin kallo take masa har sanda yadasa aya a maganar sa sannan tabuɗi baƙi cike da baƙin ciki tace
“Wlh Nura kabani mamaki domin ban taɓa tunanin haka halinka yake ba, har Ni zaka dubi idanuwana kace kana so na? Idan har baka bar mana ƙofar gida ba wlh zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba..’
Bata rufe baki ba Nura yace “haba Zainab wai meye laifina anan? me namiki da baza ki so ni ba? Kar ki manta fa wacce kike tunani akanta bata nan don me baza ki bani dama in maye gurbin ta dake ba, wlh ina ƙaunar ki tsakani da Allah..”
Cikin wani irin tsawa Zainab takatse shi
“Dalla kayi mana shiru, duk wani mutunci da nake gani naka wlh ka ɓarar dashi, bari kaji wlh koda maza sun ƙare a duniya Nura bazan taɓa son ka ba bazan taɓa auren ka ba, har yanzu kallon ka nake yi a matsayin saurayin ƙawata kuma Ni bana cikin maciya amana, and nasan da cewa Halwa baza ta taɓa barin ka ba coz nasan irin ƙaunar da take maka, duk inda take a faɗin duniya tana nan tare da kai aranta, idan ma har wani abu kuka ƙulla domin tabar gidan nan to wlh kun ci amanarta”.
Wani irin kallo tabuga masa kafin taci gaba da cewa “kasani duk inda Halwa tatafi zata dawo wannan alƙawari ne, anan ne zan tabbatar maka da cewa ita ɗin me ƙaunar ka tsakani da Allah ne ba irin ka ba”.
Daga haka tajuya tashige gida batare da tabari yasake furta komi ba, shiru Nura yayi yana kallon hanyan da tabi, ya jima anan tsaye kafin yabuɗe kyakykyawar motar sa yashiga yabar wajen, gidan da yasiya wa iyayen sa yanufa, yana zuwa yadanna hon aka buɗe masa Gate yakutsa motan ciki, bayan yayi parcking yafito yashiga cikin gidan, Mama na zaune a parlour tana faman kallon da tasaba, don tunda suka dawo gidan da zama yazame mata jiki kallon, zama yayi akan kujeran da yake Facing ɗin nata, ita kuma kallon sa take yi ganin yanda duk yasauya face ɗin sa kamar wani abu na damun sa, hakan yasaka tatambaye shi da cewa
“Lafiya Nura meke damunka ka fita cikin walwala kadawo fuska a turɓune?”
Sai alokacin yakalle ta yace “Mama Zainab ce”.
Numfashi Mama taja don tariga tasan da zancen, sai da taɗan ɗau lokaci tana ci gaba da kallon sa kafin tace “wai ni Nura meyasaka baza ka nemi wata bace sai ita? Taya zaka zauna yarinya tana wulaƙanta ka amma kaƙi kasauya ta? Ni fa dama hankalina be kwanta da ita ba tunda ita ɗin ƙawar Halwa ce ƙut da ƙut, kuma dama abokin ɓarawo ai ɓarawo ne ban ɗauke tsammanin itama halin su ɗaya ba”.
Cike da rashin jin daɗin kalaman Maman nashi yace “Mama don Allah ki dena aibanta ta, Ni nasan Halin Zainab baza ta taɓa aikata abinda Halwa tayi ba duk da kuwa suna ƙawaye, kuma Ni ita kaɗai nake jin zan iya aura sabida ina matuƙar ƙaunar ta tun ba yanzu ba, kawai ki taya ni da addu’a shine nafi buƙata a wajen ki”.
Yana ƙarisa maganar nasa yamiƙe yayi hanyan fita, ita kuma Mama tabi shi da kallo har yafice, sai kuma takaɗa kai cike da tausayin ɗan nata a ranta tana masa fatan alkhairi
…… …… …… …… . ..
Tun tafiyan Halwa babu daɗewa Nura yazo ma iyayen sa da zancen zai tafi Legos wani kasuwanci acewar sa bazai dogara da aikin gwamnati ba, dama can yana siye da sayarwa ne na kayan gona, yanda yayi musu bayani akan kuɗin da zai iya samowa hakan yasaka basu wani ja maganar ba suka barsa yatafi, to be rufa watanni uku ba yadawo da zunzurutun kuɗi acewar sa sana’ar da yayi ne Allah ya albarkace sa, iyayen sa sunyi murna matuƙa da samuwan ɗan nasu, acikin lokaci ƙanƙani Nura yayi kuɗi ya buɗe shaguna da yawa ya saka masu kula dasu, kuma ya siyan ma iyayen sa gida me kyan gaske suka koma, sannan shima ɗin yasoma ginin sa inda zai yi aure
Tun dawowar sa yasoma neman Zainab a matsayin wacce zai aura, amma har yanzu ita Zainab taƙi amincewa dashi, shi kuma yaƙi haƙura da ita sabida mugun son da yake mata.
.
_To ya za’a kaya?_
_Plz Kar ku manta kuyi_
*Shere*
*Vote*
*Comments.*
[11/1/2020, 9:20 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
_*NANA FARUK* wannan shafin naki ne ke kaɗai, Allah yabar ƙauna????_
.
*CHAPTER 40*
Turo ƙofan Mom tayi tashigo cikin ɗakin, Nazeefa dake zaune tsakiyan gado ta tanƙwashe ƙafafun ta tana faman tunani taɗago kai tana kallon Mom ɗin, ita kuma ƙarisowa tayi tazauna gefen gadon tana kallon ta tace
“Meke damunki Nazeefa?”
Nazeefa kallon Mom tayi tace “babu komi Momy”.
“Ban yarda ba ki faɗa min gaskiya idan da akwai abinda ke damun ki, gaba ɗaya na lura dake tun da daɗewa kina cikin damuwa, kullum cikin tunani kike kuma kinƙi kifaɗa min abinda ke damun ki, bana son in ganki cikin damuwa hakan na damuna coz Ina jinki tamkar ƴata ta cikina ne”.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana jin hawaye na son zubo mata, idan da tana da daman faɗa mata abunda ke damun ta da tuni tadaɗe da sanar mata, sai dai kashhh baza ta taɓa iya faɗa mata gaskiyan abinda ke cin zuciyarta ba
Dafa bayanta Mom ɗin tayi tace “ki sanar dani kinji Nazeefa zan miki duk abinda kike buƙata idan har ina da halin yi, bazan taɓa barin hawayen ki yazuba ba zan kasance me share miki hawayen ki”.
Wani irin sanyi Nazeefa taji acikin ranta tare da wani irin ƙaunar Mom na sake shiga zuciyarta, sai dai baza ta taɓa iya faɗa mata ciwon son ɗanta ne yakamata ba, “to taya?” Hawayen da taji suna son zubo mata ne tayi saurin mayarwa tana ɗago kai takalli Mom cikin sanyin murya tace
“Momy babu abinda ke damuna, idan har akwai kece ta farko da zan faɗa miki sabida na ɗauke ki tamkar ke kika zuƙuna kika haife ni, ki yarda dani Momy babu abinda ke damuna”.
Shiru Mom tayi tana kallon ta, sai dai ko kaɗan bata yarda babu abinda ke damun ta ba bcoz ko wanene yaga halin da take ciki dole yatabbatar wa kansa tana cikin tsananin damuwa, sosai take mamakin abinda ke damunta har takasa bayyana mata, amma kuma tayi wa kanta alƙawari sai ta gano ko me ke damun ta kuma sai ta share mata hawaye da iznin Allah, ajiyan zuciya tasauke kafin tace
“To shikenan na yarda dake, amma duk abinda ke damun ki kiyi gaggawar sanar dani ki dena ɓoyewa kinji?”
Gyaɗa kanta Nazeefa tayi sai kuma tace “insha Allahu Momy”.
“Ok tashi ki cire kayan makarantan akwai inda zaki raka Ni”.
Amsa mata tayi tana tashi tare da saukowa daga kan gadon, itama Mom tashi tayi tafice a ɗakin, sauya kayan ta tayi tasanya doguwar rigan abaya Blue Black, sannan sai tayi Rolling da ɗankwalin abayan, komai bata shafa a fuskarta ba illa flat shoes da tasanya a ƙafafuwan ta, sosai tayi kyau white skin ɗin ta sai sheƙi yake yi kasancewar ta samu hutu har wani ƙiba tayi tare da ƙara girma, fita tayi ta’iske Mom a parlour suka fice, motar Mom ɗin suka hau drever yatuƙa su suka bar gidan.