Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

        A wani ɗan madaidaicin gida Drever yasauke su suka fito suka shiga, matar gidan tana zaune a parlour tatarbe su cikin fara’a tare da kawo musu Drinks, sai da suka ɗan yi hira kafin Mom tace

“Yauwa Hajja Turai maganar da muka fara dake a waya ne akan kayayyakin da zaki ɗauko min a London, don haka shiyasa nataho muyi maganar sosai sai ki faɗa min da yaushe zaki tafi?”

Cikin fara’a Hajja Turai tace “ai ina da kaya a ƙasa gaskiya ba yanzu zan koma ba, inaga sai nan da One Month, yanzu abinda yakamata dai sai kiyi min list ɗin komi kibani hakan zai fi, bari in ɗauko miki Littafi”.

Miƙe wa tayi tashige ɗaki babu jimawa tadawo riƙe da Littafin tamiƙa mata, Mom amsa tayi tana cewa

“Yauwa sannan kuma zan baki saƙon ƴata ga tanan, itama ɗin kizaɓo mata kayan fitan biki masu matuƙar kyau, acikin gwala-gwalan da zaki siyo min sai ki ɗaukar mata ɗaya, Ni dai ina son ki gwangwaje ta sosai komi yakasance Expensive ne nata”.

Dariya Hajja Turai tayi tana kallon Nazeefa tace “ai babu matsala Hajiya Hajara duk abinda kikeso hakan za’a yi, amma ko itace Amaryan don naga kina ji da ita?”

Mom tace “a’a ƙanwar sa ce ai”.

“Allah Sarki”. Cewar Hajja Turai still tana kallon Nazeefa

Mom tace “don Allah Hajja kaya masu kyau nake so sabida kinsan bikin Autana ne that’s why nazo wajen ki, and sai kuma Furnitures ɗina don Ina son nasauya komi na ɗakina”.

“Baki da matsala insha Allahu duk abinda kikeso zan yi ƙoƙarin naga na samo miki dai-dai da zaɓinki”.

Ita kuwa Nazeefa da tun sanda tazauna tasad da kai ƙasa tana sauraron su, wani irin ƙunci take ji a maƙogaron ta, ji take yi tamkar tabuɗe baki tayi ta zunduma ihu sabida tsaban baƙin ciki, har hawaye sai da tai ta sharewa batare da sun kula da ita ba suna ta tattaunawa, bayan Mom ta gama yin mata list ɗin gaba ɗaya sannan sukayi sallama suka fito, har wajen mota Hajja Turai tarako su sai da taga fitarsu kafin takoma cikin gida

Suna cikin motan Khalil yakira Mom, bayan tayi peacking call ɗin suka gaisa take cewa

“Ɗazu ka kira bana ji ne matsalan network ne, yanzu kuma muna kan hanya ne naje gidan Hajiya Turai”.

Khalil da be san ma wacece Hajiya Turan ba sai tambayan ta da yayi “me taje yi?”

Nan take faɗa masa sannan taƙara da cewa “wai kuwa kana kiran surukar tawa don nasan Halin ka?”

Shiru yayi don be san amsan da zai bata ba, shi idan har basu suke masa maganar bikin ba sam mantawa yake yi zai yi aure, kuma ita yarinyan tun sanda yabar ƙasar yamanta irin ta, ko za’a tsare sa da bindiga yafaɗa yanda take bazai iya ba, abinda yasani kawai fara ce ita but kamannin ta ya daɗe da gushe masa, sunan ta ma kanshi be riƙe ba duk da su Mom wani lokacin suna faɗar sunan idan suna waya

“Kayi shiru ko dai dagaske ba ka kiran ta?’

“Ina kiran ta mana Mom”. Yafaɗa cike da sanyin murya don shi sai yanzu yasan be kyauta ba tunda ko Phone numbern ta be amsa ba

Daga nan sallama suka yi Mom ta’ajiye wayan cikin jaka, kallon Nazeefa da tatakure a jikin motan tayi idanuwanta a rufe ruf, numfashi kawai Mom taja tana ɗauke kai.

.

*** *** *** *** *** ***

    Da hannu biyu tazuba tagumi tana tunani har batasan sanda Mami tashigo tatsaya a kanta ba, sai da tagama ƙare mata kallo kafin takira sunan ta

Firgigit Kausar tayi tana ɗago kai takalli Mamin nata

“Wai ke lafiyan ki lau kike yawan tunani meke damun ki ne?”

Shafo fuskarta da hannun ta tayi cikin sanyin murya tace “babu komi”.

“Baza ki faɗa min ba kenan?”.

“Mami babu komi fa tunanin aiki ne kawai”.

Gyaɗa kai kawai Mami tayi kafin tace “to ki tashi kije Sharif na parlour yana jiran ki”.

Kausar kallon Mamin tayi fuska babu walwala tace “Mami kice masa bana nan Ni bazan iya fita ba”.

“Wai ke kanki ɗaya kuwa? Wai meyasaka yanzu bakison fita ne idan yazo? Ko faɗa kukayi ne?”

Kausar tace “a’a kema Mami kinsan Da da yanzu ba ɗaya bane, bana son takura ne kawai”.

Baki Mami tabuɗe tana kallon Kausar, ita kanta da take Mahaifiyar ta tasan Kausar ta sauya, gaba ɗaya ta dena walwala agidan, sai tashige ɗaki ita kaɗai tazauna su rasa me take yi cikin ɗakin, kuma duk uzurin da zata kawo be da wani kan gado, ajiyan zuciya tasauke kafin tace

“Ki fito ki same sa yana parlour yana jiran ki”.

Daga haka tajuya tafice batare da tajira ta bakinta ba

Ita kuwa Kausar ba’a son ranta ba tamiƙe tafito, yana zaune a parlour’n shi kaɗai, gaban sa duk an cika masa da kayan motsa baki amma be taɓa komi ba, shi kansa idan kakalle sa baya cikin hayyacin sa duk ya rame yasaka damuwa a ransa sakamakon sauyawan da Kausar tayi masa, kuma hakan sosai ke barazanan tarwatsa rayuwan sa sabida ba ƙaramin so yake mata ba, kullum ji yake yi ƙaunar ta na sake hauhawa acikin ransa memakon raguwa, ya rigada ya saka ta acan cikin zuciyarsa wanda rabuwa da ita zai mishi matuƙar wahala kuma zai taɓa masa rayuwan sa

Tunda tafito yake kallon ta har taƙariso tazauna akan kujeran dake Facing nasa, cikin sanyin murya batare da ta kalle sa ba tace

“Barka da zuwa”.

Murmushi yasaki yace “yauwa gimbiyata kina lafiya?”

“Lafiya lau”.

“Kwana biyu ina ta kiran wayan ki akashe na kasa haƙura dole nayi tunanin zuwa yau, shin meke faruwa ne Baby?”.

Sai alokacin taɗan kalle sa kana taɗauke kai tace “kashe wa nayi”.

Shiru kawai yayi yana kallon ta, sai kuma daga baya yace “wai Kausar ko dai kin samu wani ne kikeson min wulaƙanci?”

Sosai taɗago kanta a wannan karon tana kallon sa, shima ɗin ita yake kallo cike da tuhuma, sun jima suna kallon juna batare da ta sami amsar da zata bashi ba kafin taɗauke kai tare da haɗiyan yamu

“Kinyi shiru ina son insan abun da yasaka kikeson juya min baya Kausar, don Allah ki sanar dani idan wani laifi nayi miki wlh nayi alƙawari zan nemi yafiyar ki”.

Sai kuma yayi shiru yana saukowa kan kujeran yayi Neeldown agaban ta yana ci gaba da cewa

“Idan ma kina so in duƙa a gaban ki ne to gani na duƙa don Allah ki yafe min, wlh Kausar ina matuƙar ƙaunar ki bazan iya rabuwa dake ba, dan Allah ki taimaki rayuwata ki faɗa min laifin da nayi miki in nemi gafarar ki”. Yaƙarike maganar nasa da rawan murya

Kausar kallon sa kawai take yi don batasan sanda yazuƙuna ba, take taji hawaye sun cika mata idanu sabida tausayin sa, tasan da cewa tana ƙaunar Sharif matuƙa amma yanzu shigowar Khalil rayuwan ta tarasa soyayyan sa a zuciyarta, tayi iya ƙoƙarin ta don taga tayi yaƙi da abinda ke damun ta amma ina ta kasa, ta kasa dawo da ƙaunar da take masa aranta, burin ta yanzu kawai tazama mallakin Khalil, amma tarasa ta wani hanya ne hakan zai faru, tasan da cewa yanzu Khalil yayi mata nisa nisan da baza ta iya samun sa ba tunda yana shirin aure

Wani irin kuka yataho mata batasan sanda tasake sa ba, jikin Sharif har yana rawa wajen matsowa kusa da ita yana tambayan abinda ke faruwa da ita, gaba ɗaya ya shiga damuwa ya rasa yanda zai yi, ita kuwa kukan take yi tana toshe bakinta da hannayen ta, sosai take tausayin kanta don batasan halin da zata shiga ba nan gaba

“Dan girman Allah kiyi shiru Kausar, kiyi shiru ki faɗa min abinda ke damun ki, wlh idan har Ni ne baki ƙauna yanzu zan barki, zanyi nesa da rauyuwan ki idan har hakan zai saka ki farin ciki, bana son kukan ki”.

Still kallon sa take yi da idanuwanta da sukayi jazur tana ci gaba da kukan ta, daƙyar ta’iya buɗe baki tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button