BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

“Bakayi min komi ba Sharif kuma babu abinda ke damuna, idan har ka shirya aurena to katuro”.
Tana faɗan haka tatashi da gudu tayi ɗakin ta, tana zuwa tafaɗa kan gado tana sakin wani kukan da ƙarfi
Ta san da cewa hakan shine kaɗai mafita agare ta, ta hakan ne kaɗai zata sami salama tamanta shi cikin rayuwanta, hakan zai sa tayi nesa dashi gaba ɗaya.
_ ****_
A cikin kwana biyu Sharif har ya turo magabatar sa, kuma komi ya kammala har an saka rana nan da wata biyar masu zuwa, SAI MUCE ALLAH YAKAIMU LAFIYA MUSHA BIKI????
.
_Plz karku manta da comments da Vote_
[11/7/2020, 2:21 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 41*
*FIVE MONTHS AGO*
Yau ake saka ran dawowar Brr. Ibarahim Khalil, don haka Mom tashirya tarban Autan nata, Sameer da matar sa tare da ƙanwar ta Abida duk sun zo gidan su ma tarban sa, su suka taya Mom girki tare da gyare-gyaren gida, anyi soye-soye anyi duk abinda yadace sannan ne lokacin driver yatafi ɗauko sa a airport don ƙarfe 02:00pm. Jirgin su zai sauka, drever na tafiya shima Brr. Tahir yazo da nashi iyalin matar sa Suhaila da ɗan su ɗaya Adam.
Bakin Nazeefa har kunne sabida tsaban farin ciki zataga Yayan nata kuma mafi soyuwa a ranta, da ita ake aikin komi don ko kaɗan babu wanda yakula da yanda tasaki jiki take ta fara’a kamar bakin ta zai tsake becouse su ma ɗin cikin su kowa tashi murnan ya ishe sa.
Lokacin da jirgin yai landing *BRR. IBRAHIM KHALIL* yana ɗaya daga cikin waɗanda suke sauko wa ta matattaƙalan jirgin, Ni dai gaskiya bangane sa ba sai dai bansani ba Fans ɗinsa ko ku zaku gane sa, don dagaske ya sauya sosai fiye da yanda nasan shi, gold skin ɗin sa yayi wani irin haske sosai sai ɗaukan ido yake yi, hutu da kwanciyar hankali kawai nake hangowa a tattare dashi da alamun dai ƙasar tayi mugun amsar sa don ba ƙarya ya sauya ɗin, sai zuba murmushi yake yi abinda ba kasafai kake gani a face ɗin sa ba
Har sanda ya’amso trolly ɗin sa yafito haraban airport ɗin sannan ne drever yahange shi yataho dasauri yazo wajen sa yana miƙo masa gaisuwa, amsa masa yayi cike da fara’a sannan suka shiga mota sukayo gida, bazan iya fasalta muku yanda Familyn suka nuna farin cikin su ba, bayan an gaigaisa ya huta sosai sannan aka wuce dainning, anan kowa yaci abinda yakeso tukun suka dawo parlour, hira aka dasa ana ta dariya, wlh idan kukaga Khalil baza kuce shine ba domin har dashi ake ta wasa da dariya, kai sai ince har da ɗabi’u aka sauyo masa acan ɗin, Nazeefa da Abida kuwa babu abinda suke yi sai kallon sa ko wacce zuciyarta na mafarkin yakasance nata na har abada, don har alokacin Abida taƙi tacire sa aran ta duk da kuwa Hakima sai da tagargaɗe ta tamanta dashi baza ta taɓa samun sa ba coz yanzu aure zai yi, kuma itama taso ƴar uwan nata ta aure shi har mitan maganar tarinƙa ma Sameer but basu samu nasara ba.
Su Brr. Tahir suka soma tafiya sannan Khalil shima yayi musu sallama drever yanufi gida dashi, lokacin da suka isa layin su motoci yai ta gani duk sun cika layin, sai da suka matso gab gidan sa sannan ne yafahimci agidan su Kausar ake taron, ga jama’a nan burjik awaje maza da mata kowa na sha’anin gaban sa da alamu dai biki ake yi, mamaki sosai ne a fuskarsa sai dai be iya furta komi ba har Drever yayi hon agidan sa aka buɗe musu Gate motan tashige, bayan drever yayi parcking Khalil yafito lokacin duk ma’aikatan gidan sa sunyo wajen suna miƙa masa gaisuwa, haka yai ta amsa musu cikin sakin fuska sannan ne yanufi cikin gida Sale na biye dashi da trolly ɗin sa
Cikin gidan an gyara masa ko ina kuma yasan duk aikin Sale ne hakan ya faranta masa rai sosai, anan parlour yaba ma Sale umarnin ya’ajiye Jakan sannan yafice, shi kuma yaja trolly ɗin yanufi ɗakin sa, yana shiga yasaki hannun trolly ɗin yazauna gefen gadon sa, ya ɗan yi wajen mintuna 5 kafin yatashi yacire kayan sa yashiga wanka, yayi kusan mintuna talatin kafin yafito yashirya cikin farar t.shit da gajeren wando fari da ɗige-ɗigen ja, zuwa yayi yazauna kan kujera yasoma latsa wayan sa, kusan mintuna goma yaɗauka sannan yasoma laluban numban Kausar yadanna mata kira
Lokacin Kausar na zaune a ɗakin ta tare da ƙawayen ta an gama mata kwalliya, kasancewar yamma tayi har motocin ɗaukan amarya sun zo, becouse acan garin Daura zasu zauna tunda anan ne Sharif ɗin yake aikin sa, duk da dama nan ne tushen sa amma iyayen sa anan Katsina suke zaune
Tsananin firgita Kausar tayi da ganin wanda yake kiran ta har batasan sanda takusa sulmiyar da wayan ƙasa ba, sai wata ƙawarta dake kusa da ita ne tayi saurin taro wayan tana cewa
“Kee Kausar Ina hankalin ki yaje zaki saki waya ƙasa?”
Kausar da tayi mutuwar zaune sabida mamaki, ƙyafta idanun ta tayi da suka cicciko da hawaye tana bin wayan da kallo, ƙawarta me suna Rumaisa tamiƙo mata wayan da aka sake kira akaro na biyu tace
“Riƙe gashi an sake kira”.
Ahankali tasaka hannu ta’amsa wayan sai dai takasa anwer call ɗin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ganin kiran sa a wannan lokacin ba duk da tasan cewa lokacin dawowan sa yayi, tun sanda yatafi basu taɓa waya dashi ba wannan dalilin ne yasaka tashiga ruɗu da bugawar zuciya
Shi kuma a fannin Khalil tunda yatafi ya nemi layin ta sama da biyar duk sanda zai kira ta wayanta sweech off, daga ƙarshe shine yadena kiran ta gaba ɗaya don a tunanin sa ko akwai matsala ne, ita kuma kullum da tunanin kiran nasa take kwana dashi kuma take tashi, koda yaushe tana jiran taga kiran sa amma har tsawon wannan lokacin babu shi babu labarin sa kuma gashi ita bata da numaban sa na can
Batasan tana zub da hawaye ba sai da Rumaisa tadafa ta tana cewa
“Wai lafiyan ki ƙalau kuwa? Kuka fa kike yi Kausar?”
Sai alokacin tadawo hankalin ta tana kallon Rumaisa da tabi ta da kallo cike da tsananin mamakin ta, lokacin gaba ɗaya hankalin ƴan matan har ya dawo kan su, dasauri Kausar tatashi batare da ta furta komi ba tashige Toilet tana rufo ƙofa, hakan yasaka duk suka bi ƙofan da kallo suna tunanin abinda ke faruwa da ita
Tana shiga kiran yasake katsewa, sai ga wani kiran don shi Khalil ya kasa haƙura da kiran nata, sai da tajingina da bango kafin ta’amsa kiran tana sakawa a kunne, cikin ƙasa da murya tace
“Hello”.
Daga can ɓangaren Khalil kuwa shima jingina bayansa yayi da kujera cikin cool voice ɗin sa me daɗi yace
“Hello Friend”.
Kausar danne duk abinda ke cikin ranta tayi cikin ƙarfin hali tace “dama ashe zaka iya mantawa dani?”
Ɗan shafo sajen sa yayi yace “Kausar kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba, amma kuma nayi ta neman Phone Numban ki bana samun ki”.