BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Hannun ta taɗago tana kallon fingers ɗin ta da suka sha jan lalli, cikin son maida kukan da yataho mata tare da ɗaura jarumta a muryan ta tace
“Na gane Barrister, ya hanya to?”
“Alhmadulillah.. da fatan kema kina lafiya?”
Murmushi taƙirƙiro dai-dai lokacin da hawaye suka sauka kan kuncin ta tace “sai alheri friend”.
Khalil shima cikin murmushin yace da ita “Allah ko?”
“Ƙwarai”. Tataɗa tana dariya ahankali
“To bani nasha”.
Sai da taja numfashi kafin tace “Allah yayi an ɗaura aurena yau”.
Cikin tsananin mamaki da al’ajabi Khalil yace “haba dai serious fa?”
Kausar tace “I’m serious..”
Sai kuma taɗan saki murmushi me sauti tace “kaga na rigaka ko?”
“Sosai don ban yi tunanin hakan ba, sau da dama kina bani labari kuma ban taɓa jin kinyi min maganar samarin ki ba, ashe ashe..”
Sai kuma yai dariya yana cewa “to Allah yatabbatar da alheri gaskiya naji daɗin wannan maganan”.
Shiru kawai Kausar tayi bata amsa ba, hakan ya tabbatar mata da cewa tabbas bata cikin zuciyarsa, ita kaɗai take kiɗan ta kuma take rawan ta
Murmusawa shi kuma yayi yace “Amarya kenan bari in barki haka ko? don nasan yanzu kina busy”.
Share hawayen ta tayi cikin rawan murya tace “to”.
Daga haka bata iya furta komi ba don idan tasake faɗan kalma ɗaya zata iya fashewa da kuka
Nocking ƙofan da akayi yasaka tayi saurin juyowa tana kallon ƙofan, sai kuma tamaida idanunta kan wayan lokacin ne Khalil yadatse kiran, lumshe idanuwan ta tayi tana jin wani ƙunci da baƙin ciki na mamaye ilahirin zuciyarta
“Kausar wai me kike yi aciki? ki buɗe mana”.
Maganar Rumaisa yadawo da ita cikin hayyacin ta, dasauri tasanya hannu tashare sauran hawayen ta tanufi ƙofan tabuɗe, duk bin ta suka yi da kallo har da ƙanwar Mamanta da tashigo yanzu, ita kuma sai tasad da kai ƙasa don bata son su fahimci wani abun
Ƙanwar Maman nata ne tace “wai me kuke jira ne, ku fito motoci sun rigada sun iso”.
Juyawa tayi tafita tana cewa “su hanzarta”.
Kausar sai da tasha nasiha wajen ƴan uwa kafin aka fito da ita, a lokacin sai kuka take yi, Ni dai bansan ko na menene ba ni dai naga an saka ta a mota sun fice, to sai muce Allah yasanya alkhairi *KAUSAR.*
……. ……. . .. ….
Khalil kuwa tunda suka gama wayan ya’ajiye yalumshe idanun sa yana tunani, yaji babu daɗi yanda suka rabu sabida shaƙuwan da sukayi, be taɓa tunanin baza su sake haɗuwa ba idan yadawo, ya so ba yau bane auren ta ko shima yahalacci auren nata, amma gashi har anyi an gama batare da yaje mata ba, hakan yaƙara saka shi rashin jindaɗi
Allah Sarki haka shaƙuwa yake dama, a ranan kuwa haka yawuni shiru duk bashi da walwala, har yayi sallan magriba da isha’i yadawo gida komi be ci ba yakwanta, ya daɗe yana tunani kafin barci ɓarawo yaɗauke shi.
.
**** **** ***** *****
A cikin kwana biyu da dawowar Khalil sai gashi ya samu kira agidan gwamnati, koda yaje meeting akayi dashi, sun tattauna na wajen awanni kafin su gama, daga ƙarshe dai an ɗauke shi aiki a matsayin Lauyan gidan
Gwamnati, ga albashi me tsoka da zai riƙa samu, duk da dama can sosai Khalil yake samun kuɗi don zan iya cewa ko mahaifin sa be fi sa kuɗi ba, sai dai shi Lauya ne me zaman kansa haƙƙin talakawa kaɗai yake ƙwatowa, Duk wani mara galihu idan har yaje gare sa shi kuma zai share masa kuka, asannu-asannu sunan sa yayi shura sosai talakawa sun soma sanin sa, gaba ɗaya gidajen talabijin da rediyo, jaridu duk maganar sa yanzu ake yi, acikin lokaci ƙalilan Allah ya ɗaukaka shi fiye da Da, kuma duk saboda ƙarin girman da yasamu ne yanzu da kuma ɗaukan sa aiki da akayi agidan gwamnati, sanin da talakawa sukai mishi yanzu har sun soma kawo masa Cases kala-kala, shi kuma don yashare musu kuka haka yake faɗi-tashi wajen taimaka musu da ƙarfinsa da kuɗin sa.
_dama akace dare ɗaya Allah kan ɗaukaki bawa fiye da tunanin me tunani, yanzu sunan Brr. Khalil ya zagaye duk faɗin garin Katsina da kewaye sabida ƙwazon sa, sosai ake ji dashi.
October 2020.
[11/7/2020, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: ????
????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 42*
An tsai da ranan auren Brr. Kahlil da Saleema nan da Four Month, zuwa lokacin tarigada ta rubuta Final Exams ɗin ta, asannu-asannu rayuwa taci gaba da tafiya cikin nasarori da akasin sa, wasu tazo musu da daɗi wasu kuma tazo musu a yanayin da babu daɗi, ga dai shi Saleema a wannan lokacin sosai ciwon ta yatashi kullum cikin nema mata magani ake yi, wani lokacin adace wani lokacin kuma rashin sa, ga kai ya ɗau zafi karatun su ya zo ƙarshe haka take lallaɓawa take zuwa School sai dai ba kullum ba, duk ta rame sosai take jin jiki.
A fannin Khalil kuwa yanzu yana da Numban ta kuma yana kiran ta akai-akai yatambayi jikin ta tunda yasan bata da lafiya, kusan sau biyu yana zuwa gidan, shima yanzu aiyuka sun yi masa yawa baya zama sosai kullum cikin aiki yake, ahaka Allah yasa biki yaƙarato ko wani fanni tuni sun soma shiri ana hidima kala da iri, amma ta fannin Amarya babu lafiya har yanzu sai dai ba kamar da ba don yanzu jikin da sauƙi
Ummi tare tahaɗa su da Halwa ake musu gyaran jiki, itama yanzu Halwa ta soma shirye-shiryen zana WAEC da zatayi.
Yau ta kasance saura sati ɗaya biki kuma a yau ne Halwa zata soma zana jarabawan ta, haka tatsallake tatafi bada son ranta ba don ko kaɗan bataji daɗin yanda za’ayi bikin Saleema ita kuma tana Exams ba, sai idan taje tadawo ne ake Hidiman biki da ita.
Fannin su Mom yanda suka ɗau bikin nan da girma zai baka mamaki, komi cikin wadata da nuna su ɗin masu kuɗi ne don tun ana saura sati biyu ake shagulgula agidan, idan kashiga cikin gidan ko matsuguni baza ka samu ba tun kafin ma bikin yazo kenan, ƴan uwa da abokan arziƙi duk sun cika gidan.
Nazeefa kuwa damuwan da tasaka aranta har bacci bata iya yi ishashshe hakan yahaifar mata da ciwon kai me tsanani tare da zazzaɓi, duk shagulgulan da ake yi tana ɗaki taƙule taƙi fita ayi da ita, sosai take jin jiki har sai da Sameer yakaita asibiti aka dubata, koda suka dawo Mom tayi ta kula da ita tana bata drugs duk ta tashi hankalin ta, gaba ɗaya ko lokacin kanta bata dashi ga jinyan Nazeefa ga hidiman mutane, wannan yasaka taba Nazeefa tausayi sosai hakan yasa tadaure taɓoye duk abinda ke damunta tayi kamar ta samu sauƙi tana fitowa ana biki da ita, hakan yasa Mom taji daɗi har hankalin ta yakwanta.
Fannin Ango kuwa baya zama yanzu sabida Case ɗin da yake gudanarwa a Court, shiyasa duk wani shagulgula bashi ciki, sai idan ya sami kansa ko zuwa dare ne yake zuwa gidan su.
….. …… …… …… ….