Uncategorized

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

Gidan su Amarya su ma ba laifi ana ta shagulgula duk da babu wani armashi Amarya tana kwance babu lafiya, wannan dalilin ne ma yasa basu shirya komi ba in banda taron bikin kawai da za’a gudanar

Duk abunda ake ma Amarya anyi wa Saleema, an mata lalli an mata gyaran jiki komi an mata, sosai tayi kyau tafito a Amaryan ta duk da kuwa zallan raman da tayi

Sai ana gobe biki ita Halwa akayi mata nata Lallin sabida ranan bata da Exams, kuma a ranan akayi musu gyaran kai ita da Saleema, komi har gida ake zuwa ayi musu basu zuwa ko ina.

*** **** **** **** ****

Washe gari ya kasance Saturday aka shaida ɗaurin auren *BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA’UF* tare da Amaryan sa *SALEEMA MUSTAPHA*

Ana gama ɗaurin auren ango da abokanan sa suka tafi Hotel inda zasuyi ƙwarya-ƙwaryan liyafan da suka shirya.

*GIDAN SU AMARYA*

Amarya tasha kyau cikin shigan ta na Material Less me ruwan Hoda da ratsin ash colour, ɗinkin riga da sket da suka ɗauki jikinta sosai, ba’ayi mata kwalliya ba don taƙi yarda shiyasa ba’a matsa mata ba

tana zaune akan gado ta ɗaura Husna ajikin ta da take ta faman wasa da kayan Saleeman, sosai yarinyan tasake girma ga wayau sosai, idan kaganta baza kace watanni tara da haihuwar ta ba

Cikin ɗakin akwai friends ɗin ta na school su wajen biyar, sai hira suke yi suna shewa, wasu kuma suna mata tsiya “gwara tawarke don dole akaita yau ɗin”

Ita kuwa ɓata fuska tayi sai sake marairaice face ɗin ta take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakasan ta faɗa ainun hakan yasa tasake haske sosai, bata kula su ba sai dai bin su da ido da take yi

Ana haka Halwa taturo ƙofa tashigo, dawowarta kenan daga Exams da taje tarubuta, fuskarta yalwace da murmushi take kallon Saleema da itama tasanya mata idanu tana ƙara ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka, takowa tayi tashigo ciki tana gaisawa da ƙawayen Saleeman sannan tanemi wuri tazauna gefen Saleema tana sake yalwata fuskarta da murmushi, sosai take farin ciki a yau ɗin tana taya ƴar uwan nata murna

Hannu tasaka tadafa kafaɗun Saleema bakin ta yaƙi rufuwa, sai kuma tamaida hannun kan kumatun ta taja tana cewa

“Haba ƴar uwa ya haka kin ɓata fuska? Don Allah ki saki ranki kiyi farin ciki yau ranan ki ne, ko so kike Angon yayi tunanin bakya son sa ne? Kinga hakan zai jawo masa matsala akasa gane kansa”.

Hakan yasa Saleema tasaki dariya babu shiri saboda maganar Halwa ɗin, ita kuwa Halwa kallon ta take yi tana murmusawa cike da jindaɗi, sai kuma tamaida kallon ta kan Husna tana haɗe rai tace

“Waye kuma yakawo wannan yarinyan nan?”

Itama Saleema kallon Husnan tayi da tatsare su da idanu ta saka hannu ɗaya cikin baki tana ɓashe bakin kamar tana jin su

“Kawo ta in kaita wajen Larai, yau fa ranan ki ne be kamata kizauna kina raino ba, banda abinki ma ke da baki da lafiya?”

Ture hannun ta Saleema tayi tana hararan ta tace “to Ni nace akawo ta ina ruwan ki?”

“Haba Sister don Allah yau rana ɗaya kibarta wajen Larai”. Cewar Halwa tana sake kai hannu zata ɗauke ta

Sake ture hannun Halwan tayi tarungume ta da kyau tana cewa “Ni fa nace akawo min ita, wlh babu inda zata don tana nan wajena har mu tafi”.

Waro idanu Halwa tayi tana cewa “wai da ita kike nufin zaki tafi?”

“Eh mana.. da dake zan tafi?”

Sai ƴan ɗakin dake kallon su suka kwashe dariya

Zaliha tace “kai wani lokacin Saleema bata da hankali al’ƙur’an tana jinta kamar sokuwa ne”.

Sai suka sake ɓarke wa da dariya, ita kuma tabi su da harara tana cewa

“Ni ce bani da hankali ko?”

“Ai da gaskiyar Zaliha idan ba sokuwa bace ke taya ma zaki tafi da yarinyan nan? Ai mijin ma sai yakoro ki”. Cewar Dija Babbar ƙawarta tana sake kecewa da dariya

Halwa murmushi tayi tace “Sister wlh kuwa maganar su gaskiya ne, kema kinsan Ummi baza ta barki ki tafi da ita ba gwara ki sauya shawara”.

Shiru kawai Saleema tayi bata sake cewa komi ba

Cikin lallami Halwa tasake cewa “kinga koda nan da sati ɗaya ne sai in kawo miki ita idan ma wai tafiyar da ita zakiyi”.

Saleema tace “sati ɗaya ai yayi yawa, sai dai idan zakiyi min alƙawari gobe”.

Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi don ba wai ta yarda zata kai mata ɗin ba, daga nan hira sukaci gaba dayi, sai da Saleema tace ma Halwa taje tashirya sannan tamiƙe tashiga wanka.

               *****

Da ƙarfe 08:00pm. Akazo ɗaukan Amarya, tasha kuka sosai haka taƙanƙame Ummi taƙi tafiya, daƙyar aka samu aka shiga da ita mota Halwa tazauna kusa da ita tana rarrashin ta

A gidan sa aka kaita, sosai gidan yaɗau hankalin duk wanda yashigo, kamar ba gidan da akayi amfani dashi ba komi an sauya sai ƙamshin sabunta yake yi

Ɗakin ta kusa dana Khalil aka shigar da ita, haka mutane sukai ta zagayawa suna ganin abun arziƙi har da Halwa a zuwa gani, anan sukayi sallan isha’i suna ta hayaniya kamar zasu tsaga gidan

Wajen ƙarfe 10:00pm. Abokan ango suka zo tafiya dasu, lokacin ne itama Halwa takira Drever’n gidan su A wayan da Abba yasiya mata don yazo yaɗauke ta, ko kaɗan bata son bin abokan Angon sabida yanda wani yamaƙale mata ɗazu da suka zo daga ta buge sa bata sani ba, ita ta ma rasa uban wa yace musu ita ɗin Sister ɗin Amarya ce, yanzu da suka shigo parlour’n sai faman kiran ta suke yi, komi akayi sai suce “ina Sister ɗin Amarya tazo tayi musu sheda” daga ƙarshe ma tashi tayi tashiga ciki tazauna kusa da Saleema dake zaune saman gado

Har Drever yazo basu tafi ba, sannan ne ma suka soma haraman tafiya, anan ne fa Saleema tariƙe Halwa tana kuka wai baza ta tafi ba, in banda dariya babu abinda su Dija suke mata sai faman tsokanarta suke yi, daƙyar dai tasaki Halwa suka tafi suka barta ita kaɗai kamar Mayya.

.

_Nace ko ina Mijin Oho?_????????

[11/7/2020, 3:02 PM] نفيسة أم طاهرة: ????

????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *F.W.A????/*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 43*

Ƙarfe 10:30pm. Su Khalil da Brr. Tahir tare da Sameer suka shigo gidan, daƙyar ma Khalil yayarda suka biyo shi don da yace “baya son rakiyan”. Shi da kan sa yashiga har ɗakin ta yace “tafito parlour” daga haka yajuya yafita, ita kuma tamiƙe jiki a sanyaye tagyara mayafinta tafito, ahankali taƙarisa tazauna aƙasa tana gaishe su, cike da fara’a suka amsa sannan ne Sameer yasoma musu wa’azi cikin raha, daga ƙarshe suka yi musu fatan alkhairi tare da sanya alkhairi a auren nasu

Har bakin Gate Khalil yaraka su da zasu tafi, yadawo yatarda Saleema tana nan zaune inda take, be ce komi ba yanufi ɗakin sa, yana shiga yasoma cire babban rigan dake jikin sa bayan ya cire Hulan kansa, agogon hannun sa yacire tare da cire links ɗin rigan sa yazube su yanufi parlour

Har yanzu tana nan zaune inda take, zama yayi kan kujera yana kallon ta, sai kuma yaɗauke kai yana kallon ledan da suka shigo dashi, miƙewa yayi yanufi kichen sai gashi ya dawo da plate a hannu tare da wuƙa, zama yayi a ƙasa kamar yanda itama take zaune a ƙasan, yajawo ledan yabuɗe yaciro Kazan ciki yasoma yanka wa cikin plate ɗin don yayi daɗin ci, bayan ya gama duk yajera mata a gabanta da su Holandia sannan yakalle ta yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button