BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 31 to 40

“buɗe fuskar ki kici”.
Ahankali tayaye gyalen daga kanta taɗago tana kallon sa sai kuma takalli abinda ke gabanta, cike da tsananin kunya tanoƙe ko motsi ta kasa yi, ganin haka yaja baya yana ɗaukan wayan sa yasoma latsawa yana cewa
“Ki ɗauka kici nace”.
Wannan karon batayi musu ba ganin ya matsa can baya kuma hankalin sa baya kanta, hakan yasa tasoma ɗauka tana ci duk da dama tana jin yunwa amma baza ta iya buɗe ciki taci ba, kaɗan taci tacire hannun ta cikin sanyin murya tace
“Na gama”.
Ɗago kai yayi yakalli plate ɗin sannan yasake maida kansa kan waya yace “ki ƙara”.
Hannu tasaka taci gaba taci, bata daɗe ba tasake tsame hannun ta, wannan karon da yaɗago kai miƙewa yayi yaɗau komi yanufi kichen dashi, yana dawowa yace tataso su je ɗaki, miƙewa tayi tabi bayan sa, suna shiga yanuna mata Toilet tashiga tawanke hannu da bakinta tafito, yasake nuna mata kan gadon.. ta ko haye can lungu taƙudundune da gyalen ta
Shi kuwa Toilet yashiga yayi wanka yafito yashirya cikin kaya sannan yahayo kan gadon yakwanta, shiru sukayi ko wanne yana jin numfashin juna, can kamar amafarki tatsinkayi muryan sa
“Ya jikin naki?”
Cike da jindaɗi ta’amsa masa ganin yanda yadamu da ita sosai, daga haka basu sake yin magana ba har sanda Khalil yaji numfashin ta na fita da ƙarfi hakan yagane tayi barci, juyowa yayi setting ta duk da baya kallon fuskarta hakan be hana yaƙure ta da idanuwansa ba, shiru yayi yana tunani yana bin ta da kallo, abinda be taɓa faruwa dashi ba yau sai gashi zai kwana da mace
Ya daɗe ahaka yana ta saƙe-saƙe kafin yasauke ajiyan zuciya yamiƙe yakashe fitila yadawo yakwanta, addu’a yayi yarufe idanun sa, lokaci ƙanƙani barci yaɗauke sa kasancewar baya samun hutu.
Washe gari shi yasoma tashi bayan da suka koma barcin asuba, wanka yayi yashirya yasaka Milk colour ɗin Gezna da yayi masa kyau matuƙa gaya, duk da bashi da aiki ya ɗauki hutu amma Shari’an da yake yi be rigada ya ƙarƙare ba, akwai sauran aiyukan da yake yi a Court, yana cikin saka Wrest watch yaji Nocking ƙofa, fita yayi yaje yaduba yaga drever’n gidan su ne Mom ta aiko sa da breakfast, amsa yayi kawai yaje ya’ajiye a dainning table yakoma ciki, sai da yayi rubutu a ɗan Pepper ya’ajiye mata saitin kanta sannan yaɗau abubuwan da zai ɗauka yafita.
Babu jimawa da fitan sa tafarka, ahankali tabuɗe idanuwan ta yayinda ƙamshin turaren sa suka cika ƙofofin hancin ta, sake lumshe idanun tayi tana murmushi cike da jin daɗi, sai da tajima ahaka bataji motsin sa ba sannan ne tayaye gyalen fuskarta, da takardan da ya’ajiye mata tasoma cin karo, take gaban ta yafaɗi babu shiri tayi saurin kai hannu taɗauka tana jujjuya shi, sai kuma tamiƙe zaune idanun ta har yanzu akan takardan, buɗewa tayi sai taci karo da
.
_”Aslm alaikum Ni na fita zuwa wani waje bazan jima ba zan dawo, and akwai breakfast a dainning Mom ta kawo…”_
_Mijin ki✍️_
Batasan sanda murmushi yasuɓuce mata ba, kalman Mijinki shi ke ta mata yawo a ƙwaƙwalwa, gaskiya Brr. Daban ne da sauran Mazaje, duk da kuwa ta tabbatar ba son ta yake yi ba amma kuma kulawan sa agare ta da tausayin ta ya wuce tunanin me tunani, yana da halin ƙwarai sosai, memakon yanuna mata tsangwama a’a sai yana sauke haƙƙinta akansa, wannan shi ake kira adalin namiji, tayi imani koda baya son ta zata zauna dashi ahaka domin tasan shine ɗorewar farin cikin ta na har abada
“Allah yabarmu tare”.
Tafaɗa a maƙoshi tana sake faɗaɗa fara’an ta
Miƙewa tayi tasauko kan gadon tanufi ɗakin ta, Toilet tashige tawanke bakin ta tafito parlour tanufi dainning, tana jin yunwa sosai don haka baza ta iya jira har sai tagama abinda take yi ba gudun lafiyan ta, zama tayi tahaɗa tea me kauri tasha tare da ƙwai da Arish, bayan ta gama tatashi tashige ɗaki taɗauko Maganin ta cikin kayan ta taɗiba tafito tasami ruwa tasha dashi, sai kuma takoma ɗakin Khalil ɗin tasoma gyarawa musamman kan gadon da sukayi amfani dashi, duk da ita ba ma’abociya aiki bane komi yin musu ake yi, ba’a barin ta tayi komi amma aɗan kwanakin da zatayi aure sai da duk takoya abinda zai bata wahala, don bata son me aiki cikin gidan ta tana da kishi sosai
Bayan ta gama takoma ɗakin ta tayi wanka tashirya cikin farar shadda wanda tare akayi musu da Khalil ɗin, shi kuma yarigada ya saka nashi jiya, ta fito ɗas Amaryan ta sai zabga ƙamshi take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakaga ƙyallin amarci atattare da ita (aure ba wasa ba????)
Parlour takoma tazauna a lumsassun kujerun ta masu tsantsan kyau da burgewa, wayanta dake hannun ta talatsa takira Ummi, ringing biyu taɗauka
“Ummina I miss You so much”. Tafaɗa cike da zumuɗi
Daga can Ummi murmushi tayi na jindaɗi tace “me too My dear, har kin tashi?”
“Eh Ummi kuna lafiya? Ya Daddy da Halwa?”
Cikin dariya Ummi ta’amsa mata tana cewa “ai ga Halwan ma anan”.
“To Ummi bata mu gaisa”.
Miƙa mata wayan tayi suka gaisa cike da kewan juna sannan tamaida ma Ummi nan ma sukaci gaba da hira, daga baya kuma tabuƙaci akawo mata Husna, Ummi tayi ta rarrashinta akan tabari zuwa nan da sati biyu amma sam Saleema taƙi yarda ita lallai sai an kawo mata Husna yau
“Haba ɗiyata ki kwantar da hankalin ki, ki bari zuwa gobe insha Allahu zan sa akawo miki ita, kinga yau su Gwaggon ki zasu zo zasu kai ki gidan iyayen mijin naki to wa zaki bar ma wa? Ki bari gobe sai akawo miki ita kinji”.
“To Ummi amma kar yawuce gobe”. Tafaɗa a shagwaɓe”.
Daga nan sallama sukayi, tana nan zaune tana tunanin mijin nata sai murmushi take yi, sai da tagaji don kanta ga barci da tasoma ji hakan yasaka takwanta a 3sitter tana rufe idanun ta, babu jimawa barci yaɗauke ta
Can tasoma jin hayaniyan baƙinta tare da bugun ƙofa, babu shiri tatashi tana riƙe kanta dake faman sara mata, daƙyar take tafiya sabida yanda take jin wani zazzaɓi-zazzaɓi na son kawo mata cafka, tana buɗe ƙofan suka shigo nan tatare su da fara’a, duk ƴan uwan Abbanta ne dana Ummin ta su wajen biyar
Su suka sakata tashirya cikin wata Farar atamfa anyi mata Flower da kalan ja da baƙi, sosai atamfan tayi mata mugun kyau kasancewar ta fara, ga ɗinkin da yaɗauki jikin ta sosai na riga da zani, Hijab tasaka fari da takalmi ,sannan suka fito sukayo waje, a motoci biyu suka bar gidan.
*****
Tarba me kyau Mom tayi musu cike da farin ciki sai nan nan take da Saleema, hakan sosai yafaranta ran Ƴan uwanta har basuyi fargaban danƙa mata amanar ƴar su ba, ita kuma Mom ta’amshe ta hannu bibbiyu
Basu jima ba sukace zasu tafi duk da Mom tayi musu tayin abinci amma sukaƙi ci illa ruwa da suka sha, haka suka tafi suka bar Saleema anan, sauran dangin Mom da basu rigada sun tafi ba sai shigowa ɗakin Mom suke yi suna ganin amarya, bayan sun tafi yarage daga Mom sai Saleeman, duk da Saleema tasaba da Mom abaya hakan be sa taƙi nuna kunyan ta ba, Mom kuwa sai janta da hira take yi cike da ƙaunar ta, daga ƙarshe dai da taga taƙi sakin jiki da ita sai tatashi tana cewa
“Tunda kinƙi sakin jiki dani bari in Kira miki Nazeefa tataya ki hira tunda Ni fita zanyi”.
Saleema dai batace komi ba har Mom ɗin tafice.
Nazeefa tana kwance akan gadon ta duk abin duniya yabi ya ishe ta, tun sanda aka soma hayaniyan zuwan Amarya tana jin su amma takasa fita, sosai take jin baƙin ciki da kishi aranta sai dai tadage tana ta ƙoƙarin hana kanta kuka, shigowar Mom cikin ɗakin yasa tatashi tana ma Mom ɗin sannu