Uncategorized

BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

Washe gari.

Meena tunda safe bayan ta idar da sallah tanufi kitchn dan tasamu abinda tad’aura, mgnr Balkisu ce tafad’o aran Meena lkcin da aka kawota inda Balkisu ke sanar da ita abunda Hafeez yafiso yayi brkfst dashi wato soyayyan kwai da tea, dariyar mugunta Meena tayi, nan tashiga farfasa kwai wnda xatayi amfani dashi ta jajjaga tarugu mai yawa ta yanka albasanta tazuba maggi da kayan kamshi ta zuba cikin kwan ta bubbugashi sosai yabi jikinsa, nan tahau suyan kwan, daga gefe kuma tad’aura ruwan zafin tea dinsa Wanda tazuba lipton da citta suga da kalinfari da barkono sosai, ae fa nan qamshi ya karad’e gdan.

Hafeez sai da ya tabbatar da cewa yayi wanka sannan ya shirya tsaf abinsa cikin shaddarsa sky blue sai hularsa wadda tayi matchn da kayansa, agogon hannunsa yad’auka yasa sannan yafesa turare yanufi hanyar fita, bud’e kofan nan da Hafeez zaiyi yaji kamshin ya doki hancinsa da sauri yaqarasa cikin falon ko da yaduba dinning area yaga anshirya komai tsaf tsaf kmr yadda aka saba, cikin hanzari yanufi dinning table yaxauna tare da duban agogon hannunsa qarfe takwas da rabi yana ganin haka yayi saurin zaro wayanshi dake aljihunsa, wata nmbr yayi dialing cikin natsuwa yake mgn yace “yes mansur am on ma way just giv me 15 to 20 mint a will b thr soon” yana gama wayar ya hau bud’e brkfst din ruwan zafin tea din yafara zubawa kadan cikin cup sannan yadibi kwan nashi cikin plat, wani irin kamshi mai dad’i ne yake ta doke hancinsa.

Sai da ya tabbatar da ruwan xafin yad’an huce dai dai yadda zai iya sha sannan yajawo kusa dashi, plat din kwansa yasa agaba dasauri yadebo mai yawa yaddana a bakinsa yafaraci a hnkli yad’an lumshe ido sai da kwan yakai qarshe Hafeez yaji wani irin azababben zafin barkono ya ziyarci harshensa dasauri yafurzar ya dauki cup din tea dinsa ya kurba ko zaiji d’an ji dama, ae fa nan Hafeez ya miqe tsaye idanunsa sukayi jajir harshensa yadinga fiddowa waje sbd tsabar azaban da yakeji ko mgn yakasa(kasancewar Hafeez bayason abuda yaji SBD ulcer)

Meena dake la6e tana kallonsa sai kwasar dariya take abunta, kara leqawa tayi don taga yadda yake daka tsalle ae kuwa tana sa kai sukayi ido biyu da Hafeez.

NWA

[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:10AM, 8/4/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

     âœ¨BURIN HAFEEZ✨

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.

Episode3⃣3⃣

Hafeez nahad’a ido da Meena yatabbatarwa kansa cewa itace tahad’a masa wannan muguntan, dan haka a fusace yayi kanta sai dai Hafeez baisamu daman qarasawa gareta ba sbd wani irin abu da yatsaya a zuciyansa nan da nan yanemi hnklinsa yarasa jagwaaf yafad’i qasa gamida riqe kirjinsa yanata mutsu-mutsu a kasa. Abu dai kmr wasa wasa tun Meena na yar dariyarta har dai talura cewa Hafeez da gaske yake, ae da gudu Meena taqarasa inda yake kwnce nan tashiga jijjigasa tana kiran sunansa.

      Gabad’aya idanunsa suncanja kala Hafeez yajigata sosai zuciyarsa wani irin suya take masa.

Meena ta lura abin nashi dagaske ne ba wasa dan haka dagudu tashiga kiran Daniel, Daniel yazo da hanzari ganin ogan nasa cikin wani hali hakan yasa yafahimci cewa ulcer dinshi ne yatashi dagudu Daniel yashiga d’akin Hafeez yad’auko maganinsa nan ya qoqarta yasamu yabashi maganin yasha.

A hnkli Daniel yasamu yad’aga Hafeeez dakyar yataimaka mishi ya kaisa d’akinshi. Hafeez jiyayi tsanar Meena taqaru a xuciyarsa.

A bangaran Meena kuwa jitayi gabad’aya jikinta yayi sanyi, sai ynxu takejin kwata kwata bata kyauta ba nadama tashigayi marar iyaka.

Tunda wannan abu yafaru kuwa Hafeez bai qara bin tankan Meena ba, yar kulatan ma dayakeyi suna rigima kwata kwata ynxu ya daina.

      Mgnr abincinsa kuwa Daniel kedafa mishi kmr kullum.

• • • • • •

Meena abin duniya dukk ya isheta Hafeez ko kallon indatake baya son yi jiyayi gabad’aya yatsaneta, shiyasa da zarar gari yawaye yake Allah Allah yafice a gdan.

Yayin da ita kuma Meena ke tunanin hanyoyin da zatabi dan taga cewa ta kyautata masa, Hanyar farko da Meena tafarabi shine da zarar Hafeez yafita zuwa office dinshi a wannan lkcin ne take shiga d’akinsa ta gyara ko ina ta wanke toilet tattara under wears dinsa ta wanke masa, haka kullum Hafeez idan yadawo sai yaga komai Na d’akinsa very neat.

Ana cikin hakane Daniel ya samu Hafeez yasanar dashi cewa yanaso zai zaije enugu can garinsu domin gudanar da bikin kirisimeti, Hafeez yayi mishi izini sannan yad’auki kudi mai tsoka yabawa Daniel.

Lkcin da Daniel zaitafi garinsu har qofan d’akin Meena yaje yayi sallama da ita, nan itama tayi mishi fatan adawo lafiya.

*DA YAMMACI*

A yammacin ranar ne Meena tashiga kitchen tad’aura tuwon semo da miyan d’anya ku6ewa, Meena taxage sosai tadafa abinci mai kyau da tsari dukk dan taburge Hafeez.

     Bayan Meena tagama girkinta ne takoma d’akinta toilet tashiga ta silla wankanta sannan tafito tashirya tsaf abunta cikin wata jar atamfarta mairatsin ash kala, atamfar taimata kyau sosai, simple mark up tayi sannan tanufi falo taxauna ta kunna Tv.

Horn din motar Hafeez Meena taji, dasauri tamiqe taleqa window’ Hafeez din ne kuwa ta hango yayinda yake qoqarin fitowa a mota, dasauri takoma maxauninta.

Murd’a kofan falon yayi yashiga batare da ya lura cewa akwai mutun a falon ba, dasauri Meena ta taso da fara’arta tayi mishi sannu da zuwa batare da Hafeez ya kulata ba tasa hannu tana qoqarin ansar briefcase dinsa, wani irin takaici Hafeez yaji baisan lkcin daya tunkud’e ta ba tafad’i. Hafeez ko ajikinsa haka yatsallaka Meena yawuce.

Dinning area yamaida dubansa yaga cewa tahad’a masa abincin dare tsaki yaja mtssssww stupid, Hafeez nafadin Haka yanufi d’akinsa.

Jikin Meena yayi sanyi sosai a hnkli ta tashi a wurin tashiga d’akinta, saman gadonta tahau tarafka wani uban tagumi nan tashiga yin tunani kala kala akan yadda zatabi da hafeez nan dai tayanke shawaran zata jure komai dan ganin tacikawa Balkisu alqawarinta kmr yadda tacikamata nata.

Magri nayi Hafeez ya d’aura alwalarsa yawucewarsa masallaci, bayan sun idar da sallah restaurant yanufa kai tsaye yacika tumbinsa, dukk da cewa yasan Meena tayi girki amma Sam baijin iyacin girkinta koda wasa. 

__•__•__•__°__°__°__•__•__•

A kullum Meena tana qoqari sosai wajan kula da Hafeez, ta gyara mishi d’aki tasa roomfrshnr ta wanke toilet dinsa tagyara mishi kayansa, sannan tayi mishi girki kullum dukk da cewa Hafeez bayaci amma Meena dai dai da rana d’aya bata fasa abubuwan da takeyi ba, tsawa da gyara turi da masifar Hafeez baya hana Meena ta kyautata masa.

Meena ce zaune a falo tanajiran shigowar Hafeez, sai jin tayi telephone Na qara (wato landline wnda kowa xai iya d’auka, kasancewar Meena batada waya) dasauri Meena tamiqe ta isa wurin da telephn din ke ajiye tad’aga wayan kmr yadda taga Hafeez nayi, sallama tafarayi sannan suka gaisa 

      Take anan Meena tagane muryan Balkisu ne nidai naga Meena sai murmushi takeyi daga bisani kuma naji tace mekikace daqarfi!! ?? Gabadaya naga hankli Meena yatashi dasauri tajefar da wayan tanufi d’akinta.

®NWA

[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:47AM, 8/4/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button