BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣4⃣
A rikice naga Meena tafito daga d’akinta sanye da hijab dasauri naga taja kofan d’akin ta rufe sannan tanufi hanyar waje a hanzarce, bakin titi tanufa kai tsaye da alamar tana jiran abin hawane.
Kmr wucewan minti biyar Meena na nan tsaye bata samu abin hawa ba, sai ga Balkisu nan cikin motarta tun kafinma taqarasa tagane cewa Meena ce tsaye bakin titi.
Dasauri Balkisu tayi parkn din motarta kusa da Meena, zuge glass din motar tayi lkcin ne Meena tafahimci cewa Balkisu ce, ae kuwa da hanzarinta taqarasa cikin motar.
Bayan tashiga cikine Balkisu tafashe da yar dariya tace “a’a Anty amarya inazaki haka badai kice mgnr da mukayi bane dukk tafirgitaki haka ba?” Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar zuciya tace “haba Balkisu mai xai hana hanklina baxai tashi ba karki manta fa cewa basan garinsu mahaifiyata ba ynxu idan ta tafi tabarni batare da nabita naga dangina ba mai kike tunanin xaifaru? Gsky nidai xanbi Amma na xuwa garinsu, Balkisu tadubi Meena da murmushin nan nata tadafa kafad’arta tace “haba kekuwa Anty amarya ae baki bari naqarasa miki abinda nake son cewa ba kawai naga kinkatse call din shiyasa kikaga nafito a hanzarce”.
Ynxu koh da ace bin Baba Rabin zakiyi hakanan zakitafi batare da izinin yayana ba ko kuwa hakanan zakije hannu siddan babu kayan sawa balle tsaraba?
Meena ta sadda kanta qasa tace “wlh dukk na rikice ne sbd bana fatan abinda xaisa nasakeyin nisa da mahaifiyata” Balkisu tace “hakane amma ae ba yau bane tafiyan nata sai jibi ne fa Dan haka muje namaidaki gda ki kwantar da hnklinki zanfad’awa Yaya mgnr tafiyan naku amma inaso kema kisameshi dakanki kifad’a masa, toh kawai Meena tace.
Hakanan Balkisu ta mai da Meena gda sai faman zolayanta takeyi.
** ** **
Hafeez ne zaune awani tafkeken Restaurant yana cin abincinsa hnkli kwance, daga gefe kuma inda ya ajiye wayansa tashiga ruri! A hnkli Hafeez yajawo wayan ‘luvly Sister’ sunan da Hafeez yayi saving nmbn Balkisu shine ya baiyanna agaban screen din wayansa da sauri yad’auka gamida sawa a kunnenshi, bayan sun gaisa ne Balkisu ke sanar da Hafeez mgnr tafiyan Meena wnda zasu ita da mahaifiyarta, Hafeez yace “olryt Allah yakaimu lkcin” Balkisu tace ameen nan suka d’an ta6a hiransu daga bisani kowannensu ya ajiye waya.
Abangaran Hafeez kam shiru yayi hakanan kuma sai yakejin kmr babu dadi, can dai kuma ya hori xuciyarsa tama daina damuwa da wannan yar qauyan ae ma inta tafi kahuta, inba ma tsabar rainin wayo ba Balkisu nake aure ko ita ae kamata yayi taxo da kanta taneme ixinina wato tanaji ita watace tafi qarfin takawo kanta knan?, hakanan Hafeez yayi tasaqawa da kuncewa a cikin xuciyarsa. Har dai yagama cin abincinsa sannan yanufi gda.
Yau ma kmr kullum Meena tayi masa abinci ta ajiye dukk da tasan cewa baci xaiyi ba, haka nan bayan shigowarsa cikin gda har bakin kofa tabisa dan ta tarbeshi amma gayen nata ko kallon inda take baiyi ba, balle yanxu dama cike yake da haushinta akan qin xuwa da batayi da kanta tafara tambayarshi ba.
Inda sabo kam Meena tasaba da irin abubuwan da Hafeez ke mata wanda zuwa ynxu kam har sun fara daina damuwarta.
Misalin qarfe tara na dare Meena tashiga bayi tayi wnka sannan tad’airo alwala, kayan bacci tasaka masu sauqin nauyi hakanan tajawo xani tad’aura saman sleepn drss din sannan tasanya hijabinta ta gabatar da nafilfilunta kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne ta yankewa xuciyarta shawaran cewa gwnda taje a daidai wannan lkcin tasanar da Hafeez mgnr tafiyanta inba haka ba da safe koh da zata tashi olrdy ya fita.
Hakanan ta gama yanke shawaran ta, ta amincewa zuciyarta, Dan haka d’akin Hafeez tanufa kai tsaye a hnkli tashiga knckn kofar,…sai da Hafeez yagama jan ajinsa kasancewar yasan babu wnda xai kwankwasa mishi kofa adaidai wannan lkcin sai Meena shiyasa sai dayagama jan ajinsa sannan yace yes come in! A hnkli Meena ta murd’a kofan d’akinta shiga.
Hafeez tagani zaune bakin gado dagashi sai farar vest da boxsas yanata aiki da system inshi, da sallama tashiga cikin d’akin, Hafeez ya amsa mata sallamarta batare da yad’ago ya kalleta ba.
Meena taduqa har qasa ta gaida Hafeez,..Hafeez kuwa ko kallo bata ishesa ba amaimakon ma ya amsa gaisuwansa datayi sai cemata yayi yes inajinki fad’i abunda yakawoki kinga aiki nakeyi.
Meena ta had’iye wani yawu dakyar yawuce sannan ta sadda kanta qasa sbd jitayi gabad’aya Hafeez yayi mata wani irin kwarjini, cikin nutsuwa Meena tace “dama Amma nane xatayi tafiya xuwa gda shine nake so na bita” Hafeez yace “dakyau yar qauye xa’aje qauye kenan? Meena dai batace masa komai ba sai wasa kawai take da d’an yatsanta.
Wani murmushin takaici Hafeez yayi sannan ya d’auko wata waya LG yamiqa mata yace ga waya nan inkinje kiyi amfani da ita, Meena ta amsa tayi godiya sannan Hafeez yad’auko bandir din kudi yan dari biyar biyar ya watsawa Meena cike da gadara yace gashinan wannan akaiwa tsohuwa nasan zata buqata.
Mgnr Hafeez ta matuqar 6ataran Meena amma sai ta danne xuciyarta miqewa tayi cike da d’acin rai takalli Hafeez ta kalli kud’in har dai Meena tayi niyar sakar mishi mgn sai kuma nan da nan ta taushi zuciyarta, ajiye masa kudinsa tayi a qasa dai dai qarfarshi taficewarta a d’akin.
Binta Hafeez yayi da kallo cike da mamakinta
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:27AM, 8/5/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣5⃣
Balkisu da kanta taje wani babban super market tahad’owa Baba Rabi tsaraba masu kyau na amfani, su sabulun wnka wanki turaren shafawa kwalayen biskuit da dai sauransu, hakanan ta kwasa tayi gdan Baba Rabi dasu ta kai mata. Baba Rabi tayi farinciki sosai da irin yawan hidimar da Balkisu keyi da ita, nan tayi tasawa Balkisu albarka gami da nuna farincikinta.
Washe Gari.
Tunda asuban fari bayan Meena ta idar da sallah batasamu ta kwanta ba sai da ta tabbatar da cewa tayi dukkan wani aikinta kmr yadda tasaba, agogon dake liqe jikin bangon d’akinta ne yabuga qarfe 6:30 a gaggauce Meena tafad’a toilet tayi wanka kasancewar tasa qarfe 7:00 Hafeez ke fita, gashi yau tanason tawuni gdnsu dan tasan irin shirye shiryen da yakamata suyi ita da Ammanta.
Wata dakakiyar shadda lemon green wadda akayiwa aiki dazare orange, riga da siket ne su Meena tad’auko tasa (woww ni kaina munay sai dana yaba wannan shiga) dukk da ba wata kwalliya Meena tayi sosai ba amma tai matuqar kyau, nan tad’auko takalmi orange gyale orange.
Motsin Hafeez taji yana qoqarin fitowa daga d’akinsa dasauri taduba agogo taga 6:57 a hanzarce ta zura wata qatuwar Hijabi tanufi waje.
Ki6iss sukayi da juna Hafeez ke kokarin fita yayin da Meena tafito a d’akinta dasauri tace Yaya!!
Mamakine qarara ya baiyanna a fuskar Hafeez jin cewa Meena ke kiransa da Yaya dukk da cewa bata fiye kiran sunansa ba, sannan a iyazatonsa yana tunanin tayi fushi da shi sbd abinda yayi mata jiya daddare.