Uncategorized

BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

Tsayawa Hafeez yayi batare da ya juyo ba, a hnkli Meena taqarasa kusa dashi tace “ina kwana” Hafeez ya amsa a takaice Lfy, Batare da nuna damuwa ba Meena tace “Dan Allah sonake kamin izini xanje gdnmu nawuni acan sannan inba damuwa inaso ka ajiyeni a gda.

       Hafeez har yayi niyyar cewa wani abu sai kuma yafasa, juyowa yayi yakalleta sama da wasa sannnan yace olryt nabaki nan da minti d’aya inbaki shirya ba xan wucewata.

Ae Hafeez nacewa haka dasauri Meena ta miqe kafinma Hafeez yabar falon tuni tashige d’akinta hijabin dake sanye jikinta tacire tasanya gyalenta sai takalminta da tasa tad’auki wayarta a gaggauce tarufe d’akinta da kofar falo, kasancewar ita da Hafeez kowa nada nashi mukullin.

Hafeez ne zaune cikin motarsa yana jiran fitowan Meena, hango ta yayi tafe sanye da gyale dasauri Hafeez yasake kallonta dakyau wani irin abu yaji ya d’arsu a zuciyarsa wanda shi kansa baisan miye ba wani irin kishi yaji domin kuwa ko da ace maqiyin Meena ne yaganta to tabbas dole ya yaba mata sbd tayi masifar kyau, cikin zuciyar Hafeez yace “lallai yarinyan nan ta rainamin hnkli ba ynxu naganta sanye da hijabi ba? Wato dan zata fita shine hadda wani sa gyale.

      Hafeez naganin Meena taqaraso ya watsa mata wata uwar harara, wanda hakan yasa Meena tasha jinin jikinta, a qufule Hafeez yace kee wato baki shirya fita zuwa anguwan ba shine kikayi westin tym dina?

Meena tadubi kanta sama da qasa sannan tasake duban Hafeez tace “wlh yaya na shirya” Hafeez yadaure fuska yace kina nufin da gyalen nan zaki fita? Meena tafahimci abinda Hafeez yakeson cewa wato bai da tsarin son iyalinsa su sa gyale, dasauri Meena ta koma cikin gda tasanyo hijabi dukk da cewa hijabin sam baiyi matchn dakayan jikinta ba hakanan tasanya abinta domin ita dai buqatarta kawai ta jita ajikin Ammanta.

Gdan baya Meena ke qoqarin bud’ewa dasauri Hafeez yace ke yar qauye wakike ajiye drivanki look inbaki shirya tafiyan ba nixan wucewata ko ancemiki banda abubuwan yine, jiki a sanyaye Meena tabude gdan gaba taxauna Hafeez yaja motan sukafice a gdan.

Sanin datayi Hafeez baisan gdnsu ba shiyasa tadubeshi cikin sanyin muryanta tace “famfamari zamuje wurin masallacin juma’a, ko uffan Hafeez bai ce mata ba hakanan yaja motarsa yanufi anguwan da tafad’a mishi.

      Sunxo dai dai kofan gdan ne Meena tace sun iso tsayawa yayi a hnkli daga gefen hanya, Meena tasa hannu zata bud’e kofan Hafeez yace “ke tsaya yar kauye karki 6allamin murfin mota, zura hannunsa Hafeez yayi yabud’e mata kofan sannan yace, nabaki nan da awa biyar kikoma gda kinji abinda nace?”

 Ran Meena ya6aci sosai amma talura Hafeex neman rigima yakeyi shiyasa kawai ta gyada masa kanta tafice a motar.

Meena taji dadin kasancewa da Ammanta sosai wnda har hakan yasa tashagala tamance da umarnin Hafeez.

Qarfe 2 dai dai Hafeez yakoma gda amma still Meena bata dawo ba, wani irin haushi Hafeez yaji ganin cewa yadawo gda babu Wanda ta tarbeshi dukk da cewa baya kulata amma yau din sai yaji babu dadi.

Wani irin tunani ne yazowa Hafeez lkci d’aya wanda yad’imautashi, dasauri ya zari car key dinshi yafice a gdan, gdansu Meena yanufa kai tsaye sbd tunawan dayayi cewa matuqar Meena tace zata koma gda tofa motan haya xata hau, tunanin Hakan ne yasa ya gaggauta zuwa yad’auko ta da kansa.

Hafeez na danna kan motarsa cikin kwanar gdansu Meena nan ya hango abinda yad’aga masa hankali.

®NWA

[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:23AM, 8/5/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

     âœ¨BURIN HAFEEZ✨

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.

Episode3⃣6⃣

Hafeez Meena ya hango tsaye a kofar gdansu ta tsaida mai adai-daita sai faman murmushi takeyi mishi yayin da suke mgn ita da mai adaidaitan, wani irin kishi Hafeez yaji, nan fa jikinsa yafara kyarma a guje yashiga cikin layin ko gabansa ba ya iya gani mai kyau, Hafeez na pake motanshi kafinma yakasheta a hanzarce yabude murfin motan yafita batare da ya kashe motan ba.

Gadan gadan Hafeez ya nufi kan mai adai daita, mai adai daita na cikin tsaka da ciniki da Meena sai ji kawai yayi anshaqo wuyansa ta baya ana dukansa ta ko ina.

       Dasauri Meena tafasa ihuu! Tana roqon Hafeez da yabar abinda yake yi, Hafeez kam kojin ta bayayi gabad’aya jiyake kmr ya kashe mai adai daitan sbd haushi,. ihuun da Meena takeyi ne yajawo hnklin mazan anguwar dakyar suka samu suka kwaci mai adai daita a hannun Hafeez.

Idanun Hafeez gabad’aya sun rine sunkoma ja sbd tsananin kishi, a tsorace Meena tafara ja dabaya sbd gabad’aya Hafeez tsoro yabata sai wani irin huci yakeyi tamkar zaki cikin dawa, gawata uwar harara dayake jeho mata.

     Da gudu tashiga gdansu dai dai lkcin ne Baba Rabi takejiyo hayaniya daga waje dole tamiqe tanufi hnyar waje don ganin mekefaruwa, Meena ce tashigo gdan da gudunta sai faman waiwayen bayanta takeyi.

Hafeez kam mutanen cikin anguwar sai tambayanshi sukeyi mai wannan bawan Allah yamasa? Kota Kansu Hafeez bai biba yanufi motarshi ya kasheta yarufe sannan yanufi cikin gdansu Meena din.

     Meena rungume Amma tayi dukk tsoro yacikata sai wani faman haki takeyi kmr wacce tayi gudun 3kilomita, Baba Rabi sai faman tambayarta takeyi Aminatu lpy kuwa meyaparu waye ya biyoki? Meena kasa mgn tayi sai faman kallon hanyar shigowa gdan takeyi a tsorace “domin atunani Meena hadda ita Hafeez zai hada”

Hafeez ne yashigo gdan sallamarsa, Baba Rabi ta amsa mishi sallaman yayin da ta kura mishi ido tanajiran yafad’i da wacce yazo domin atunanin Baba Rabi shine Wanda ya biyo Meena,(domin kuwa Baba Rabi ko a hoto bata ta6a ganin Hafeez ba) Hafeez har qasa yaduqa ya gaishe da Baba Rabi, Baba Rabi ta amsa “lafiya kalaw” Lkcin ne Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar xuciya sannan tace “Amma wannan shine Hafeez yayan Balkisu” Baba Rabi ta fad’ad’a murmushinta sosai tace “Allah sarki kayi Hkri Sam ban shaida ka ba, nan tayi mishi iso ixuwa cikin gdan, A falo Hafeez yazauna Baba Rabi da kanta takawo mishi abinci tuwon semo da miyar allayahu zallah, drinks takawo mishi da ruwan sanyi.

Baba Rabi da Meena kitchn suka koma suka fara had’awa Hafeez juice din kwakwa, Hafeez kam yunwa yakeji sosai dan haka bude kulan yashigayi tuwon semo yagani anyi malmalanshi ansa leda tsaf sai kuma miyan allayahu wnda taji manja, malmala d’aya Hafeez yad’iba yasa a plat bayan yazuba miyan allayahun nan fa yahauci, kafin Hafeez ya ankare tuni yagama da malmala guda”woww vry nyc Hafeez kawai ke fad’i yana lasan baki😋”

Meena ce tashigo Hannunta d’auke da jug din juice din kwakwan, duqawa tayi tad’auki glass cup a kusa dashi batare da ta kalleshi ba tashiga zuba mishi.

       Kura mata idanu Hafeez yashigayi kmr yajawota kusa dashi haka yakeji, Meena nagama zuba mishi juice din ta tashi tabar falon a hanzarce.

Hafeez jiyayi kmr baxai iya tashi awajan ba sbd wani irin qoshi dayayi, rabonsa da cin abinci kmr haka har yamanta, murmushi kawai Hafeez keyi shi kad’ai yasan abinda yasashi murmushin.

      Meena ce tashigo cikin falon wannan karon ba Hijabi, filas din da Hafeez yagamacin abinci dasu shine Meena tashigo danta kwashesu, Hafeez kam sai binta yake da kallo tamkar wata baquwa, Hafeez kam sai mamakin knsa yakeyi yadda ya lura cewa Meena naqoqarin zautar dashi lkci d’aya mamakin kansa yashigayi sosai wnda har Hafeez yakama tantamar anya kuwa shine? (LOL)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button