BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣8⃣
Wurin Motarsa kai tsaye Hafeez yanufa yayin da Meena tarufa masa baya, bud’e motan yayi ya xauna batare da ya rufe ba, hakan ne yabawa Meena dama bud’e daya site din itama tazauna.
Wata irin nannauyar ajiyan zuciya Hafeez yayi sannan yamaida dubansa ga Meena yace “idan kukayi tafiyan sai yaushe zaku dawo? Meena wacce ke wasa da gefen hijabinta kai duqe tace naji Amma nacewa sati d’aya xamuyi mudawo, dammm! Gaban Hafeez yafad’i amma sai yayi saurin dakewa yace olryt” shiru sukayi gabad’ansu na d’an wani lkci, can dai Hafeez yace “amm Balkisu takirani ta sanar dani cewa drivan Dr Muh’d ne xaikiku can Gwazan ko? Meena tace eh shine..
Ciro kudi Hafeez yayi sannan yamiqawa Meena yace gashinan susha mai a hanya, kar6a tayi sannan tayi mishi godiya, Hafeez ya maida kallonsa ixuwa wani gefe batare da yakalli Meena ba yace “i hope kinji gargad’in danayi miki cewa banda sa gyale ” Meena tace insha allahu zankiyaye hakan.
Murmushin jindadi Hafeez yayi yace “vry gud of u”Meena dai batace komai ba. A dan gaggauce Hafeez yace ni xanwuce kada nayi latti Allah tsare hanya, Hafeez sai tsintar knsa yayi dacewa “ki kula da kanki Meena”
Insha allahu shine abinda Meena tafad’a sannan tafice a motan, sai da Hafeez ya 6acewa ganinta sannan tashiga gda.
Hafeez na isa cikin falo gabad’aya sai yaji dukk gdan yamasa fili babu Meena ba Balkisu, wata irin kewa ce tadinga shigarsa Wanda hakan yasa Hafeez yanufi dinning area yaxauna kawai sai tsintar kansa yayi yanacin abinda Meena ta girka masa
Hakanan Hafeez yagama cin ferfesunsa sannan yazuba kunun gyad’a yafara sha yana lumeshi idanu, cikin ransa sai tunani yakeyi haka dama Meena ta iya girki bansani ba Oh my God!! Hafeeez yabud’e cikinsa sosai yakwashi girki.
Bayan ya kammalane yanufi d’akinsa domin ya shirya zuwa office.
** ** **
Balkisu da kanta ta tura Habu driva yad’aukisu Meena, hakanan suka kama hanya, cikin ikon Allah sun samu isa garin gwaza lafiya.
Yan’uwa da abokan arziqi kowa yayi farin cikin ganin Baba Rabi, haka nan su Baba Rabi sun sami tarbo mai kyau awajan yan’uwansu (kasancewar iyayen Baba Rabi sunjima da rasu, a hannun kawunta ta taso) Khadija yar gdan kawu Usman tun zuwan Meena gdan nan Allah ya had’a jininsu khadija tayi farin ciki sosai da xuwan Meena(kawu Usman shine kawun Baba Rabi) yaransa guda biyar mata hudu daga ciki dukk sunyi aure sai khadija auta.
Meena ma tajidadin kasancewa da Khadija sosai, gashi sunkasance sa’anin juna, khadija tabawa Meena wata hud’u shiyasa inkagansu atare tamkar wasu twns,
Tun zuwansu gwaza Meena kullum tana tare da khadija tana d’aukan lesson domin kuwa khadija akwai wayo da son gayu shiyasa kullum Meena na tare da ita tana koyan wasu abubuwan.
Abangaran Hafeez kuwa fushi yake da Meena wanda ita batasan ma yanayi ba,..fushi yakeyi sbd Meena bata kirashi tasanar dashi sun Isa lafiya ba, sai abakin Balkisu yakeji. Kullum Hafeez wayanshi na kusa dashi yana jiran call daga Meena amma shiru kakeji, da xarar Hafeez ji kira yashigo wayansa da hanzari xai jawota yaduba a tunaninsa Meena ce takira, Hafeez nason kiran Meena a koda yaushe amma girman kai yahanashi aikata komai.
*Bayan Sati Daya*
Dakyar Hafeez yaga wucewan sati dayan nan domin kuwa jinsu yake tamkar shekara d’aya wani irin farin ciki Hafeez yake ji idan ya tuna cewa Meena yau zata dawo kmr yadda tafad’a mishi, hakanan Hafeez yatsinci kansa da fita waje yana sadaka sbd farinciki.
A gajiye Hafeez yakoma gda falo ya kwanta domin yahuta, baifi wucewan minti biyu ba yafarajin bacci na fisgarsa, kmr daga sama yaji wayansa Na ringing da farko har ya share har ta tsinke baid’aga ba sai da aka sake kira a karo na biyu sannan yasa hannunsa ya lalubo wayar d’aukan kiran kawai yayi batare da yaduba sunanan ba.
Cikin muryan bacci yace “hello” a bangaran Meena tace Assalamu alaikum, lkci d’aya Hafeez ya fahimci mai mgn firgigit ya miqe ya xauna dasauri Hafeez yace Meena kece?
Meena tace eh Yaya nice dama nabugo insanar maka cewa akwai wani biki da zamuyi anan bazan samu damar zuwa yau ba inaso zanqara wani satin sbd in…..kafin Meena taqarasa abinda take son fad’i tuni Hafeez ya katse wayan.
Wani irin numfashi Hafeez keyi cike da tashin hnkli sbd tsabar takaici baisan lkcin da yayi wurgi da wayansa ba yace “ohhh no Meena baki Isa ba I cnt tollrt it any more idan baxaki iya dawowa da kanki ba nizanje nadawo dake, tsawan wannan satin dakikayi bakisan halin damuwar dakikabar ni aciki ba, am vry eager to c ur cute face Meena.
Hafeez nafad’in haka yanufi d’akinsa da sauri car keys dinsa ya Zara yadawo yadauki wayansa afalo ya fice a gdan.
Hafeez na kan hanya yakira Dr Muh’d yace yanaso Dan Allah yabashi aron Habu driva zai rakashi izuwa wani waje, Dr Muh’d yace okay Abokina ba damuwa.
Asibitinsu Dr Muh’d Hafeez yanufa yad’auki Habu driva yace dashi yanaso yarakashi garin da yakaisu Meena a yau din nan. Cike da bin umarninsa Habu driva ya harba motansa izuwa garin gwaza.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:54AM, 8/7/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣9⃣
Kasancewar Habu driva yasan gdan kawu Usman hakan yasa suka nufi gdan kai tsaye.
Meena ce zaune tsakar gda ita kadai ta rafka uban tagumi tunani ne sosai aranta addua kawai takeyi kar Allah yasa Yaya Hafeez yace baxa tasamu daman tsayawa bikin nan ba,
Meena tayi nisa sosai cikin tunaninta sai jiyayi andafata a hnkli tadago kanta, Khadija tagani tsaye, ae kuwa bashiri tasakar mata murmushi, cike da kulawa Khadija ta duqa daf da Meena tace sister anya lpy kuwa? Wani murmushin yaqe Meena tasakeyi sannan tadubi Khadija tace “sister lpy Lou mekika gani?” Khadija tace a’a naga kinxauna ke kadai kin zuba uban tagumi ko dai kina tunanin Shine? Dasauri Meena tace haba dai khadija wlh ba haka bane kawai nadamune sbd inason natsaya bikin Hamza (hamza qanin Kawu usman ne) Khadija tayi murmushi sannan tadafa kafadan Meena tace “kema bnda abinki banace ki kira mijin naki kisanar masa cewa kina son yabaki damar qara wasu kwanakin ba?.
Meena tashare kwallar dake qoqarin zubo mata tace “wlh sister na jarabba hakan hasalima dana fadamishi bai ce dani qala ba kawai yakashe wayansa.
Khadija tace ohhh wlh kina damuwa da abinda baikamata ace kindamu ba, kikasani ko ntwrk ne ko rashin caji kibari anjima kisake tryn. Murmushin yaqe Meena tayi tace oky.
Khadija tace yauwa kokefa, nan taja hannunta tace tashi ma muje kasuwa daxu Baba yabamu kudin sayen anko yakumacemin haddake dan haka kisaki ranki kitashi mutafi.
Jiki ba kwari hakanan Meena ta tashi tashirya suka tafi kasuwa.
Su Meena ko minti uku basuyi da tafiya kasuwan ba sai gasu Hafeez sun kunno kai cikin anguwar.
Dai dai kofar gdan Habu yayi parkn, kafinma yace da Hafeez wani Abu tuni Hafeez din yafahimci cewa nan ne gdan.
Fitowa sukayi daga cikin motan sannan suka sami yaran dake wasa kofan gdan suka aiki daya daga cikinsu akan yaje yace wai ana sallama da Meena