Uncategorized

BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

 Yaron kuwa dagudu yashiga cikin gdan kmr yadda aka umarce shi, yana zuwa yace “wai inji wani mutumi awaje yace ana sallama da Meena”

Amma nadaga cikin d’aki tajiyo muryan yaron da sauri tafito waje tace da yaron “waye ke sallama da Meena?” Yaro yace shima baisani ba, Baba Rabi tace da yaron yatsaya nan tashiga ciki tad’auko hijabi tace da yaron suje tagani.

Koda fitar Baba Rabi izuwa waje Hafeez tagani tsaye jingine da mota, dasauri taqara wajansu tana musu sannu da zuwa, Hafeez kam sai waige waige yakeyi inda xai hango Meena.

Baba Rabi tace “sannunku da zuwa Hafeez kai ne tafe? Hafeez yayi murmushin yake yace wlh kuwa Baba nine, Baba Rabi tace toh sannunku da zuwa kushigo daga ciki.

Dakin Kawu Usman Baba Rabi tasauqe su Hafeez, bayan sunqara gaisawane baba Rabi takawo musu ruwan sha.

     Sannan tace da Hafeez yad’an jira kadan Meena sunfita ita da yar’uwarta, shiru Hafeez kawai yayi, tunanin inda Meena taje a wannan yammacin kawai yakeyi.

Abangaran Meena kuwa suna can kasuwa wajen siyan anko, bayan sungama ne Meena tace sister inaso kikaini inda ake siyan gyale da hijabi, haka nan Khadija takaita gurin da tabuqata, Meena tasaima kanta hijab kallan ankon nasi sannan tasaima Khadija Gyale itama kallan ankonsu.

     Haka nan suka gama siyayyansu cike da farinciki suka koma gda.

Mai taxi na ajiye su Meena fitowan nan da zatayi idanuwanta sukayi tozali da motar Hafeez, rass!! Gabanta yafad’i, amma sai tadake domin tana tantama kmr ba motansa bace, hakanan suka kwashi kayansu suka nufi cikin gda.

®NWA

[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:57AM, 8/7/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

     âœ¨BURIN HAFEEZ✨

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.

Episode4⃣0⃣

Suna shiga cikin gdan da sallamarsu kafin sunemi waje suzauna Baba Rabi tace “kee! Aminatu daga xuwa kasuwa kuje kudawo shknan sai kumaida gari naku kuje kuyi xamanku, Meena tace Amma wlh ba haka bane mund’an tsaya siyan wasu abinne shiyasa mukadan jima.

Baba Rabi tace toh ae kunkyauta sai kitashi kije d’ankin Kawu Usman kinyi baqo, dasauri Meena takalli Baba Rabi tace “Amma baqo kuma”? Baba Rabi eh kawai tacemata tabar wajan.

     Khadija tadubi Meena tace sister tashi kije natabbata babu wani namijin daxaixo yanemiki har ayimishi izinin zuwa d’akin Kawu face mijinki, plss tashi ki kintsa kijeki.

Kafin Meena tace wani Abu Khadija taja hannun Meena izuwa d’akinsu, nan ta tsara mata kwalliya mai kyan gaske Khadija da kanta tabud’e akwatin Meena taza6o mata wasu riga da siket masu kyau tace tasasu. Batare da Meena ta musawa Khadija ba hakanan tadauki kayan tasa, sai da tashirya tsaf sannan tasanya hijab tanufi d’akin kawu usman.

Qamshin turaren Meena ne yadoki hancin Hafeez, dasauri yad’ago kansa Meena yagani tana qoqarin xama bisa kujerar da yake zaune.

Meena wacce gabanta yatsananta Faduwa cikin siririyar muryanta tace sannu da zuwa Yaya ina wuni? Hafeez ya kura mata idanu ko qiftasu bayayi, shiru yayi tamkar baxaice komai ba , can dai yace Meena ba wannan ne yakawoni ba “Habu driba kam tun shigowar Meena yabar d’akin” Meena tayi shiru tana sauraren Hafeez taji da wacce yaxo.

Hafeez ya matso daf da Meena yace zuwa nayi domin inaso kimai maitamin abinda kikace lkcin da kika kirani awaya d’axu.

     Shiru Meena tayi takasa cewa komai sai faman wasa takeyi da d’an yatsanta,, Hafeez yaqufula sosai yace ko bakyajina ne nace kimaimaita abinda kikafad’a daxu. Cikin tsananin faduwar gaba tafara mgn tamkar ta mai in’en “tace umh uhm dama cewa nayi inaso kabani dama domin na samu halartan bikin Hamza.

Hafeez yace okey dukk satin da kikayi anan basu isheki bane,? Meena tayi shiru! Hafeez yace kibani amsa mana ko kuma baki san cewa kinbar mijinki shi kad’ai cikin wani hali na kewa ba? 

      Kewa?? Shine abinda Meena tamai maita cikin xuciyarta, Hafeez yace toh bari kiji nazo intafi da mamata kuma ayau din nan komin dare xamu bar Gwaza mukoma Maiduguri, Meena tad’ago kai fuska a maraice tace “Dan Allah yaya kayi hkri kabarni ko kwana biyu ne inqara.

Cike dajin haushinta Hafeez yace kinsan Allah bari kiji wlh ko awa d’aya bazan bari kiqara ba, kuma kitashi ynxun nan kije kihado kayanki inajiranki a mota.

Hafeez nafad’in haka yatashi yabar d’akin, a tsakar gda ya tarar dasu Baba Rabi.. nan yaduqa har qasa yayi musu sallama yace “Baba ni zan wuce ynxu” Baba Rabi tace haba Hafeez baka tsoron kuyi dare a hanya, murmushi yayi sannan yace Bakomai insha allahu, nan yayi musu godiya yafice a gdan yakoma cikin motarsa yana zaman jiran fitowan Meena.

Abangaran Meena kuwa dagudu ta tashi takoma d’akinsu Khadija sai faman kuka takeyi, Baba Rabi nazaune cikin d’aki taga wulgawar Meena dasauri ta tashi tabi bayanta.

      Ko dashigarta ta tarar da Meena na kuka tana had’a kayanta, Baba Rabi tadubi Meena tace “ke kuma miye kikewa mutane kuka?” Meena wacce kuka yaci qarfinta tafashe dawani sabon kukan tace ” Amma Yayane yace yaxo tafiya dani bayan Kuma nafadamishi cewa muna da biki.

Baba Rabi wani uban tsaki taja tace “mtsww aekin wofi kawai yoo dama inkika zauna bikin kawu Hamza uban mexaki tsinana toh kisani dukk wani abu marar muhimmanci dakike tunani yafi miki bin umarnin mijinki domin kuwa bikin Kawu Hamza kodake ko bake xa’a daurashi dan haka kirufewa mutane baki tun baki tarawa kanki jama’a cikin d’akin nan ba.

Meena kam gabad’aya takawo iya wuya wani irin takaicine ya sarqe ta, dasauri tashirya kayanta tsaf tayi sallama da kowa kafin Khadija tadawo tayi saurin ficewa tabar gdan (khadija na gurin Sa’idu tailor ta kaimusu kayan ankonsu dinki)

    Fushi Meena tayi sosai dan haka tana xuwa tasa kayanta a booth tabud’e gdan baya tazauna.

Hafeez naganin haka yafito daga gaban mota yadawo baya inda Meena ke zaune, kowa na gdan yafito yayi musu Allah kiyaye hanya.

Batare da Bata lkci ba sukabar cikin garin gwaza, suka kama hanyan Maiduguri.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button