NOVELSUncategorized

NAJEEB 44

Lokaci d’aya oxygen din ya tsaya cak……..

Ibtisam gaba d’aya k’asa tayi ta fad’i bata san ta fad’i ba, gaba d’aya hawayen dake idonta lokaci d’aya ya tsaya cak….


Dr ne ya shigo inda ya fara dubata amma ina rai yayi halinsa, Innalillahi’wa inna ilaihirajiun abunda Dr ya iya fad’a kenan tare da fad’in Allah ya amshi rayuwarta

Zarah kuka ta saki ita dasu Mum suko su Dad da abba kukan zuci suke, najeeb kam gaba d’aya wani irin yanayi ya shiga Mai wuyan misaltuwa, lokaci d’aya hawaye ya fara zuba a idonshi lallai sunyi babban rashi a family d’insu

Ibtisam kam gaba d’aya ko kukan ta kasayi ma, zan iya cewa kaman tunaninta ya dauke Domin gaba d’aya ta daina jin komai, ita gadai ta nan ne kawai

Nan aka d’auki Granny bayan Mum ta d’aga ibtisam tare da ri’keta suka nufi Gida inda aka ma granny wanka domin kaita gidanta na gaskiya, kafin kace Mai mutane har sunji kabarin mutuwar lallai Granny tayi mutane sosai sai dai muce Allah yaji kanta lallai ciwon ajali kenan, wanda ya kama Granny lokaci d’aya ashe ciwon bana tashi bane Anata amsan gaisuwa…..

Ibtisam kam gaba d’aya ta kasa kuka, magana ba ta kasa furta komai, ganin haka yasa hankalin Mum ya tashi inda taita fad’in ibtisam kiyi kuka domin rashin kukanki akwai matsala…..

Ibtisam ido ta bita dashi tana kallonta kaman wata mara wayau yanda takeyi da idonta

Mum ganin haka yasa ta janyota jikinta tana fad’in ibtisam Granny ta rasu kiyi kuka, duk wannan abunda Mum take fad’i tana fad’a ne domin ibtisam tayi kuka amma ta’ki yi.

Koda Ummi tazo taga Mum na fama da ita akan tayi kuka amma ta kiyi kaman ma bata jin mum din, sai taji ibtisam din ta bata tausayi lallai dole tayi kuka domin kuwa ibtisam tayi mugun sabo da Granny, sunyi mugun shakuwa Sosai

Ummi itama babu yanda batayi ba amma ibtisam taki yin kuka, gaba d’aya su duka sun shiga cikin wani hali, zarah itama tayi tayi amma ta’ki kuka

Mum ta kalli ummi tace rashin kukanta Akwai matsala babba, inaga ko zan kaita hspt ne??

Zarah tace Bari dai a kira najeeb ya kaita tunda kuna amsan gaisuwa ku a nan

Zarah kiran najeeb tayi a waya ta fad’a mishi halin da ake ciki, kai tsaye yace Bari ya shigo cikin gidan

Shigowa yayi inda ya iske basa falo sai mutane wanda suka zo gaisuwa, ummi ce ta fito ganin najeeb yasa tace yauwa tana d’aki tare da nuna mai d’akin ya shiga


2gnovel


4medicals

Smidris


Koda NAJEEB ya shiga itama mum fita tayi Bayan tace ya kaita asibti, ganin haka yasa Zarah itama ta fita

Najeeb kallonta yayi gaba d’aya sai yaji ta bashi tausayi domin yasan sun shaku da Granny Sosai, gashi ta tafi ta barta bazata sake dawowa ba

Najeeb kusa da ita ya zauna tare da kallonta lokaci d’aya ya juya da ita tare da kallon fuskanta ya fara fad’in ibtisam kin tuna alkawarin da Granny tace mu d’aukar mata??  We don’t love each other but we have to live together saboda munyi Mata promise, kin San bana sonki I…..

Kuka ta saki mai sauti tare da sauke idonta akanshi, wani irin abune ya tsaya mata a wuya Mai zafi

A hankali ta Fara kiran sunan Granny tare da fad’in shikenan na rasa ki, sai kuka Sosai wi wi wi……

Najeeb jin kukanta yake har cikin ranshi, Lokaci d’aya ya janyota jikinsa tare da rungumeta yana rarrashinta tare da fad’in ibtisam addu’a za muyi mata, ba kuka ba, wannan kukan baida amfani plz ki daina….

Cikin kuka tace ya zanyi??  Just muna fira nida ita ta fad’i ban taba kawo mata mutuwa ba, amma ta tafi, ban taba zaton zata mutu yanzu ba, amma gashi ta tafi ta barni, zuciya ta babu abunda take sai ciwo tare da rad’adi Innalillahi’wa inna ilaihirajiun

Ibtisam gaba d’aya ita tama manta ko wa take tare dashi, domin bata cikin yanayin da zata iya tunawa ko ganewa

Shi kam NAJEEB sai shafa mata baya yake alaman tayi shuru…..

Mum ce ta shigo d’akin domin taji shuru basu fito ba, ganin tana manne jikin najeeb tana kuka hakan yasa Mum jin dad’i tunda tana kukan

Itama Mum zama tayi a kusa data gefen ibtisam din, ganin haka yasa Najeeb tashi tare da fad’in tunda tayi kukan bari in fita waje

Tashi najeeb yayi ya fita tare da tausayawa ibtisam din

Mum ta kira sunanta da fad’in ibtisam

D’ago Kai tayi ta kalli mum wanda gaba d’aya idon ibtisam din ya canza yayi ja

Mum tace ki daina wannan kukan addu’a ya kamata ki mata domin shine babban gatan da zaki nuna mata a rayuwa, idan mutum ya mutu babu abunda yake bukata face addu’a

Ibtisam kaman an danna stop, gaba d’aya ta tsaya da kukan lokaci d’aya, inda ta kwantar da kanta akan gadon d’akin, gaba d’aya abubuwan daya faru ita da Granny taita tunawa, lokaci d’aya kuma ta Fara Mata addu’a tare da neman Allah ya gafarta mata zunubanta, lallai ibtisam taji wannan mutuwar Sosai.

Ibtisam gaba d’aya ta rame saita k’ara yin haske, fuskanta yayi fayau, Mum a gidan take kwana dad da najeeb kuma a hotel

Yau akayi sadakan uku

Ibtisam dai har yanzu ga tanan ne dai, gaba d’aya bata jin dad’in komai, rayuwa kenan, shikenan yanzu babu Granny a wannan duniyar

Sallama Dad ne da Abba da najeeb yasa ibtisam d’aga Kai tare da gaidasu ta tashi tabar falon

Najeeb da ido ya bita harta bace Mai

Shima kanshi najeeb din yayi mugun jin mutuwar Granny, wanda ya tabbata da yanzu tana nan yazo data Fara fad’a Mai magana, Allah sarki rayuwa kenan

Dad yace Yau zasu koma Abuja, dan haka saisu tashi su wuce

Abba ya kalli Dad yace zaku tafi da ibtisam, tunda mijinta yazo banga amfanin zamanta a nan ba….

Mum tace hakane duba da irin yanayin data shiga, Indai tana nan zatai ta tunani, musamman yanda ta saba da Granny kwana tare sukeyi yau ta bud’e ido ta ganta ita d’aya Abun akwai ban tausayi

Dad yace hakane tare da fad’in Ina ibtisam din ku kirata

Mum tashi tayi inda ta nufi d’akinsu ta gansu ita da zarah duka sunyi jigum babu Mai magana

Mum tace ibtisam zo ana kira

Ibtisam tashi tayi tare dasa hijab tabi Mum inda sukai falo

Bayan ta zauna, Abba yace ibtisam inaso ki shirya zaku wuce abuja yau, za Kibi mijinki ku tafi, ina son kiyi hakuri ki zamo Mai biyayya, sannan karki manta abunda mama ta fad’a kafin ta rasu….

Kuka ta farayi domin ta tuna da abunda granny tace, tana son su kasance ita da najeeb har abada…….

Abba ne ya Katseta da yake fad’in ibtisam Nima Ina neman alfarma dan Allah….

Da sauri tace Abba karka nema alfarma a wajena ka bani umarni, zanbi ni y’arka ce komai kace inyi nimai biyayya ce a gareka

Idon najeeb na kanta ya rasa mai yasa take bashi tausayi Sosai, kodan saboda halin data shiga ne oho

Abba yace Allah yayi miki albarka, ina son ki zauna da mijinki lafiya, sannan ina son ki sani shifa aure bauta ne, sannan hakuri ne, duk abunda hakuri bai baka ba, toh rashin shi bazai baka ba, Kibi mijinki sauda k’afa, domin aljannanki tana k’asan kafarshi, sannan ki kasance mace Mai rufa ma mijinki a asiri, karki zama d’aya daga cikin mata masu fad’ama kawaye sirrin miji, komai mijinki yace kiyi, toh ki tabbata kinyi indai bai saba ma Shari’a ba, sannan karki manta najeeb dan uwanki ne, idan kika ga yayi abunda ba dai dai ba ina son ki daurashi a kan hanya, wannan Abun shine kawai nake nema a gareki ina fatan zan samu

Kuka take Sosai, bata samu ta iya bama Abba amsa ba sai kukan da takeyi Mai cin rai, yanzu shikenan kaddaranta ta soma daga yanzu, domin a wannan karan tasan dole ta zauna da najeeb, duba da yadda Granny ta nemi alfarma kuma wannan itace magananta na karshe kafin tabar duniya, inda tace tana son su kasance tare har abada, yanzu shikenan gaba d’aya rayuwarta zata koma irin rayuwar da sukai baya, za suyi rayuwa irin wacce sukai da, cikin kunci da rashin ganin girman kowa, amma babu komai zanyi k’okarin in cinye wannan jarabawan insha Allah,….

Ummi ce ta katse mata tunani tare da fad’in saiki tashi kije ki had’a kayanki.

Ibtisam tashi tayi jiki a sanyaye inda ta nufi d’akinta wanda Zarah ke zaune nan ta Fara hada kaya itama Zarah tayata ta farayi, idon ibtisam yakai wajan kayan granny da sauri ta nufi wajan kayan tare da rungumo kayan Tana kuka Sosai, tana fad’in wayyo granny shikenan yanzu kin tafi kin barni, ina nan ina kewarki Mai yasa kika tafi??  Yanzu kinsa gaba d’aya bana jin dad’in komai na rayuwa kuka take Sosai tare da shessheka

Dakyar Zarah ta rarrasheta tayi shuru inda Mum ta shigo ta kira Zarah domin tazo su tafi, motar su Dad mum da Zarah suka shiga

Ibtisam kam ita da najeeb Mota daya, duka suna baya, driver ya tada motar suka Kama hanya, ibtisam naji an tada motar ta kuma sakin sabon kuka, najeeb na jinta baice mata komai ba sai wayarshi daya d’auko yasa ear piece a kunne

Ibtisam kuka take Sosai har kanta ya fara ciwo, bata san lokacin da bacci ya d’auketa ba, ta dai farka ta ganta a kwance kanta a cinyar najeeb, wanda yasa ta tashi da sauri tare da kallonshi suka had’a ido, tayi saurin kawar da kanta gefe

Murmushi yayi domin ganin yanda take Abu kaman dole an matsa mata.

Tafiya suke har suka k’arasa garin Abuja babu wanda ya k’ara koda kallon Dan uwansa balle yayi mishi magana, koda suka k’arasa masu aikin Gidan suka kwashe musu kaya, inda ibtisam kai tsaye tayi d’akin Zarah domin har yanzu kanta na Mata ciwo tana bukatar ta kwanta ta huta, tana shiga toilet tayi ta dauro alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta hau gado sai bacci

Zarah ganin tana bacci yasa tayi dariya tare da fad’in ai dole gaba d’aya tunda akai rasuwa bata samun wani baccin kirki

Najeeb shima part d’inshi ya nufa, inda yayi toilet tare dayin wanka, da yake shi yayi sallah domin saida yasa driver ya tsaya yayi sallah, shima kwanciya yayi domin yana bukatar ya huta

Yau kwanan ibtisam Biyu a Abuja bata K’ara bari sun hadu da najeeb ba, domin kullum tana d’aki, yau Tana zaune tayi wanka tasa Wata ba’kar jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan yayi mata kyau duk da ita ba ma’abociya son kwalliya bace…..

Zarah ta fito daga toilet tace sai Ina haka??

Ibtisam tace ai tare zamu fita, domin zamu skul din su Ahmad ne Ina son ganinshi  na tabbata bai San Granny ta rasu ba

Zarah tace hakane kam, bari insa kaya muje Toh, Suma naji ance sun kusa Fara exam, ya kusa dawowa gida

Zarah itama jallabiya ta saka amma ita nata brown, ya mata Kyau, tace ma ibtisam muje

Fita sukayi inda Zarah tace bari in fad’ama Mum samu fita, part din Mum tayi inda ibtisam ke tsaye a falon tana jiranta…..

Najeeb ne ya shigo falon kallonta yayi har zai wuce ya fasa tare da dawowa yazo gabanta ya tsaya…..

Ibtisam fat fat fat gabanta ke fad’i ga zuciyarta dake bugawa da karfi

Idon shi na kanta yana kallonta, da sauri tayi k’asa da kanta

Yace sai Ina??

Kasa magana tayi domin gaba d’aya yanzu ta rasa mai yasa take jin nauyinsa gashi yana mata wani kwarjini Sosai

Yace am asking

A hankali tace zamu skul din su Ahmad

Yace da izinin wa??

Da sauri ta d’ago ta kalleshi ganin ita yake kallo shima yasa tayi k’asa dakai da sauri

Najeeb yace ban yarda a fita ba, saida izini na, tunda zaki fita without my permission ban amince ba, and kin San hukuncin macen data fita ba tare da izinin mijinta ba??

Ibtisam shuru tayi tana jinshi, amma cikin ranta Abun haushi yake bata akan wani dalili zaice saita wani tambayeshi Bayan shi ba d’aukanta yake a matsayin mata ba….

Yace koh kina son tsinuwan mala’iku ne a kanki??

Da sauri ta girgiza kai alaman a’a

Ganin haka yasa yace so as from today duk inda zaki you have to ask me, inna yarda sai aje in ban yarda ba a zauna a gida

Ibtisam bata ce komai ba,…..  Zarah ce tazo tana fad’in bros Mum ta fita ne??

Yace eh ta fita d’azu what happen??

Tace no dama zan fad’a mata zamu fita ne

Najeeb yace zaki fita da matata ba tare data tambayeni ba?? Wato ke kike son janta yawo right???

Zarah ta zaro ido tare da fad’in Wlh bros nifa Banyi niyan fita ba, ita tace in shirya in rakata, ni Wlh fitan nan dan dole zanyi ni dama zaka kaita…..

Ibtisam wani harara ta sakar ma Zarah ta gefen ido

Najeeb kallon ibtisam yayi tare da fad’in Kinji abunda tace nima inada abunyi saiku koma ciki, domin ban yarda da wannan fitan ba

Yana fad’in haka yayi part d’inshi

Ibtisam wani haushi ne ya cika ta, ji tayi kaman ta fasa ihu dan takaici, yanzu kenan duk inda zata saiya bata izini

Zarah dariya tayi tare da fad’in Kinji abunda mijinki yace saiki koma

Tsaki taja tare da hararan Zarah tayi ciki da sauri

Zarah dariya tayi tana fad’in, wannan Abun naku yana ban dariya

Najeeb koda ya shiga part d’inshi kwanciya yayi tare da lumshe ido bacci yake son yi amma ya kasa gaba d’aya sai juyi yakeyi, maganan Granny ne yake tamai yawo a kunne, ina son ku kasance a haka har abada, da sauri ya k’ara lumshe ido yana mata addu’a

Tashi yayi lokaci d’aya ya fita inda ya shiga mota tare da tada ta ya fita yabar gidan

Ibtisam na kwance gaba d’aya ranta babu dad’i domin tana son ganin k’anin Nata amma ya hanata fita

Tana nan zaune saiga Ahmad ya shigo yana fad’in sis sis

Ibtisam da sauri ta tashi Tana fad’in Ahmad, dama yau zaka dawo?  Rungume juna sukayi ita dashi suna murna

Yace a’a bros NAJEEB ya daukoni yace Kece kike son ganina

Ibtisam bata san lokacin data saki murmushi ba

Zama sukayi inda zarah ta shigo d’akin Tana fad’in Toh yanzu saiki bar fushi tunda mijinki ya kawo miki abunda kike son kije ki gani

Murmushi ibtisam tayi

Ahamd yace ina Abba da ummi, da y’ar tsohuwa mai jaraba

Ibtisam kuka ta saki tare da fad’in Ahmad Granny ta rasu……

Ahmad gaba d’aya shuru yayi yana jin wani abu yana mishi yawo a Kai…..  Yayi wajan 5 mnt a haka sannan ya saki dariya yana fad’in granny din kike ma fatan mutuwa??  Wlh Bari ta jiki zaki sani shine harda wani kuka koh?? Toh ai ba first April bane balle ace April Fool …..

Ibtisam tace Ahmad dagaske Granny ta rasu jibi ne zata cika kwana 7

Tashi yayi da sauri ya fita ganin haka Zarah da ibtisam suka bishi

Direct part din najeeb ya shiga inda ya Tarar dashi daga shi sai boxer da singlet

Najeeb yace Ahmad lafiya kuwa??

Dai dai lokacin ibtisam ta shigo ita da Zarah

Najeeb idonshi ya sauka akan na ibtisam dake kuka

Nufan Ahmad tayi ta rungumeshi tana fad’in Ahmad dagaske nake maka….

Ahmad yace Ban yarda ba, kallon najeeb yayi tare da fad’in bros dagaske abunda take fad’a gaskiya ne Granny ta rasu….

Najeeb yace eh dagaske ne ta rasu….

Ahmad wani irin kuka yasa Mai ban tausayi, tare da fad’in shine babu wanda ya fad’amin sai yanzu, wayyo Granny, kuka yake Sosai

Najeeb gaba d’aya sun Fara juyar Mai dakai ga ibtisam na kuka wanda yake jin kukan nata har cikin ranshi, ga Ahmad shima yana kukan

Karfin hali yayi inda ya kalli Ahmad yace haba Ahmad karka manta addu’a take bukata ba kuka ba, kaifa namiji ne, taya zaka dinga kuka irin haka?? Namiji an sanshi da dauriya

Nan Ahmad ya share hawayen idonshi tare da fad’in hakane, addu’a take bukata ba kuka ba, rayuwa kenan, Allah yaji k’anki Granny yasa kin huta.

Zarah da najeeb suka amsa da Ameen

Ganin Ahmad yayi shuru yasa najeeb nufan ibtisam tare da ru’ko hannunta….

Ganin haka yasa Ahmad da zarah suka fita daga d’akin

Najeeb d’ayan hannunshi yasa yana share mata hawayen idonta tare da fad’in plz ki daina wannan kukan, kalla yanda gaba d’aya kika saka kanki cikin damuwa duk kin rame, karki manta duk wani mai mai mamaci ne, dole mai rai saiya mutu komin dad’ewa, sannan ita Granny addu’a take bukata ba kuka ba…..

Cikin kuka tace kasan zafin rabuwa da wanda kake so a rayuwa kuwa??  Sai yanzu nake yarda da abunda ake fada ba mutuwa akema kuka ba sabo ne, d’aki d’aya nake kwana da Granny, gado d’aya, koda tafiya zatayi yawanci tare mukeyi, sabo dani yasa ko tafiya bata son yi, sanda zan tafi skul babu yanda batayi ba akan in fasa tun Tana fad’in bata so harta dawo tana fad’in in zauna a Kano inyi kar inje wani gari, kasan mai yasa take fad’in haka??

Duka saboda Sabo ne, ta saba dani, bata son inyi nesa da ita, gashi yau na wayi gari gaba d’aya babu ita a cikin wannan duniyar, dole inyi kuka, kukan ne kad’ai zaisa in rage abunda nake ji, kaf duniya bana tunanin akwai wanda ya shaku da Granny sama dani, a gaban idona ta fad’i ta Fara jinyar kwana biyu, haka a gaban idona ta mutu, wannan abubuwan gaba d’aya sun kasa goguwa a idona

Najeeb matseta yayi a jikinsa tare da fad’in daga ranan da mutum ya rasu, a lokacin baya son komai sai addu’a, domin wannan addu’a ita yafi bukata, ita kad’ai ce mutum Zaima mutum ka nuna mishi gata

Nasan yanda sabo yake, lallai nasan dole ki shiga cikin wani hali, but Ina son kiyi hakuri a duk sanda kika tuna ta kiyi mata addu’a, kinji

Ta tsagaita da kukan amma bata bashi amsa ba, tana nan dai manne a jikinsa

Najeeb ganin haka yasa ya dan cireta a jikinsa, yaja hannunta yai gadon d’akin da ita tare da zaunar da ita akai

Shima zama yayi a kusa da ita, ya kura mata ido, abubuwa da yawa yake ji a game da ita, wanda bazai iya misalta yanda yake jiba,  gaba d’aya baya Son ya ganta cikin damuwa

Ibtisam kam lokaci d’aya ta tashi tare da fara tafiya Tana son barin d’akin

Najeeb rukota yayi tare da rungumeta yana fad’in ibtisam, sanda Granny zata rasu ta ro’ki alfarma akan mu kasance tare har abada, wannan shine magananta na karshe……

Ibtisam a hankali tace ina sane ban manta ba, amma ina son ka sani zan zauna dakai domin haka Granny take Fata, amma badan ina so ba, najeeb gaba d’aya har yanzu na kasa manta abun da…..  Sai kuma ta saki kuka tare da k’okarin jan jikinta daga nashi

Shi kam najeeb ido ya lumshe jin tana k’okarin kwatan jikinta daga nashi yasa ya saketa tun Kafin ta fad’a mishi Kalman da yafi tsana a duniya

Fita tayi da sauri Tana kuka

Najeeb idonshi ne ya canza launi, Lokaci d’aya ya lumshe ido, tare da zama a kujeran dake kusa dashi wanda yake cikin bedroom din nashi

Ibtisam kam daki ta shiga inda ta tadda babu kowa kwanciya tayi akan gadon d’akin tana kuka, ba komai take tunawa ba sai yanda taga najeeb da Najwa, duk yanda taso ta manta da abun amma saita kasa, Abun yana damunta sosai, tana jin Abun Sosai a cikin ranta, ko tayi niyan sakewa dashi saita kasa inta tuna abun , taci kuka Sosai har bacci yayi gaba da ita

Washe gari da safe suna zaune a dinning suna breakfast saiga najeeb yazo inda ya gaida iyayenshi cikin girmamawa

Dad amsawa yayi tare da fad’in an tashi lafiya??

Yace lafiya kalau..

Ahmad da Zarah gaida najeeb sukayi wanda yasa itama ibtisam ta gaidashi

Amsawa yayi ba tare daya kalleta ba..

Dad yace ma najeeb anjima kaida mamana ku shirya kuje kuga wani gida dana siya nasa an saka komai, saiku koma can, inda akwai abunda kuke bukata saiku k’ara da kanku

Mum tayi dariya tare da fad’in Aikam, yauwa ba yanzu zata koma ba, sai anyi Mata kayan akwati gaskiya, domin ba’ayi mata ba, naso inyi tafiya inje in had’a mata Toh ban samu naje ba, abubuwa nata taso wa

Najeeb yace Mum zamu saudiya cikin week dinnan, domin ina son muje mu duba mahaifin malami na, sannan kuyi mishi godiya daya koyar dani

Mum tace hakan yayi.

Wajan k’arfe biyar NAJEEB ya kira Zarah tare da fad’in ta turo Mai ibtisam tazo ta sameshi a mota

Fad’ama ibtisam abunda najeeb yace tayi har zata ce basai taje ba, ta tuna da abunda abba yace, tashi tayi tasa after dress akan kayan dake jikinta ta fesa turare sannan ta kalli Zarah tace kizo muje tare mana

Zarah tace wa??  Sai dai kun dawo, ban zuwa gayyan sodi muje in rakaki Mota dai

Fita sukayi najeeb tunda ta fito ya kura mata ido, har suka k’araso zarah ta bud’e Mata Bayan motar inda najeeb ke zaune ta shiga driver yaja

Har suka k’arasa gidan babu wanda yama dan uwansa magana

Bayan sun k’arasa fita yayi itama ganin haka yasa ta fita suka nufi cikin gidan, wanda NAJEEB ya bud’e wow Masha Allah, falon babba ne yayi mugun tsaruwa ga kyau, gidan d’aki d’aya a k’asa da falo sai kitchen sannan d’aki hud’u a sama da falo

Ko wani d’aki ansa kayan furniture Gidan yayi mugun tsaruwa, kallonta najeeb yayi tare da fad’in mai kike bukata a saka a ciki??

A hankali tace babu komai

Yace ok, fita sukayi inda ya amshi ke din motar yace driver ya koma Gida bayan ya bashi kud’i, kallon ibtisam yayi yace shiga gaba muje

Bata Musa mishi ba, domin a yanzu tayi aniyar bin umarninshi duk da bawai tana sonshi bane, zata bishi tunda shine a saman ta, uwa uba tana tuna abunda Granny tace sannan da abunda mahaifinta shima yace Mata

Tuk’i yake basu tsaya ko ina ba, sai wajan saida waya inda yace ta fito suje, Bayan sun shiga yace a bashi latest iPhone inda aka d’auko Mai iPhone 11 ya amsa tare da tambayar Kudin aka fada mishi, ATM d’inshi ya bada aka cira cikin POS  sannan suka fita kai tsaye mtn office suka nufa yace a bashi sim card, shi yayi register da sunanshi da komai nashi

Bayan sun koma Mota ne yace ta bashi duka iPhone d’inta

Kallonshi tayi alaman akan wani dalili??

Ganin bata da niyan bashi yasa ya d’auki wayar duka a gabanta ya goge komai na ciki, tare da kallonta Wanda itama shi take kallo yace ba bincike zanyi miki a waya ba, gashi na goge komai, ciro sim d’inta yayi a gabanta ya karya sim din guda biyu, ya jefar tare da mi’ka mata wayar daya siya da sim din, yace bana bukatar kiyi amfani da abunda bani na siya ba……  Yana fad’in haka ya tada motar sukai gaba

Ita ibtisam mamaki abun yake bata, Toh miye na karya mata sim, tare da ri’ke Mata wayoyi, Indai haka yake ji basai ya siya mata sim kawai ba

Shi kam NAJEEB ganin wayoyin hannunta yasa yake zargin kabir ne ya bata, wanda ya tambayi Zarah tace kabir ne ya bata wannan shine dalilin da yasa baya son ganin wayoyin a hannunta, domin kwata kwata baya bukatar abunda ya shafi kabir a wajan ibtisam din…….  Hmmm ikon Allah toh wannan idan yaji kabir din yabar mata kayan akwati ya zaiyi????

pls click

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button