2023: Matasan Arewa Sun Roki Dangote Ya Fito Takarar Shugabancin Kasa

A
cewarsu, Najeriya na bukatar basira da shugabanci irin na mutane kamar Alhaji Aliko Ɗangote, Femi Otedola, Mrs Ngozi Okonjo Iweala da sauransu, da suka yi nasara a harkokinsu.
Matasan na arewa sun ce bai dace a bar batun shugabancin Najeriya a hannun ƴan siyasan zamanin yanzu ba kuma suka yi kira ga yan Najeriya kada su yarda a rude su da kyautan kudi da kayan abinci a 2023.
Matasan na Arewa sun bayyana hakan ne cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Mohammed Ɗanlami, da magatakarda, Desmond Minakaro a ranar Juma’a.
“Ilimi da ƙwarewar da masu kamfanoni ke samu daga kasuwanci yakan sa ya gano yadda gwamnati ke shafan ɓangaren kasuwanci, wanda shine jigon habbakar tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
“A kasa kamar Najeriya da ke da hazikan mutane da ake girmamawa a duniya irin su Mrs Ngozi Okonjo Iweala, Mrs Ibukun Awosika, Mr Bode Augusto, Mr Segun Agbaje, Mr Fola Afrika, Alhaji Tunde Folawiyo, Mr Atedo Peterside, Mr Kola Adesina, Alhaji Aliko Ɗangote, Me Femi Otedola, Mr Herbert Wigwe da Mr Aig Imoukhuede, wadanda ke da ilimin kasuwanci, me yasa za a bari wadanda ba su da wannan ilimin su rika shugabantar kasar?
“Duk dan kasuwar da zai iya bunkasa kasuwanci da a kasa mai hadari kamar Najeriya tabbas zai iya jan ragamar kasar. “Najeriya za ta bunkasa idan ya zama shugaba tunda dama shi mai samar da ayyuka ne kuma zai samar da yanayi da kasuwanci za ta bunkasa.
“Muna rokon yan kasuwa da suka yi nasara a ɓangarorin su su shiga takarar shugaban kasa a 2023, ya zama dole su shiga a dama da su. Muna rokon ku zo ku jagoranci ƙasar nan ba wai kasuwancin ku ba kawai. Ku zo ku ceto Najeriya daga shugabanci maras alkibla.”
Daga Muryaryanci
[ad_2]