MAKAUNIYAR KADDARA 54

 *Page 54*

………..Duk yanda taso dojewa a baya doleneta ta yarda suka shigo sashen nata a tare, kusan duk sai da suka ɗago suka kallesu jin sassanyar muryarsa na 

sallama. Bayansa ta koma ta maƙale saboda kunya da taji na iyayenta da ƴan uwanta. Gani take kamar kowa zai gane abinda ya faru kafin su shigo, Aunty Salima 

ce ta bashi kujerar da take zaune. Babu musu ya zauna yana musu sannu da zuwa fuskarsa a ɗan sake.

    Cikin mutunta juna sukai gaisa. Yana musu godiya suna masa, tare da jera musu addu’oin zaman lafiya mai ɗorewa na har abada da zuri’a mai albarka da 

nagarta. Gwaggo Maryama ce tai masa bayanin kowa a wajen da matsayinsa wajen Zinneerah, ya ƙara musu godiya yana ambaton masha ALLAH. Kafin ya miƙe bayan 

suma su Meenal sun gaishesa. 

     Sai da yazo saitin Zinneerah dake tsaye yay magana ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce. “Ki sameni idan sun tashi tafiya”.

      Binsa da kallo kawai tai ta gefen ido dan ya riga ya shige bai bata damar amsa masaba. Hankalinta ta maida akan ƴan uwanta dake yabonsa da sake jera 

masa addu’an fatan alkairi. Ita dai uffan bataceba sai zama data sakeyi. Sun ɗan ƙara taɓa hira kafin su mike domin ganin ɗaki. Lungu da saƙo babu inda basu 

shigaba, Sa’a nata santi da ƙarajin daɗin sauyin rayuwa da ƴar uwarta ta samu. Hakama Yaya Gajeje bakinta yaƙi rufuwa dan farin ciki. Karima da Atine kam 

dai anata naɗar rahoton da za’a kaima Inna fuska a taɓe.

     Babu wanda ya damu dasu, dan ƴan ɗan-musan ma dasu Gwaggo Laritu sai faman yabawa sukeyi abinsu. Bayan sun gama zagayensu sukai haramar tafiya, maganar 

cewa ta sameshi yasata cewa su jirata tana zuwa. Duk da ranta cike yake da fargabar abinda ya faru ɗazun ga kunyarsa haka dole ta nufi sashen nasa again.

       Yanzu kam bata tsaya knocking ba sallama kawai tayi da murɗa kofar ta shiga, yana tsaye alamar shirin fita yake ta shigo bayan ya amsa mata 

sallamarta da bata izini. Kanta a ƙasa saɓanin shi da yake kallonta kai tsaye, yanda batai magana ba shima baiyiba, sai ma ya ɗauke kansa daga kallon nata 

yana ƙoƙarin tattare takardun daya baza a falon. Ganin haka yasata faɗin, “Yayanmu zasu wuce”.

      Bai amsataba sai da ya gama abinda yakeyi, ƙananun ledoji guda biyu dake a saman kujera ya nuna mata, “Ki bama Gwaggo Maryam ɗaya taba ƴan ɗan-musa, 

ɗayan ki bama Gwaggo ta danya nasune suma”.

       Ɗaukata tai tana kaiwa tsuggune. “ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara arziƙi mai albarka da amfani, ya cigaba da baka kariya a dukan al’amuranka”.

      Har cikin ransa yaji daɗi da farin cikin wannan addu’a tata, dan haka yay ɗan murmushi yana amsa mata da “Amin, nagode”.  

      

      Kamar yanda ya bata umarni haka ta aikata, aiki suka shiga godiya da masa addu’a harta rakosu harabar gidan ita da su Meenal. Kasancewar motocin da 

zasu wuce dasu suna ta waje yasata jan birki iya nan tana hawaye. Rungumeta Sa’a tayi itama tana hawayen, dan harga ALLAH tanason Zinneerah. jitake kamar 

karsu rabu a yanzu, amma yaya zasuyi da ƙaddarar aure sai haƙuri.

      Tanaji tana gani suka wuce su Bahijja suka tafi rakasu har waje. Jikin bango ta lafe hawaye na cigaba da sakko mata, ɗan kwana ukun can da taje tayi a 

Danya sam ba isarta sukai ba, musamman da ayanzu baba ya samu ƴancin kansa daga hannun Inna, sai taji inama tana a zaman gidan ne har yanzu.

          Dawowar su Bahijja ya sata share hawayenta suka koma ciki suna mata tsiya ƙasa-ƙasa gudun kar Yayansu yaji. Ita dai hararsu kawai tayi dan basusan 

yaya takejinta bane. Da taimakonsu ta gyara falon, suna ƙoƙarin dasa zaman hira AK ya shigo. Tsit sukai daga dariyar zancen Meenal dake basu labarin abinda 

wata innarsu datazo daga bauchi tayi a sashen Granny yau da safe.  

      “Ku baku wuce ba?”. Ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Meenal ce tai ƙarfin halin bashi amsa. “Yayanmu muna nan sai anjima, dan ƴan bauchi ma zasu zo suyi 

muku sallama”.

     Baice komaiba sai kallon agogon hannunsa da yayi ya sake duban Zinneerah. “Ni zan fita, Khalipha zaizo da mai gyaran ruwa dake fita ta baya, idan sun 

gama ki ɗauka masa kuɗi a ɗaki saman bedside drawer”.

       Kanta ta gyaɗa masa da cewa “to” idanunta a ƙasa. Daga haka shima ya juya ya fita a binsa suna masa a dawo lafiya. 

     Sai da suka tabbatar da fitar motarsa a gidan sannan bakin su Meenal ya buɗe. Suka sheƙe da dariya suna tafawa da faɗin, “Soyayya ruwan zuma. Abin 

mamaki Yayanmu da auta a gado ɗaya”.

        Hararsu kawai Zinneerah tayi ta ɗauke kanta. Bahijja ta kamo hannunta murya ƙasa tace, “Tawan dan ALLAH da gaske ɗaki ɗaya kuka kwana da Yayanmu a 

gidan nan?”.

      “Ya ilahi”. Zinneerah ta faɗa tana zaro idanu, sai kuma ta rankwashi kan Bahijjan da faɗin, “Kirasa a waya ki tambayesa mana, wai yaushe kuka lalace 

haka ne?”.

        “Karkiga laifinmu, tunda kema jiya Yayanmu ya lalataki a gado muma gara dai ku guntsa mana kafin a kaimu dan wlhy nima aure nakeso”. Cewar Meenal 

tana wani karya jiki.

     Bahijja tai zaram tana faɗin, “Haɗa dani ƴar uwa”.

    Kallonsu kawai Zinneerah take baki buɗe, suko ko’a jikinsu. A haka su Jamal suka shigo suka samesu ɗauke da abincin rana, yanzu kam a sake suka shigo 

dan sunsan sun baro boss a can gidan.

___________________★

        A ɓangaren su Farah kam lafiya lau ta farka yau, sai dai tunda ta tashi hawaye basubar sauka mata a idanu ba, sai faman sambatu take akan dan ALLAH 

suce mata mafarki take bada gaske AK yayi aure ba. 

     Da farko daga Mammah har Mahma lallashinta sukeyi, ganin abun nata bana ƙare bane yasa Mahma fara mata masifa. 

     “Ke dan ALLAH kin ishemu haka nan, ba’irin wannan ranar ake hanngo mikiba ana nuna miki hanya kina kaucewa. Ni bansan wane irin rashin hankali ke 

damunku ku yaran yanzu da bakwa aiki da tunaninku ba. Abinda kawai kuka ɗauka idan namiji na sonku dolene ya cigaba da sonku, kun manta ita soyayya ado ce a 

cikin aure, a duk lokacin da ɗiya mace ta kasa toshe ƙofofi da ramukan ginshiƙan aurenta adon soyayya zai disashe. Duk yanda zakiso miji ki nuna ƙin 

danginsa rayuwar aurenki na cikin matsala koda kuwa su suna nuna miki basa son nakine ƙiri-ƙiri a gabansa. Koda shike kawo miki sukar danginsa ki faɗi 

alkairi da tausar zuciyarsa karki yarda ki tofa mara daɗi. Kiyi haƙuri da halayensa ku kashe ku rufe a ɗakinku dan kai ƙarar miji ga iyayenki ko nashi na 

zubar miki da kima, ke hatta ƙawayenki kikace ke kullum ƴar fallasa asirin gidankice da niyyar neman shawara to kina cikin kwan gaba kwan baya kuwa a garesa 

da zubar muku da kimar aurenku. Domin shi aure ibada ne ba komai ake samu hundred percent a cikinsa ba. Dole yau ayi dariya gobe kuka, jibi rabi da rabi 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button