Uncategorized
MATAR UBA 5

???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
_(A True Life Story_ )
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️
_(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
CHAPTER 5
????????????????????????????????????????
………….Asiya tun da ga Wannan ranar ta daina cin girkin Baraka idan ta bata zubarwa take idan tayi bacci sai ta Shiga kitchen ta girki indomie ko taliya Kan tayi bacci wasu lokutan Kuma da yunwa take kwana.
Baraka kullum cikin mamaki take taya za’a yi tana cin abincin Kuma babu abinda ke samin ta hakan yasa ta hakura ta d’auki alwashin gana mata azaba ba dare ba rana in yaso ta gudu ko Kuma wahala ta kashe ta.
Daddy Kuma yasa Ido sosai a lamarin Asiyah don ya lura tana cikin damuwa, gashi yarinyar na da zurfin ciki hakan yasa yake bata kulawa na musamman in dai Yana gida ta tana makale a jikin sa, Baraka Kuma tayi ta Mata Hidima kamar zata goyata Amma da zaran ya fita sai ta Zama kamar dodo.
*BAYAN WATA SHIDA*
Baraka ta samu Ciki, Daddy kullum cikin tarairayar ta yake yana bata kulawa, Asiyah Kuma ko da Wasa Bata tab’a fad’a masa abinda ake Mata ba.
Kamar kullum suna zaune a parlor shi da Baraka aka Kira wayar sa, Yana picking daga d’ayan b’angaren akace “Sir munyi baki Kuma sunce suna bukatar ganin ka yanzu”
Jin suwaye bakin hakan yasa ya Mata Sallama ya fita.
Bayan ya gama abinda yake yi a office din a hanyarshi ta komawa gida yayi hatsari, Baraka na zaune da cikin ta d’an wata shida aka kirata aka Sanar da ita ba ta tsaya b’ata lokaci ba ta fita tana zuwa asibiti ta Samu Yana emergency kuka ta shigayi ganin yanda yaji ciwo, kafan sa na dama karaya uku Haka ma kansa bandeji ne hannun sa na dama ya karye, riko hannun ta yayi da hannun hagunsa Murmushi yayi sannan yace “Baraka ki daina kuka kinji?”
Cikin kuka tace “Taya za’ayi na daina kuka ka duba kaga yanda ka ji ciwo wallahi tausayin ka ne ya kamani Allah ya tashi kafad’ar ka”
Ya amsa da “Ameen Amma Baraka Ina ji a jikina kwanaki na sun Kare Dan Allah Baraka ki kula da Asiyah ki rike ta tamkar Yar ki kisani cewar marainiya ce, dukiya ta duk sunan tane akai sannan Kema akwai naki kason da abinda ke cikin ki, Dan Allah ki sata a makaranta tayi karatu ta Zama likita sannan ki aurar da ita ga miji na gari” ya Karasa Maganar Yana kuka, cikin kuka Tace “Insha Allah Kai zakayi Mata duk wa’annan, insha Allah Kai Zaka aurar da ita”
Kallon ta yayi idon sa cike sa hawaye yace “Na so nayiwa Asiyah kallon karshe Amma nasan bazaiyu ba”
“Dan Allah Sadeeq ka daina fad’in haka”
Murmushi yayi yana ciza leb’en sa,shi kad’ai yasan abinda yake ji yace “Ki taimaka min da Ruwan sha”
Cikin rashin nitsuwa ta fita don sayo ruwa.
Tana shigowa d’akin ta ji likita na cewa time of death 6:46″ Yana kokarin rufe Masa fuska, yatsar da pure water hannun ta tayi, ta d’aura hannu a Kai ta kwala ihu tana fad’in “Na Shiga uku” da sauri likitoci sukayi kanta Nan take ta fad’i sumammiya.
Nan ta Fara bleading dakyar suka samu suka tsayar da jinin, Asiyah na gida ta kasa bacci sai safa da marwa take duk hankalin ta ta kasa kwanciya.
A Rana ita kad’ai ta kwana, a asibiti aka sallace shi ta Kira abokan nan sa na gida da gun aiki aka Sanar da dangi na kusa da na nesa anan aka sallace shi, Aunty Rukayya ce ta d’auko Asiyah don ta ganewa idon ta don sanda ta fad’a Mata Taki yarda cikin kuka Asiyah ke fad’in “Karyane Daddy Yana Raye Bai mutu ba, Daddy bazai min Haka ba, Daddy bazai barni a duniyar Nan Ni kad’ai ba”
Rukayya Taji tausayin ta sosai, Yarinya Yar karamar ta zama marainiya ba Uwa ba uba, duk yanda za a yi Dole ma ta d’auki Asiyah ta dawo gunta” tana maganar Nan ne acikin zuciyar ta.
Sai da ta ga mahaifin ta a kwance cikin likafani ta Fad’i sumammiya, Nan aka tafi da gawar aka kaishi makwancin sa, mutanen gun duk sai da sukaji tausayin Asiyah wa amda suke da saurin hawaye Kuma sai da suka Mata kwalla ganin halin da take ciki.
Kwana ta yi ta wuni a sume farkawan ta ta d’auka mafarki take Nan ne fa bud’e sabon shafin kuka.
Tun daga Wannan ranar Rayuwar Asiyah ta canza ta lalace, Baraka abin nema ya samu gaba ki d’aya ta Hana ta zuwa makaranta makarantar ma ta Hana ta zuwa Islamiyya kuma sai ta ga dama ta Barta ta tafi Sam Bata damu da mutuwar Mijin nata ba ita dai dukiyar take so Kuma yanzu ya shigo hannun ta sai yanda taso tayi dashi.
*BAYAN WATA UKU*
Baraka ta haifi ‘yar ta ta mace kyakkyawa ce kamannin ta sak kamar Anisa, Baraka ganin kamannin Anisah ce ta tsorata da farko ganin ba amfani ta sake jikin ta, ta cigaba da kula da ‘yarta Wacce aka sawa suna Safiya.
AFTER FIVE YEARS
Safiya na gani zaune Akan koshin ta yi Hannun ta rike yake da remote, fitsari ne ya dame ta hakan yasa ta tashi ta Shiga toilet dake parlor d’in bayan ta fito ga mamakin taga TV a kashe Remote ta d’auka ta danna switch bottom Amma yaki yi a fili Tace “Na Shiga uku Kar dai na sake lalatawa, yau Mummy zata kashe Ni” ta karasa Maganar had’e da goge hawayen da ya zubo Mata.
Asiyah na gani ta Shigo parlor jikin ta duk kura da alama shara tayi ganin safiya tana kaiwa ta na kawo wa yasa ta karasa inda take Tace “Ya dai Safiya me ya faru na ganki kamar kina cikin damuwa? Kuma harda kuka lafiya kuwa?”
Cikin kuka Tace “Aunty Asiyah na Shiga uku yanzun Nan nake kallon TV sai na Shiga ban d’aki don nayi fitsari sai na dawo Naga TV ya d’auke”
Murmushi tayi Tace “ki daina kuka Bari na duba” Asiyah tayi duk abinda taga zai iya Zama matsalar Amma yaki kawo wa, huci tayi Tace “Inaga fa yaci fuse ne Dole sai an kai shi gyara.”
Safiya ta fashe da kuka Tace “Yau na Shiga uku nasan yau Mummy sai ta kusa kashe Ni”
“Ki daina kuka Safiya kinsan bana son kukan ki ko?”
Cikin kuka Tace “Aunty Asiyah Dole nayi kuka idan mummy tasan nice nasan sai ta kusan kashe Ni.”
“Ki kwantar da hankalin ki ba Mai kashe ki kinji?”
Jaaa da baya safiya tayi Tace “kamar ya? Kar dai yau d’in ma zaki karb’i laifin da ba naki ba?”
“Safiya bana so mummy ta dake ki sabida Haka Kar ki fad’a Mata kinji?”
Safiya Tace “a’a Ni gaskiya yau Kam bazan yarda ba kullum cikin karb’an laifina kike mummy ta Rika dukan ki bana so”
Murmushi tayi Tace “Muje muyi sallah” rike hannun ta tayi suka haura sama.
Bayan ta dawo daga yawon ta, ta zauna a Parlor ta d’auko remote tayi kallo Amma yaki yi ta duba sosai Amma yaki yi murmushin gefen baki tayi tace “Lallai yarinyar Nan wato na hanata tab’a TV Nan Amma Taki ji Zaki gane kurenki” Nan ta Fara kawala Kiran sunan su,cikin sauri suka sauko cikin girmamawa ta durkusawa Tace “Mummy welcome” Rai a b’ace Tace “Sau nawa nace Miki ki daina cemin mummy Ni ba mamarki bace ban haifi mayya ba” Kai ta San kasa sai Baraka ta d’aura da fad’in “uban wa ya tab’a TV Nan tsakanin ke da safiya?”