ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Zaune Alhaji Mansur da Maman Labiba suke a tsakar gidan Malan Sani yayin da Halima take jingine da filo Rumaisa tana gefenta gwanin tausayi. Tunda aka tafi da Malan Sani washe gari ta tashi da rashin lafiya, makwabciyarta ce ma tashigo saboda ma’aikaciyar asibiti ce tazo su gaisa dan ta saba kullum sai tashigo sun gaisa kafin ta wuce, bayan ta shigo ta isketa cikin wannan yanayin hakan yasa ta tsaya sai da ta taimaka mata tayi wanka ta had’a mata shayi sannan ta koma gida ta kira mai aikinta suka kama Halima suka nufi asibiti. 

Bayan anyi mata gwaji aka gano tana da ciki har ya kusa b’arewa sakamakon tashin hankalin data shiga, hakan yasa aka bata magunguna har yamma tana can, sai da matar ta tashi daga aiki kana suka dawo tare kuma ta hanata aikin komai har sai ta warke, taso ta barta a asibiti Halima tace bata so, shiyasa suka dawo, Mai aikinta tasa ta kawo masu abinci dan tace Halima kada tayi aiki. 

Cike da tausayi Alhaji Mansur yake mata ya jiki tare da kwantar mata da hankali. Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata tana fad’in wallahi Alhaji sharri akayima Malan, tunda yashigo na gane ba’a hayyacinsa yake ba, taya za’ace Malan ne zai… Hannu Maman Labiba tasa ta rufe mata baki tana fad’in ya isa haka. 

Alhaji Mansur yace yanzu kam bamu da wata sheda, duk da nayi magana da Brr. Kamal kuma shima yace sunyi waya da Alhaji akan yana so yaje suyi wata magana mai muhimmanci saboda zai shigar da k’ara, amma yace Alhaji bai riga ya bashi wata sheda da zai iya tsayawa da ita ba, kawai zaije ya tsaya ma Malan Sani idan Allah yasa basu da shedar da zata kada Malan Sani komai zaizo cikin sauki, idan kuma suna da ita sai dai Allah ya bimasa hakkinsa domin kotu da sheda take amfani. 

Halima tace bakomai nayi imani da k’addara, kuma ina rokon Allah yasa mani juriya akan wannan abun tashin hankalin daya samemu, insha Allahu Allah bazai bar kosu waye suka aikata haka ba. 

Alhaji Mansur yace haka ake son mutum mai yarda da k’addara, inaso kuma idan komai ya lafa mutafi gaba d’aya Kano tunda Malan Sani yace shima can zai koma.

 Murmushi Halima tayi tana fad’in matuk’ar aka yanke hukunci mukayi nasara to tare zamu tafi, amma idan sune sukayi nasara zan zauna anan har sai ranar da Malan ya rasu, idan ina raye zan koma Kano da zama, idan kuma nima na tafi to ga Rumaisa nan ku kular mani da ita. 

Tausayin Halima ne ya kamasu, hannu yasa ya goge idonshi kafin ya mik’e yana fad’in ina so naje naga Malan Sani. Saurin kallonsa tayi tana fad’in dan Allah ka tafi damu. Alhaji Mansur yace shikenan muje. 

***

Kuka kawai sukeyi Alhaji Mansur ne yake lallashin su. Bayan sunyi shiru Malan Sani yace shikenan yanzu an rufe Alhaji ba tare da nayi rakiyarsa ba? Wallahi an cutar dani, Allah ne kad’ai zai saka mani, yanzu ina Ummun Ra’eez take?…. Labarin halin da take ciki Alhaji Mansur ya bashi. 

Sosai yake kuka yana fad’in Allah ya isa, Allah ka saka mani. Alhaji Mansur yace bani labarin abinda ya faru…..Komai Malan Sani ya fad’a masa har zuwansa gida ya kwanta. Hannu Alhaji Mansur yasa ya goge kwallar data zubo masa, kallon Malan Sani yayi yana fad’in wad’an nan mutanan shed’anu ne, dalilin barinka araye saboda su d’ora laifin awajenka. 

Malan Sani yace bakomai Alhaji, zan d’auki kaddarata da hannu biyu, fatana Allah ya albarkaci abinda na bari. Alhaji Mansur yace insha Allahu zaka kara samun wasu zuri’ar ma. 

Saurin kallon Halima yayi ita ko ta duk’ar da kanta. Tambayarta yayi wata nawa? Da hannu tayi masa nuni wata biyu. Murmushi ne ya sauka akan fuskarshi, itama Halima murmushin takeyi. 

Malan Sani yace narokeki Halima da ki cire damuwa aranki saboda ki kular mana da zuri’ar mu, kinga dai halin da nake ciki, ke kad’ai zaki cigaba da kula da tarbiyar yaran mu, ki daure kisa juriya aranki dan Allah. 

Jinjina kai tayi tana hawaye. Alhaji Mansur yace zanga Brr. Kamal insha Allahu zamu san abunyi. Murmushi kawai Malan Sani yayi, dan yasan Alhaji Mansur ya fad’a ne kawai dan ya kwantar masa da hankali, amma yasan dole ayanke masa hukunci. Sallama sukayi masa suka tafi yana kara kwantar ma Halima da hankali. 

***

Fetur Lucky yasa ma Wayar Naseer da Kamfutar Alhaji bayan sun gama kallon abubuwan da suke ciki, wuta ya kuna nan take suka kama da wuta. 

Dariya Alhaj Marusa yasa yana fad’in Brr. Barau aiki yayi kyau, saura zuwa kotu, nasan dole a yanke ma Malan Sani hukunci.

 Brr. Barau yace ai mune da kotu, kuna da ni sannan muna da ‘Yallab’ai, dan haka ku kwantar da hankalin ku, wani abu sai ma na zama Alkali. Dariya sukasa gaba daya. 

**** ***

*Safiyar Litinin a kotu*….. 

Wajen k’arfe tara na safe akayi addu’ar sadakar ukku ta Alhaji Maiwada, bayan an kammala suka nufi kotu saboda k’arfe goma za’a fara shari’a, tare da Halima suka tafi bayan ta mik’a Rumaisa makaranta. 

Babbar kotu ta cika da al’umma, domin kowa yana so yaji yanda wannan shari’ar zata kasance, hatta da Mr. Kallah sai da yazo, duk da yau litinin yana da aiki a ofis amma haka yazo dan tunda Alhaji ya rasu hankalinsa ba akwance yake ba, gani yake kamar za’a ganosu idan akazo kotu, shiyasa ya tsaya yaga komai ya kammala agabanshi. 

Brr. Barau yau shiri yayi na musamman, fuskarsa babu alamun far’a dan so yake ya nuna matuk’ar damuwa akan wannan shari’ar saboda kowa ya yarda dashi, koda ya iso bakin kotu be tsaya magana da kowa ba yashiga ciki, dan baya so aganshi tare da kowa ayi tunanin wani abu, shiyasa suka shirya baza suyima juna magana ba har sai sun bar kotu saboda idon mutane ga yan jarida agefe. 

isowar Alkali yasa kowa ya natsu, bayan ya zauna aka shigo da Malan Sani, gaba d’aya aka bishi da kallo, kwana biyu amma ya canza, Halima kuwa duk’ewa tayi tana kuka. Malan Sani kuwa tunda yashigo yaki kallon kowa. 

Bayan an natsu Alkali ya bada ikon a karanto k’ara. Tashi Magatakarda yayi yana fad’in *a yau litinin goma ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da takwas (10/05/2008), wannan kotu zata saurari k’arar da hukumar kwastam ta shigar akan mutuwar shugabansu Alhaji Hamza Maiwada wanda ake zargin direbansa wajen aikata kisan a daren juma’a da misalin k’arfe bakwai na dare, bayan nan kuma suna zarginsa da hayyek’ema matar Ubangidansa a wannan rana inda sanadiyar haka har cikinta ya zube kuma ta had’u da lalurar tab’in hankali sakamakon dukan da yayi mata akai, yanzu haka tana kwance a asibiti*. 

Risnawa yayi tare da mik’ama Alkali takardar, komawa yayi ya zauna. Duk’ar da kai Malan Sani yayi hawayen bakin ciki suna zubo masa, addu’a kawai yakeyi. 

‘Dago kai Alkali yayi yana fad’in ina lauyoyin da zasu gabatar da shari’ar? Tashi sukayi suna risna kai. jinjina kai Alkali yayi kafin ya basu iznin gabatar da kan su. Brr. Barau ne ya fara gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Alhaji, sai Brr. Kamal ya gabatar da kansa amatsayin wanda zai kare Malan Sani. 

Alkali yace wanda zai fara ya fito. Komawa Brr. Kamal yayi dan ba shine zai fara ba. Matsowa Brr. Barau yayi yana fad’in idan kotu ta bani dama inaso nayima Malan Sani wasu tambayoyi. Kotu ta baka, Malan Sani ya matso gaban kotu. 

*Brr. Barau*… Kotu zata so taji sunanka da kuma san’ar ka. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button