Uncategorized

Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

“Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani’imanwakil.

Allahumma ajjirni fi musubati!!..”

Ƙasa idawa yayi, jin an saɓule wondon jikinsa yayi ƙasa,

da ƙarfi ya buɗe kwayar idanunshi da suka koma tamkar garwashin wuta. Tafarfasar da jininshi keyi shine abu mafi tartsatsi a rayuwarsa.

Hannunshi Galadima ya jawo da ƙarfi wanda dole yasa ya ɗaga sawunshi ya tsallake wondon ya zama babu komai a jikinshi  dagashi sai Boxes wanda Allah yayi mai ɗan tsawone yazo har kusa da guiwarsa saidai a matse yake.

A tsakiyar filin ya tsaidashi kana ya juya ya koma ya zauna kusa da Lamiɗo.

Jalal ne ya sunkuya ya ɗauki wondon da sauri ya miƙa wa, Haroon.

Shi kam Jabeer zuwa yanzu,

Ya sani a duniya ba’a taɓa yi mishi tozarci sama da wannan ba, ji yakeyi a duk faɗin duniya babu garin daya tsana sama da garin Rugar Bani, bai taɓa jin haushi da tsanar wani abu a duniya ba sama da mutanen garin Bani, ji yakeyi ya tsanesu gaba ɗayansu, ya tsani komai nasu, baya so da fata da sha’awan komai nasu.

ƙasar garin ma da yake tsaye a kai ya zuba mata ido ji yake tamkar ya ƙonata ta sauya launi daga farin yashi zuwa baƙin yashi.

A tsakiyar taron kuwa, da sauri al’ƙalin gasar ya jawo hannun Ba’ana da ya zaro wata asirtaciyar bulalar tsamiya, daga cikin randar bulalinshi 

sai wani motsi bulalar keyi tamkar tanada rai.

Bayan Jabeer al’ƙalin gasar ya kawoshi. Yana sake hannunshi masu busar al’gaita da sarewa suka farayi da ƙarfin su.

Lokaci ɗaya kuma ranar data take buɗe tarwal ta lumshe.

Mutanen kuwa sai tasowa da ife-ife akeyi. Kallo kuma kab ya  dawo kan farar kekyawar fatarshi da kekyawan baƙin tattausan gargasa yayi mishi ƙawanya, iya kyan fatarshi kaɗai ya ishi ɗan adam kallo.

Da ƙarfi Jabeer ya taune lips ɗinshi, yana maiji tamkar zai hudasu sai ambaton sunan Allah yakeyi, babbar yatsar ƙafarshi ta dama yasa yana caka ƙasar garin, kana yatsunshi na hannun kuwa yasa babban yana zagaye kan ƴar manuniyarshi.

A yadda yake jin zafi da ƙuna da baƙin ciki a cikin zuciyarshi ya tabbatar babu wani abu da za’ayi mishi a yanzu yaji zafinsa fiye dashi, to me za’ayi mishi mai zafi sama da tsiraiceshi da akayi.

Ba’ana kuwa cikin dariyar mugunta da sautin amo mara daɗin ji, ya taƙar-kara ya ɗago bulaliyar asirin nan, da iya ƙarfin shi ya zabga mishi ita a tattausar fatar tsakiyar bayanshi.

Da ƙarfi su Jalal kab suka rumtse idanunsu.

Lamiɗo kuwa wani irin kallo yayiwa Jabeer da yayi.

Wani ir…..!

Biya darinki uku kacal domin jin wannan labari har ƙarshe. 

Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina.

Wannan shafin nakune gaba ɗaya waɗanda suka karanta FREE PAGE????????????????

                             By

                *GARKUWAR FULANI*

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button