Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

Jinjina mata kai yayi kana yaci gaba da cewa.
“Wadannan sune, maƙurar, mgnin kariya da zan saka a jikina, zan sasu a gaban idonki, wannan ƙaramar ita zan saka a dundunyar ƙafar dama, itace kuma layar, ƙarfe, mudin wannan laya tana jikina, to wlh babu wani ƙarfe dake kan doron duniya da zai shiga jikina”.
Cikin mamaki tace.
“Koda bulet ne!?”.
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Koda menene, kuwa su wannan sabbin layune, wanda babu makarinsu, sai dai ina na ciresu a jikina,
ita wannan da zan saka a ƙafar hagu, layar zanace.
Duk sihirin mutun bazai karyashiba, zan iya ɓacewa inje ko ina, makarinta abu ɗaya ne!”.
A hankali tace.
“To menene makarinta?”.
Cikin sauƙe wani nannauyan numfashi yace.
“Idan wata rana dubuna zaicika za’iya kamani, to ammanfa tabbas, zan iya ɓacewa sai dai in ba’a barni na sha ruwaba, amman muddin akabani ruwa nasha zan iya ɓacewa.”
Da sauri tace.
“Ya Ba’ana dubunka ya cika kuma, kamar wani mugu ko maiyin mugun abu”.
Da sauri ya fizge mgnar da cewa.
“Eh to ai yanzu zan fara fataucin nemo. Suya Yaya Giɗi ne, kinga kuwa, sai yadda hali yayi”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe kana tace.
“To ita layar ɓatan da ta ƙarfe menene makarinsu?”.
Kanshi ya ɗan jingina da bakin bukkar ido ya ɗan zuba mata, kana cikin sanyi yace.
“Uhum makarinta sai in an samu maza tagwaye, da matar da bata al’ada sunyi tuwon sabon geron da za’a shuka a tsakiyar garken fulanin kana tuwon za’ayishi da garin dakan hannune, kuma maza tagwayen sune zasu tuƙa tuwon kana matar da mijinta ya tara da ita batayi wonkan tsarkiba, ta kwashi tuwon , to su kam in naci, tuwon gaba ɗaya sihirin jikina zai karye, in kuma ba haka sai dai ina an tsaga dundunyar ƙafar tawa an ciresune kafin makami ya iya min illa”.
Cikin wani irin sanyi tace.
“In sha Allah zaka nemosu lfy ka dawo dasu lfy, zanyi ta addu’a Allah ya baiyanasu.”
Kanshi ya tanƙwasar kana a hankali yace.
“Uhum sai daifa Shatu akwai wasu bulalin da aka bani tabbacin zasu worwore duk wani asiri da kafi da nayiwa jikina,
Amman duk da haka bazasu worwore waɗannan layunba, sai dai an bani tabbacin, muddinfa aka dakeni da wannan bulalin zan ji azabar dukan, da zai iya ɗauke raina”.
Cikin mutuwar jiki tace.
“Bazama su dakeka ba, Ya Ba’ana”.
Kanshi ya mirgina kana, yasa hannu ya ɗauki askarnan, kawai sai ya datsata kan dundunyar ƙafar damanshi,
Da ƙarfi Shatu tasa salati tare da rufe idonta, gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi murya na rawa tace.
“Innalillahi ya Ba’ana zaka kashe kanka”.
Cikin harshen fillanci yace.
“Ai bazanji zafinba Mata, bari yanzu in ɗinkesu, buɗe idonki ki gani.”
Cike da tsaro tace.
“Bazan iyaba, ina tsoro”.
Jin hakane yasa bai kuma ce ta buɗe idonba, har saida ya gama cusa layun kana yasa ƙayar aduwa ya rinƙa hudawa yana ɗinkawa da zaren, gashin bindin shanu, saida ya gama yace ta buɗe idonta.
Cikin tsoron ta zubawa wurin ido, ga jini ya ɓata ko ina,
Sai kuma ta ƙurawa ƙafafuwan ido ganin yana shafa musu man shanu sai wani tafasa wurin yakeyi, cikin mintuna uku duk wurin yayi tib-tib kamar ba shiba.
Cikin tsoro tace.
“Ya Ba’ana, ka dena irin wadannan abubuwa, wallahi shirka ne, tsafine babu kyau! Haramunne.”
Ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa tace.
“Kayi haƙuri, shiyasa tun forko ina son ince maka ba kyau bana son kana irin wadannan abubuwan”.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
“In kin sake min mgnar, bulala ɗaya zan ɗauko cikin bulalin shaɗi na, in zaneki da ita sau ɗaya kiji irin zafin da masu gangancin cewa suna sonki, sukeji a jikinsu.”
Cikin tsoro tace.
“Bazan sake bama Ya Ba’ana wadannan, bulalin da kake tsumasu da dafin kunama ai Ni kam na sani bulala ɗaya zakamin zan mutu”.
Da sauri yace.
“Azubillah, Mata kada ki sake cewa zaki mutu, domin duk randa kika mutu nima zan mutu, sai dai batun gsky ko Mata, duk mutumin da kikaga ya iya jure bulalin shaɗi na, har ya kai matakin nasara, to wlh ki sani ki shaida, jarumine, irin jaruman da sunyi ƙaranci a duniya.”
Hannu tasa ta kange fuska daga wani irin kallo mai cike da so da yake mata,
Tabbas Ba’ana ba barbarene, amman yanada wani irin kyau mai ban mmki, a hankali tace.
“Ya Ba’ana wai da waye kake kamane?”.
Cikin murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoransa yace.
“Ni da kakata Maman babana nake kama, ita kuma ba kanuribace, fulatamare ce ita”.
Cikin sanyi tace.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
Cikin sanyi tace.
“Haba shiyasa mana kake da kyau sosai”.
Wani irin kallo ya mata tare da cewa.
“Eyeh ashe Ni kekyawan ne Mata, ke dama shine baki taɓa gaya min ba inji daga bakin wacca nafiso fiye da komai a duniya dan inji daɗi, kin bari sai wasu can keta cemin wai ni kekyawan ne”.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
“Sai anjima, Mai kyau ka tashi kaje ka tafi masallacin kaga lokacin sallan jumma’a yazo anata tafiya”.
Da murmushi ya rakata. Ita kuwa da haka ta tafi gida, sabida tuni wasu masallatan har sun fara huɗuban sallan jumma’a.
Tana shiga gida ta samu.
Rafi’a, Junainah, Ummiy da Bappa, gaba dayansu a.
Cikin Babban birnin Ɓadamaya, a cikin masarautar Joɗa, kuwa.
Tuni masallacin Lamiɗo Nuruddee, ya cika yayi maƙil da bani adam tako ina zuwa, akeyi.
Masallacin ya cika tab tamkar zai fashe, shiru kakeji babu wani amon sautin ɗan adam dake tashi, sai sautin muryarsa.
Yana tsayene cas kan ƙafafunshi,
Wata dan datsetsiyar, shaddar Super Nour ce a jikinshi wacce take Brown color a ƙalla kuɗinta zai kai dubu ɗari da ashirin, shaddar irin mai mai ɗinnane,
Yayi kauri cikin kayan ko dan yanayin suturar da ya sakane, boxes ce fara ƙal yasa a ciki, sai snglet itama fara ƙal, kana sai Rigar half jomfar yaddan dake jikinshi sai wonɗota, wanda sunyi cib-cib da madaidaicin jikinsa,
Kana sai watta tattausar doguwar al’kyabbar sa, Golding color, sai wani irin sheƙi takeyi, sai hirami fari daja irin mai ɗigo-ɗigo nan, yayi masa sakin manyan Dattawan bai lonƙosashi, ya barshi a zube bisa kafaɗunshi, sai ta gaban goshinsa da ya ɗan matseshi ya bada ɗan tsini dai-dai kan karan hancinsa,
Sai baƙin zagayen daya ɗaura bisa kam hiramin.
Kana sai wasu takalman shi dake can bakin ƙofar shuga masallacin ta ƙofar liman, takalman irin na sarauta ne half cover, wanda suma fari da ɗigon jane.
Yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali haibarsa da kimarsa da dottakunsa sunyiwa fuskarshi ƙawanya, sajen nan nashi yayi lib-lib tamkar anayi wa koren ciyawa bayi, sai wani irin sassanyan ƙamshin turaren OudKareem ɗin sa, dake tashi a jikinsa.
Muryarsace ta cika ko ina na yankin.
Shiru mutanen wurin sukayi kowa na jin, wa’azin yana ratsasu.
Yana Hudbane akan, wuraren da ya dace namiji ya gani a jikin matar da yake neman aurenta,
yana kan hankali, bisa wuce gona da iri da mafiya matasan yanzu keyi, a kan wannan dama da Allah ya basu.
Gyara tsayuwarshi yayi, tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya, ya haɗe bakin al’kyabbar jikinshin. Cikin tattausan lafazi mai ratsa kunne da zuciyar duk mai sauraro da imani yaci gaba da cewa.
“Aure wata muhimmiyar hanya ce, wanda idan aka ƙullashi zai bawa ma’auta daman saduwa, tsakaninsu, ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma’autan zasu zama sutura ga junansu. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa, a Suratul Baƙara aya ta , 187:-
(HUNNA LIBASUN-LAKUM WA, ANTUM LIBASUN-LAKUM). Ma’ana su mata suturane gareku maza, sannan ku maza suturane garesu (Su Matan).”