Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

Gyara zaman al’kyabbar sa yayi tare da kallon tarin dubban al’ummar Annabi dake zaune gabansa, hankalin da nitsuwar kowa na kanshi.
Sai ɗan haskem cameras da yake gilmawa ta kanshi da sauran na kusa dashi, shaidar ana naɗar sautin muryarsa nayin huɗuban. Cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
“Saboda haka, ya zama dole mutun, ya nitsu ya maida hankali ya zaɓi abokiyar zama ta gari da zata zame mishi sutura ya zame mata sutura, wajibine kuma kayiwa kanka da jikinta iyaka har sai an biya sadaki, an kuma ɗaura aure, shaidu sun shaida sannan zaka samu nitsuwa da ita.
Domin shi aure, yana samar da nitsuwa tsakanin ma’auranta. Ɗan Adam bazai samu cikakkiyar nitsuwa a gidansa ba sai in har yanada mata, wacca ya aura. Domin zata ɗebe mishi kewa, ta sa shi ya samu nitsuwar hankalinshi. Saboda zamansu tare, a ƙarƙashin inuwar aure zatayi mishi maganin kaɗaci. Kamar yadda Allah, (A.A.W) ya faɗi a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN ANFUSAKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA’ALA BAINAKUM, MA WADATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN).
Yana daga cikin ayoyin da Allah mai girma ya halitta mana mataye daga kawunan mu. (Mataye da muke aure da su) domin su sami nitsuwa junanku, sannan kuma ya sa muku soyayya a tsakanin ku tare da Rahma da tausayawa juna. Lallai a cikin wannan al’amari akwai ayoyi abin lura ga jama’a’an da suke masu tunani”.
Gaba ɗaya taron al’ummar babu, hayaniya ko motsi shiru kakeji,
Baba Nasiru kuwa, yana dai zaune ne cikin sahun da masallacin amman ji yake tamkar ya shaƙo wuyan Jabeer sai ya kaishi ƙiyama, Baba Bashiru ne dake gefenshi, ya ɗan kalleshi tare da yin ƙasa da murya yace.
“Ya Nasiru ka nitsu mana ka koyi danne abinda ke ranka”.
Cikin tarin baƙin ciki yace.
“Haba Bashiru ya zanyi in iya danne abinda ke raina, bayan da kai sani dama duk sauran yan uwanmu, mahaifinmu ko sarautar sarkin ƙofa bai bamuba,
Tunda ya bawa Ya Muhammad, Galadima, yana rasuwa, madadin a maida sarautar Galadima kaina, ko kan Hashim tunda shi ubanshine Galadima, sai ya ɗauki wannan sarautar ya bawa, Jafar shi ɗan rashin adalci.”
Murmushi Baba Bashiru yayi tare da cewa.
“To ai kuma dai gashi ya haukace ko? Ina dai yanzu sarautar tafi ƙarfinsa, dole dai ya barta”.
Cikin fusata Baba Nasiru yace.
“To ɗaya barta ya haukace ɗin ma, ya maidota ga ƴan ɗakinmu ne, inji, wancan tsohon ya bawa, waishi ya bawa ƙaninshi, ai shima ɗan tsohon sarkine
Sannan kana ganin yadda ya kuma ɗaukar sarautar GARKUWA ya bawa Jabeer, sannan babban tashin hankalin kanaga yau tare suka fito ɗakin labbare dashi wannan munafikin yaro, waishi Sheykh ɗan iska anyi asiri anyi tsafi duk baya kamashi yadda mukeso”.
Barrister Kamal ne dake gefensu, yayi ɗan wani guntun tsaki cikin tsuke fuskarsa, da jin haushin yan uwan nashi yace.
“Ya Nasiru kufa, ji tsoron Allah, ku tuna, cikin Masallaci kuke, kuma ba kyau liman na huɗuba ana. Surutu.”
Wani irin mugun kallo Baba Bashiru ya watsa mishi tare da cewa.
“To ɗan masu matacciyar zuciya, wa’azin da yakeyi ai tun kan a haifi uwarshi mun sani”.
A kufule Barrister Kamal yace.
“Ƙaryane, da kun san abunda ya sani wala Allah da zuciyarku ta tsarkaka”.
Shiru yayi tare da fuskantarta Inda limamin take jin yana cewa.
“Halaccin kallon matar da mutun yakeso ya aura.
Haƙiƙa munsan matarka abokiyar rayuwarka ce. Kuma gonarka ce da zakayi shuka a cikinta, sannan kuma gareta zaka samu konciyar hankali. Kuma shi manufar yin aure ya hana kallon wata ko wasu matan wanda ba nakaba da dai makamantansu Irin hakan.
IN KUWA HAKANE TO LALLAI AKWAI BUƘATAR SAI MUTUN YA ƊARJE! YA ZAƁA. Haka kuwa baya yiwuwa sai ka kalleta sosai da sosai. Saboda mahimmancin haka nema shariyar musulunci ta yardar maka da ka kalli wacce kakeso zaka aura da kyau. Don ka tabbatar da wancan abubuwan da aka ambata a sama.
Kuma wannan dama da Shari’a ta bada ta bada shine, a matsayin halasci na wurin mafi yawan malamai, kuma wannan Halascin da akace halasne ya haɗa da cewa. Shin ta yarda ka kalleta, ko bata yardaba, halasne in dai ka kalleta. Kuma wannan hukuncin haka yake a wojen mafiya yawan malamai, sai dai Malikiya, sunce shi hukuncin Halascin ya dogara ne, in ta bashi izinin amma in bata bashi izinin ba to bai halasta ba.
Haka kuma shi wannan hukuncin halascin an samo shine daga, hadisin Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) yace, wani mutun ya nemi auren wata mata, ƴar Madina, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: “Shin ka kalleta kuwa?”. Sai mutumin yace, wa Manzon Allah (S.A.W) “A’a ban kalleta ba”. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace.
“Tafi ka kalleta, domin mutanen Madina sunada wata illa a idanunsu.”
A wata ruwayar kuma da Abu Dauda ya ruwaito.
Daga Jabir Bin Abdullahi cewa: Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace.
“Idan ɗayanku zai nemi aure to idan ya sami ikon kallonta wato kallon abin da zai burgeshi zuwa ga aurenta, to ya aikata hakan, (ma’ana ya kalleta) Jabir yace sai na nemi wata mata, daga cikin ƙabilar Banu Salma na kasance ina bibiyanta har sai da naga abin da zai birgeni a aurenta.
Ɗan zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa.
“To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waɗannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci ɗanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, Gargaɗi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura.
Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keɓantaccen wuri wanda aka keɓe ko aka ce nanne kawai za’a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka:
1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta.
A Duba Fiƙhu wadi Juzu’i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ƙara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni’imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni’iman jiki.
Sheikh imamul Al-Auza’i yana cewa.
“Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura.
Duba cikin Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24.
Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa:
Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da ɗago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake ɗaure samfarin Gucci,
Ganin lokacin salla ya ƙara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace.
” A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurrazaƙ Umar Sa’idu ɗan Mansur yace,
(Amirul mu’minin) ya nemi auren ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ƙanƙantarta, sai yace.
Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ƙwaurinta.
Sai tace.
(Ba don kai Amirul mu’minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya inƙanta to ana iya yin hakan.