Uncategorized

Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

Cikin wani irin jin daɗin daya bashi mamaki mai yawa tace.

“Ko kai zasu dakane Jazlaan, Sheykh Jabeer, yasha zana a hannun Fulani”.

Cikin sanyi yace.

“Su kashe Ni dai Umaymah, ke kin sani tunda nake a duniya, ba’a taɓa dukana ba, sabida koda iba yaroma ban taɓa yiwa Mama da Ummi laifin da zai kaisu ga yimin dukaba, Abba na kuma baya dukanmu,  Umaymah kema baki taɓa koda marina ba, to kuma wa kika ga zai dakeni a faɗin duniyar nan banda ruwan sama”.

Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin cikin sanyi tace.

“Allah ya tabbatar da al’khairi cikin tafiyar naku, ka dai lura kaine GARKUWAR dole da duk abinda zai cutar da Lamiɗo ko masarautarku ko sunanta dole kai ne zaka zame musu Garkuwa, so dan Allah bana son kayiwa Lamiɗo musu bare gardama a cikin duk abinda zai umarceka”.

Cikin sanyi yace.

“To Umaymah, in na koma zamuyi mgna”.

Daga nan sukayi sallama, cikin mamaki ya kalli yadda gaba ɗaya manyan hakimai sun firfito, ga Lamiɗo ya fita amman yana tsaye bakin ƙofar motar.

Cikin sauri ya kalli Hashim tare da cewa.

“Hashim Lfy kuwa naga duk suna tsaye, garin basu da abin zamane daza’a karrama baƙi?”.

Cikin nitsuwa Hashim yace.

“Uhum cewa sukeyi, wai sun yafe ziyara da ja-jantawar Lamiɗo”.

A wojen  kuwa, cikin ɗaga sauti Danzagi yace.

“Hattara dai fulani mai ƙasar ne gaba ɗaya, ke tsaye tsakiyar garinku, maza ku bada masauƙi”.

Ya ƙarishe mgnar yana jujjuua bulalar hannunshi haka sauran fadawan.

Cikin fillanci ɗan aiken Arɗo Bani ya buɗe murya da ƙarfi cikin harshen fillanci tare da cewa.

“Maza ku bada hanya mai martaba ya iso fadar Arɗo Bani”.

Jin haka gaba ɗaya taron al’ummar fulanin suka fara buɗa hanya,

Har gaban rumfar da Arɗo Bani ke ɗauke baƙi, inda aka shimfiɗe wurin da manyan taburmaii kana aka malale manyan kilisai irin namu na fulanin dawa.

Bappa Malam Liman Alhaji Haro Alhaji Umaru, Musu, da kuma Ardo Duno  da Arɗo barwa maƙotansu, duk suka mimmiƙe tsaye sai dai gaba dayansu fuskokinsu babu wal-wala, asalima wasun cikinsu jikinsu  har ɓari yakeyi, dan fushi da zafin zuciya.

A can cikin ƙauyen Bonon kuwa, Ba’ana da sauran ƙabilum ɓamawam duk suna gaban dodon tsafinsu Bonon ɗin,

Da gudu Maman Ba’ana ta iso wurin cikin Yaren ɓacamancin ta sanar dasu zuwan, sarki Lamiɗo da tawagarsa, jin hakane yasa, Ba’ana ya miƙe jiki na rawa ya nufi rugartasu.

Su kuwa sauran yace in yaje yaga da matsala zai kirasu.

Nan ya tafi su kuma sukaci gaba da dariyar mugunta.

A cikin Rugar Bani kuwa, Bukar Baban Ba’ana ne yayi wata iriyar fitinenneyar murmushi mai cike da mugunta dan son haddasa fitina, ta yadda zai samu masarauta Joɗo da kanta ta shiga matsala.

Kutsawa yayi tayi cikin mutane har ya samu ya shigo gaba-gaba.

Lamiɗo kuwa da tawagarsa taku sukeyi cikin al’farma da ƙasaita.

Su Waziri, Galadima, Wambai, Ɗan iya, ɗan buram, duk suna biye dashi a baya,

Dogari na rike mishi da laima, fadawa kuma na zazzaune a ƙasa, gefe da gefe, Ɗanzagi kuwa muryarsa ce cika wurin baki ɗaya duk da hayaniyar da wurin kedashi.

A hankali Jabeer ya sako sawunshi woje, yana taka ƙafarshi ta dama kan ƙasar garin, yaji zuciyarshi ta buga da azaban ƙarfi har saida ta kaishi da rumtse idonshi tare da ambaton.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.

A saman red lips ɗinshi.

da ƙarfi yasa hannunshi ya dafe ƙahon zuciyarshi, tare da kuma maimata.

“Hasbunallahiwani’imanwakil”.

Sabida ji yayi tamkar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ta faɗo ƙasa. Jalal, Jamil, kuwa ido suka zuba mishi, sabida ganin yadda ya rumtse idonshi, sabida suna bakin ƙofar motar, sune ma suka buɗe mishi marfin.

Haroon kuwa da Hashim da Laminu, jira suke ya fita kafin su fita.

Cikin mugun tsana Laminu ya kalli Jabeer ɗin da ya yunƙura ya fita,

zuwa yanzu, wani irin harbawa da tsalle zuciyarshi keyi, wani irin masifeffen fargaba, da kaɗuwa ne suka dirar masa lokaci ɗaya.

A hankali duk suma su Haroon suka fito, a tsakiya sukasa Jabeer kana bayinshi na biye dasu a baya.

A hankali ya gyara tattausan al’kyabbar jikinshi, tare gyara hiramin kanshi ya kange kekyawar fuskarshi.

Takun da yakeyi ne ya ƙarawa shigarsa ta al’farma daraja,

ya fito tamkar balarabe, gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ƙasar wannan wurin.

Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace.

“Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai  hasken addini a jiki da zuciyarshi”.

Ga mamakinshi sai yaji Ɗanzagi na cewa.

“GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya”.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al’kyabbar sa buɗuwa tana bajewa, sabida ɗaga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci.

Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni’imar ambaton sunan Allah da rike littafi al’ƙur’ani, da kuma jin daɗin.

Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi.

A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin.

Inda Lamiɗo da sauran tawagarsa ke zaune.

Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna.

Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi.

Cikin nitsuwa Lamiɗo ya kallesu tare gyara zamanshi.

Muryar Ɗanzagi ce ta karaɗe wurin da cewa.

“Gyara kimtsi. A saurara dai Lamiɗo jikan ɗan  Lami Bubayero jikan Lamiɗo Joɗa zaiyi mgna”. 

Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku tace.

“Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky.”

Da ƙarfi Ɗanzagi yace.

“Amin”. Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi.

Shi kuwa Lamiɗo  a hankali yaci gaba da cewa.

 “Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa.”

Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa.

“Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu ɗaukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi”.

Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar.

Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu.

Cikin tsauri Lamiɗo ya ɗagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa.

Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi,

Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi.

Shi kuwa Lamiɗo cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli Arɗo Bani tare da cewa.

“Arɗo Bani zaku haƙura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku ɗauki makami dan ramawa?”.

Cikin tarin kufula da harzuƙa da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daɗe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haɗe yace.

“Babu wani wanda zan kuma hana ɗaukan makami,

Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana.”

Cikin tarin Mamaki da al’ajabi Bappa da sauran dattawan suka buɗe baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buɗe cikin sanyi yace.

“Baba Ardo kayi haƙuri, muyi aiki da al’ƙalami, domin al’ƙalami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ƙasarmu da nake shugabanta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button