Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata Lamiɗo Arɗo Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa.
“Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba.”
Cikin sauri Ɗanzagi yace.
“Hattara dai Ƙaramin Ardo, wannan sarkine na fulɓe masarautar filɓe ce gaba da bayanta”.
Cikin ɗaga Muryar Ardo Bani yace.
“Tafi can baƙin bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulɓe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulɓe ba”.
Cikin sauri Waziri ya yunƙura zaiyi mgna, da sauri Lamiɗo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin ɓacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun Arɗo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu baƙar mgna, cikin fushi yace.
“Masarautar Joɗa ɗince bata fulani ba?”.
A harzuƙe Arɗo Bani yace.
“Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu ɗaukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ƙasashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai ɗaya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro.
Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku ɗebo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi,
Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun ɗaya da zai iya jurar koda bulalar *(SHAƊI)* ma bare sara da yanka da suka da wuƙa a hakan kuke ganin kanku Fulani”.
Cikin tarin zafin ƙuna da tafasar zuciya Waziri yace.
“To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba”.
A harzuƙe Bukar yace.
“Ƙarya ne babu wanda yazo”.
A hankali Jabeer ya buɗe baki da nufin zaiyi mgna sai yaji Lamiɗo na cewa.
“Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar Joɗa zai iya jurarar bulalar SHAƊI bare manya ko ɗan baiwa zai iya bare jinina ƴaƴana ko jikokina, ko kun manta masarautar Joɗa ce tushen Shaɗi?”.
Cikin son harzuƙa Lamiɗo Arɗo Bani yace.
“A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaɗi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada ɗan ka ko jikanka ayi gasar Shaɗi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulɓe bace.”
Wani irin karkarwa jikin Lamiɗo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulɓe a ƙasar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, Ɗan iya, Ɗan buram, Ɗan Maliki, Sarkin Dawaki.
Gaba ɗaya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki Lamiɗo.
Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali.
Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa,
Hankalinshi tashi, ƙarfin addu’o’in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa.
Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya Lamiɗo na cewa.
“Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar Shaɗi ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi Shaɗi dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI”.
Tunda ya amɓaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daɗin alamun burinshi zai cika.
Hakama Arɗo bani wani irin asirtaccen murmushi yayi.
Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi.
Cikin tsananin kaɗuwa da firgicin batun Lamiɗo suka zuba mishi ido.
Bukar kuwa cikin karaji yace.
“Ba’ana Bukar shi zai kara dashi.”
Ya ƙarishe mgnar da fatan Ba’ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan Lamiɗo ne.
Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan.
Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi.
Ga mamakinsu kab sai sukaji Arɗo Bani na cewa.
“A yau ɗinan kuma Yanzun nan, a kuma nan za’ayi gasar Shaɗi in har kun isa fulani.”
Sosai Lamiɗo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za’asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ƙuresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace.
“Na Aminc….!
Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.
By
*GARKUWAR FULANI*
????????????????????????????????????????????
????????️????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 16
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????????????????????????
*FREE PAGE SUN ƘARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KUƊI zuwa makka????????????*
*Littafin GARKUWA na kuɗine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da haƙƙi naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za’a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki ɗaya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu ɗaya ko baki da ra’ayi kina iya turo ɗarinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuɗinki in cireki a group na, dan Allah???????? nace badon niba*
“Na Amince!”. Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar Lamiɗo suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al’ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba,
Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.
Ba’ana kuwa da tun ɗazu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daɗin yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba ɗaya, masarautar Joɗa bazata kulasuba,
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.
Arɗo Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa.
“To, ina gwanin naku?”.
Cikin karaɗi Ɗanzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa.
“Malami ba faɗen Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, GARKUWAN sarki Lamiɗo, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar Joɗa.”
Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma’anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi,
Cikin yin ƙasa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya ɗan ronƙofo kanshi, kusa da Lamiɗo murya a kausashe yace.