Uncategorized

Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

“Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace”.

Da sauri Lamiɗo ya katseshi da cewa.

“Eh amman koyarwar Masarautar Joɗa ce”.

Cikin kufula yace.

“Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar Joɗa ce”.

Cikin haɗe fuska da ƙasaita Lamiɗo yace.

“Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce”.

Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taɓe fuska yace.

“Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje”.

Cikin kausasa murya Lamiɗo yace.

“Kai ne dai zaka tashi”.

Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace.

“Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?”.

Cikin faɗa Lamiɗo yace.

“To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba”.

Jin muryar Lamiɗo ta ɗan yi samane, yasa fadawanshi suka miƙe tsaye,

Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu,

Cikin haɗe fuska Jabeer yace.

“Yesss shi bazai ƙiba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ƙaton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaɗaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ƴaƴan ai, ka kira ɗaya daga cikin ya’yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya’a in tsaya wani gardin makiyayi ya ɗimeni, tunda ba faɗin Allah bane”.

Ya ƙarishe mgnar yana yunƙirin tashi tsaye.

Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaɓe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al’kyabbar jikinshi,

Cikin tausasa harshe Galadima yace.

“Jabeer kafa san ma’anar GARKUWA a masarauta.”

Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaɓe fuska tare da cewa.

“Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani.”

Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace.

“Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine”.

Rai a ɓace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace.

“Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama”.

Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata.

Jalal kuwa cikin haɗe fuska yace.

“Wannan ma ai zancen banza ne,

An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi.”

Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya ɗaga mishi hannu.

Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ƙarar da ƴaƴan ɗakinsu,

Laminu kuwa ɗan Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daɗi yakeyi.

Shi kuwa Lamiɗo, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi.

Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.

A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni.

Arɗo Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa.

Ana gamgamin Shaɗi yanzu-yanzu tsakanin Ba’ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.

Tuni an firfito da ganguna anata kaɗe-kaɗe da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za’ayi Shaɗi yanzu.

 Kafin kace  kobo, Rugar Bani ta cika tayi maƙil da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za’ayi Shaɗi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa  kuma da jikan Sarki za’ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma’ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma’a.

Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa.

Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.

Bukar kuwa mahaifin Ba’ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya ɗauko tukunyar tsumin bulalim shaɗin da Ba’ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon.

Matasa majiya karfi ne keta ɗebo ruwa, cikin rijiyoyin garin.

Suna jiƙa taron wurin dandamalin, da za’ayi gasar kaɗe-kaɗen duk sun taru sun cika kunnen kowa.

Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali.

A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito.

A gidansu Shatu kuwa,

Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar Shaɗi tsakanin Ba’ana da jikan sarki.

Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiɗima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace.

“Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi.”

Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace.

“Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na haƙura zan auri ya Ba’ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ƙoƙarin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina”.

Da sauri Rafi’a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace,

“Rafi’a wlh ya Ba’ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahaluƙin da zai iya cin Ya Ba’ana gasar Shaɗi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa.”

Cikin sauri ta miƙe tare da miƙar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna,

Jin muryar maƙocibsu Sarkin aska, yana cewa.

“A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya .

Yanzu ma Arɗo Bani ne ya aikoni da in gargaɗeki.”

Yana faɗin haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar.

Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta miƙa ta nufi kitchin ɗin su, tana cewa.

“Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba’ana ya kawo mana muci.

Ɗazu da nace muci Adda Rafi’a ce, tace mujiraki.”

Cikin sanyi Rafi’a tace.

“Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba.”

Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace.

“Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma taƙi cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji ɓatansu ya Giɗi da rasuwar Ya Lado da Inna.”

Cikin zubda hawaye ta gyaɗa mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta.

Da sauri Junainah ta nufosu riƙe da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin.

A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa.

Tuni su Ba’ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ƙa’ida shi zai fara duka,

Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaɗa da mabusa nata yi mishi kirari.

A cikin wurin da Fadawa suka kange Lamiɗo da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer,

Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi.

“Nifa babbar matsalarta wannan abun da za’ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taɓa cin karo da wannan banzar  al’adar da kukeso in yarda ayita dani ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button