Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

Ina kuma da yaƙini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za’a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan Lamiɗon Joɗo da yaji haza a gasar Shaɗin shine ya hana wannan al’adar a masarautarsa sannan yanzu ace za’a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba’ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba.”
Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace.
“To ya kakeso ayi ɗan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da ɗan karen son jiki kana gudun abinda zai taɓa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir ɗin kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba”.
Gaba ɗaya sun hautsuna mishi zuciya,
Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al’adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a ɓace yace.
“Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za’ayi wannan abunba, sun daɗe basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane.
A kirani da ko wacce ƙabilar ma in anga dama aikin kawai!”.
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Laminu kuwa da yake cikekken ɗan jarida, tuni yana naɗe komai a faifai jawaban su.
Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran, murmushi yayi, irin nasu na manya, kana da sauri ya kira, Umaymah.
A can Babba birnin Katsina, kuwa Gimbiya Khadijah Umaymah kenan , wacce take matar ɗan Sarkin Tsinako, Kekkyawar mata mai cikar haiba nitsuwa, tana kishinɗe, bisa wata tattausar doguwar kujera, yayinda Hadimanta biyu ke mata tausa.
Jin wayarta na suwane, yasa ta buɗe idanunta dake lumshe, tunda sukayi waya d, ɗan ta Haroon ke gaya mata inda sukaje da ƴaƴan ƴar uwarta mafi soyuwa a rayuwarsu ne, taketa murmushi.
Ganin sunan mahaifinta ne yasa tayi saurin amsa kiran.
Bayan sun gaisane, Sarki Jalaluddin ya ɗanyi murmushi cikin nitsuwa yace.
“Khadijah, kira ɗan ki, ki bashi umarnin bin umarnin mu, domin yana nuna mana ai bamu muka haifeshi ba, bazamu tirsasashi ba”.
Cikin tarin girmamawa tace.
“Ranka ya daɗe, me kukeso in bashi umarni a kai nasan bazaiyi min musuba”.
Cikin jin daɗi yace.
“Kice dashi ya amince da gasar da za’ayi”.
Cikin sauri tace.
“To An gama yanzu kuwa, in sha Allah zaku sameshi mai biyayya a gareku”.
Daga nan sukayi sallama,
Kana ta kirashi, sau biyu tana kiranshi baya ɗagawa, sabida kanshi ya ɗau zafi yana ganin za’a tirsasashi ya cutar da kanshi.
Ga wani irin azabebben tsinkewa da zuciyarshi keyi,
Ji yake tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito, tayi ta tsalle a doron ƙasa.
Gashi duk tsoffin Masarautarsun sun zagayeshi.
Kowa da abinda ke ce mishi.
Ga uban kiɗen-kiɗen dake hawa mishi kai.
Ita kuwa Umaymah ganin bai amsa kiran bane, yasa ta kira Haroon yana ɗagawa tace.
“Ina Jazlaan bashi wayar”.
Da sauri yace.
“To Umaymah uwar Garkuwa gashi nan ido ya raina fata”.
Cikin barkwancinta da yaron nata tace.
“Kaci gidanku Haroon Ni ɗana ba ragobane”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“To mu gani a ƙasa mana Umaymah”.
Yana faɗin haka ya miƙa Jabeer wayar wanda yake cewa Lamiɗo.
“Bafa zan yiba, tsohon nan gwara ka miƙe kaje ayi da kai tunda kaine sarkin Masarautar Joɗa, Ni nan babu abinda na sani bayan nonon uwata sai al’ƙur’ani da hadisai, sai likitancin da kuka sani na karanta a dole badon raina yasoba, tun ina yaro kullum Ni a cikin sani dole kuke da tsabar rainin hankali, kaje a jibgeka, Ni kuwa nayi al’ƙawarin zan jinyaceka, Lamiɗo Joɗa.”
Ya ƙarishe mgnar yana amsar wayar da Haroon ke miƙo mishi cikin faɗa yace.
“Mitsss wai meye kaketa tura min wannan argar wayar taka ne?”.
Cikin mamaki Haroon yace.
“Kan uba Jabeer wayar tawace ma arga, wayar da kuɗi ta sun kai rabin million To inma argace Umaymah ce bisa layi”.
Ba tare da ya kara wayar a kunneba yace.
“Hello Umaymah”.
Cikin tausayi Jalal yace.
“Hamma Jabeer baka kai wayar kunneba”.
Lips ɗinsa ya taune tare da cewa.
“Au, zama su sani yin abu da yawa”.
Haroon kuwa mamaki yakeyi domin karo na forko kenan da yaji Jabeer yace Hello a madadin Assalamu alaikum, da shine abinda yakeyi.
Ita kuwa Umaymah tana jin ya kara wayar a kunne shi ya kira sunanta cikin rauni.
Murya a kausashe tace.
“Jabeer”.
Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace.
“Na’am Umaymah”. Cikin bada umarni tace.
“Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba”.
Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi,
Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo ya miƙe tsaye cikin tashin hankali da kiɗima da firgici da baƙin cikin dakatar da gasar Shaɗi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ƙalubanceshi ba, cikin sanyi yace.
“Zanje za’ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba.”
Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ƙalla ya kai shekaru 91 a duniya.
Cikin kauda kai yace.
“To Umaymah yadda kikace haka za’ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi”.
Da sauri tace.
“A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za’ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al’adace, to ban yardaba maza tashi”.
Ganin Ya Hashim na miƙa masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah.
To cikin sanyi.
Yana amsa wayar da Ya Hashim ya miƙa mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace.
“Jabeer ashe har kayi girman da Lamiɗo zai umarceka da yin abu kaƙi yi mishi mubaya’a,
Ashe har na haifi ɗan da zai ja da mahaifina.”
Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa.
“A’a Abba, kayi haƙuri kada kayi kuka a kaina.”
Bai kulashiba yaci gaba da cewa.
“Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za’a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ƙiyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da ɗaya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?”.
Cikin rauni da ƙunar zuciya, ya miƙe tsaye hannunshi yasa ya kamo na Lamiɗo cikin tarin ƙuna da zafin rai da takaici yace.
“Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna”.
Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zuƙatansu gaba ɗaya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa.
Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu.
Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al’fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron.
Kana fadawansu na biye dasu a baya.
Ɗanzagi yana.
“Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi”.
A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa.
Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki,