NOVELSUncategorized

YARIMA FUDHAL 1-10

 NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

*YARIMA FUDHAL*

©FIDDAUSI S.A*
(QURRATUL-AYN)

01

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM…….!


DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAD’AUKA KIN SARKI MAI KOWA MAI KOMAI.


INA ROK’O AGARESHI YANDA YA BANI IKON FARA LITTAFIN NAN LAFIYA, YA BANI IKON KAMMALA SHI LAFIYA AMIN.


TSOKACI

WANNAN LITTAFIN K’AGAGGEN LABARI NE BANYI SHI DANCIN FUSKAR WANI KO WATA BA, FATANA KAWAI AL’UMMA SU AMFANA DA DARASIN DAYAKE CIKIN SA.


BANYAR DA WANI KO WATA YA JUYAMIN LITTAFINA TA KO WACCE SIGA BA DUK WANDA YA JUYAMIN LITTAFI KO YA CIRE SUNANA ZAN BARSHI DA ALLAH KAWAI.

**********************************


**







Gida ne tamfatsetse mai dogayen katangu da suka sha zane mai d’aukan hankalin wanda yake kallo, hakanne zai baka tabbacin cewa gidan sarauta ne.

Haka kuma girman gidan zai baka mamaki kai kace gari ne guda.

Gidan na d’auke da b’angare guda bakwai, banda filin shamaki da k’afa bata iya kaiwa k’arshen sa.

Soron fada shine soro na biyu a cikin gidan, sai kuma soraye uku da za ka sake wuce wa da zai sa da ka da farfajiyar gidan, a nan ne za ka ga b’angare har guda shida. B’angaren Mai Martaba sai b’angaren Mai Babban d’aki, sannan wajen Matan sarki guda biyu, sannan b’angaren yaransa, sai can ciki kuma b’angaren bayi ne tare da ma’aikatan gidan.


Sai kuma b’angaren kwara-kwaren sarki daban sannan kicin a can k’arshen gidan, sai shamakin doki da shamakin tsakar gida.


°°°°

Gidan ya hargitse baki d’aya, jama’ar gidan sai kai kawo suke daga tsakar gida zuwa sauran sassa na gidan.

Hakan ne zai tabbatar maka da wani muhimmin abu ne yake shirin faruwa a cikin gidan.


“Allah ya taimaki sarki ina mik’o gaisuwa, Yarima Fudhal na kan hanya duk kan jama’ar gari kowa na marhabin da dawowar sa”.


Murmushi sarki ya yi wanda ba’a iya ganin sa sabida rawaninsa daya rufe rabin fuskarsa, amma duk wanda ya kalli fuskarsa zai san ya yi farin ciki da jin wannan maganar.

Fadawa suka hau fad’in’ “Sarki ya amsa gaisuwa kuma ya yi farinciki da kyakkyawan albishir d’in ka”.

Waziri Salmanu ya d’an rusuna gaban sarkin shi ma yana mik’a tasa gaisuwar tare da fad’in’ “dole kowa yayi farin ciki ya mai Martaba, domin yau kimanin shekaru goma sha biyar kenan rabon Yarima Fudhal da k’asar nan, gashi kuma yau zai dawo k’asarsa cikin k’oshin lafiya tare da nasarori masu tarin yawa”.


Shi ma Fadawa suka amsa masa da’ “Sarki ya amshi gaisuwarka ya kai babban waziri “.


Haka dai kowa ya dinga kawo gaisuwarsa Fadawan sarki na amsa masa.


Sarki ya cika da murna da farin ciki ji yake kamar yajawo goben yaga Yarima kuma d’a mafi soyuwa a gareshi.



Mai Martaba Sarki Ubaiyd kenan, ya gaji sarautan a wajen mahaifinsa sarki Salmanu. Shi kad’ai ne d’a a wajen mahaifin nasa bashi da wa ba shi da k’ani. Shiyasa yakeji da iyalinsa sosai musamman Yarima Fudhal wanda yake ganin shi ne magaji a bayan sa.


Sai dai wani abu dake b’atawa mutane rai da Sarkin kuma basu da ikon magana akai shine.


Sarki Ubaiyd ya tsani a fad’i laifin yaransa, shi a ganin sa komai sukayi dai-dai ne.

Domin ‘ya’yan sarki ne kuma jikokin sarki ‘ya’yan masu fad’a aji a cikin k’asar, a ganinsa kome suke so suyi kuma komai sukai dai-dai ne.

Abin da mutane suka kasa fahimta kenan rashin ‘ya’ya da yawane ya sa shi yin hakan, ko kuwa son nunawa duniya yaransa sunfi kowa ne?.


•••••••••••••• 

Mai Babban d’aki Hajiya Marka mahaifiya ce ga mai martaba sunanta na gaskiya Hauwa’u.

Mace ce kamila mai son addini ga faram-faram da son jama’a, ga kuma uwa uba fad’a aji in dai taja layi a gidan ko sarkin k’aryarsa ya tsallaka balle kuma sauran al’ummar gidan.

Fulani Bingel itace uwar gida a cikin gidan mace mai alkunya da addini da son mutane, tana girmama dukkan mutumin daya girmama ta ba tada wulak’anci ko kad’an gata da son ado. Yaran ta uku, mata biyu an aurar dasu Sadiya da Sa’idah sai autan su Yarima Fudhal.


Sai Fulani Sokoto mace ce fara doguwa mafad’aciya ce tak’in k’arawa. Gata makira tasan luggar tuggu kala-kala, duk bayin gidan suna tsoron ta ainun, domin sarki yana yarda da maganarta d’ari bisa d’ari.

Tana da yara biyu Mace da Namiji Jalil da Jalilah su kad’ai ne yaranta a gidan.



Sai uwar Soro babar kwarkawara ce ta sarki, Sauran kwara-kwaran sarki guda biyu duk babu wadda ta tab’a haihuwa a cikinsu.


************

Kishingid’e take bisa kushin tasha ado kamar babu gobe sark’ar gwal ce dank’areriya a wuyanta hatta warwaro da ‘yankunne zuwa zobuna duk na gwal ne. Tana sanye da wani dank’areren less fari da ta d’ora alkyabba bak’a akai.

Gefe guda farantin kayan marmari ne ajiye sai bayi uku mata zaune a gabanta suna mata hira jefi-jefi.

Jakadiyya ce ta shigo da sallamarta ta zub’e bisa carpet tana gaishe ta.



Fulani bingel ta amsa fuskarta cike da annuri tana duban jakadiyya da kanta yake k’asa.


Jakadiyya ta cigaba da magana ba tare da ta d’ago kanta ba’



“Gani Gare ki, naji ance kina nemana ?”.

Fulani ta sake fad’ad’a murmushinta, kafin ta bud’e baki ta fara magana’ “Inaso a shirya dukkan abinda ya dace domin tarbar Auta na, sannan a canja masa bayi wad’anda ki ka amince dasu”.

“Angama ya shugaba ta”.


Daga haka Jakadiyya tamik’e ta fice, ta nufi b’angaren bayi domin cika umarnin Fulani Bingel.

Nan da nan ta gama bawa kowa aikin sa, an gyare b’angaren su Yarima tsaf.

An kuma gyare masa d’akinsa duk da cewar baya nan amma d’akin fes domin kullum ne sai an share an goge shi.

“Yanzu Mama wannan Yayan namu na dawowa Sarki zai daina bi takanmu fa, baya nan ma ya aka cika bare kuma ya dawo”.


Cewar Jalil kenan yana kishingid’e a gefan mahaifiyarsu.

Yaro d’an kwalisa kenan mai shekara ashirin da bakwai a duniya. Jalila dake kwance kan cinyarta taci gaba da fad’in’ “ai ina jin ma mance zai yi muma ‘ya’yansa ne, gaskiya Fulani ta cuce mu wallahi da take k’ok’arin rabamu da mahafinmu”.



Fulani sokoto ta d’an tab’e baki tare da murmushi tana shafa kan d’iyar ta ta.


“Haba dai ita d’in me?, ai ko tana yawo da guraye k’aryarta ta rabaku da mahaifinku ku dai ku zuba ido ba ga ni ba?”.

Sallamar d’aya daga cikin bayin gidan ne ya katse su daga tattaunawar da suke.


Baiwar ta fad’i gaban Fulani sokoto tayi gasuwa tana fad’in’
“Da girman kujerar ki uwar magajin gobe, hak’ika na jiyo wani batu mafi girma!”.

Fulani sokoto ta mik’ar da Jalila da ke kwance bisa cinyarta tana duban Baiwar ta ta domin jin batun da tazo mata dashi.

“Ina jinki Ladidi”.

“A gafarce ni Uwar Magajin gobe, albishir mafi muni ne ke tafe da ni, Fulani Bingel ta saka Jakadiyya ta canjawa Yarima Fudhal bayi, 
bayan duk mun gama shirin mu a kan tsofaffin bayin nasa”.

Fulani Sokoto rik’e kai kawai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba tsabar takaici, ta yiwa Ladidi nuni da hannu akan ta tashi tafita, nan da nan Ladidi ta mik’e ta fice jiki na b’ari.

“Yanzu Mama meye abin yi?”.


Jalila ke tambayar Fulani Sokoto da k’yar ta iya bud’e baki ta ba ta amsar.

“Zan yi tunani akan haka”.


Ta mik’e tayi cikin d’akinta ta barsu nan cikin falon na ta.


*****

Jakadiyya ta sa aka jere mata ‘yan matan bayin gidan kaf ta gama duba su duk ciki ba su yi mata ba kuma bata amince dasu ba, hakan yasa tace musu kawai su cigaba da aikinsu, ita kuma ta koma b’angaren Fulani Bingel.

Da shigarta ta fad’i a gabanta tana fad’in.

“Ayi hak’uri a gafarce ni na duba duk kan bayin babu wanda su ka yi, da za’a bani dama zuwa gobe da k’arfe bakwai sai a sake d’iban sabbin Bayi kafin zuwan Yarima”.


“An baki dama, kiyi duk kan abinda ya dace”.


“Nagode kwarai da gaske”. Jakadiyya ta mik’e ta fice.


*UNGUWAR KWARI*



Unguwace da mutane da dama su ke mata ik’irari da unguwar talakawa.
Domin a ganin su babu unguwar da ta kai yawan miskinai da gajiyayyu a cikin fad’in garin kamar Unguwar Kwari.

Unguwace mara tsarin gidaje ga tarkacen bola kala-kala a cikin unguwar layi-layi, gidajen duk na k’asa mara sa kyan gani.


Amma duk da katutun talaucin da ya yiwa unguwar yawa hakan bai hana a samu wad’anda suke neman nakansu da guminsu ba. Duk da wasu jama’a nawa unguwar lak’ani da unguwar k’azamai hakan bai sa an rasa masu tsafta cikin su ba sabida ba duka aka taru aka zama d’aya ba.


Gidane na k’asa wanda katangarsa iya rabi ce kana iya hango dukkan abinda mutanan gidan suke yi a tsakar gidan.


Gidan na d’auke da d’akuna biyu kacal, sai kicin da wani kwarab’abb’an band’aki da yasha tsimmokara kala-laka domin kariya.


Gidan tsaf dashi an share shi tas ko ba tabarma sai mutum ya zauna duk da turb’ayace a k’asan.


Wata ‘yar dattijuwar mata ce zaune bisa ledar buhu a tsakar gidan da sanda a gefanta.

Idanuwanta a rufe wanda shine zai baka tabbacin makauniya ce, magana take yi cikin d’aga murya’
“Aynu! Ke Aynu!! wai mai kike yi a cikin d’akin ne haka?”.


Dattijuwar ke ta b’ab’atu bakin k’ofar d’akin da take zaune.


Gidan shiru kai kace sambatu take babu kowa a gidan, can aka d’ago yagaggen zaninda a ke rufe k’ofar d’akin da shi da sunan labule.


Wata ‘yar budurwa ce da shekarunta ba zasu wuce goma sha biyar zuwa da shida ba ta fito da ga cikin d’akin. Tana sanye da wata kod’add’iyar atamfa da ba za ka iya tan-tance kalar taba bare ganin zananta, hijabin jikinta bak’ine amma ya zama ja tsabar dad’ewa da gajiyar wanki da rana.


Fuskarta watsai bak’ace amma ba can ba, tana da manyan idanuwa da gashin ido dana gira zara-zara, sumarta har kusan girarta hakan ne zai saka kasan tanada yawan gashi sai pink lips d’inta, duk da bak’ace. Amma leb’anta pink a tak’aice dai kallo d’aya ba zai sa ka fahimci kyawunta ba.


Wato dai tana da wani sihirtaccen kyawu na ban mamaki da ba kowa ke iya sanin hakan ba.


“Gani Ummata ina shiryawa ne fa, mai zan siyo miki?”. Tayi maganar cike da shagwab’a.

Murmushi Umman tata tayi, tana mai mik’o mata wata duk’unk’unanniyar Naira hamsin “Ungo Aynu maza je ki kisiyo mana garin kwaki da sugar musha, nasan baki karya ba ko?”.


“Ehh Ummana bari in je in dawo to”.

“To ki dawo lafiya akula da hanya”.


“Amin”. Aynu ta amsa tana mai sanya wani talitsattsan silifas da k’iris ya rage ya hudo k’asa ta sanya ta fice tana ‘yan wak’e-wak’enta.


Awaje taci karo da wani mutum dake jingine jikin wani icen dalbejiya, bai da k’afa d’aya sai guda d’aya yana 
dogarawa da sanda.


Durk’usawa tayi har k’asa na ji tana fad’in’ “ina kwana Baba?”.


“Lafiya k’alau Aynu, kin tashi lafiya?”.


“Lafiya k’alau Baba, Ummata ta aikeni ne”.


“Ki dawo lafiya a kula da hanya”. Cewar Baban nata kenan. Ta mik’e ta ci gaba da tafiya abinta.
[07/07, 16:13] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®





©FIDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)


02


Mintuna kad’an da fitar ta sai gata ta dawo hannunta rik’e da leda bak’a k’arama, da sallamarta ta shigo cikin gidan Ummanta dake zaune bakin k’ofa kamar yanda ta fita ta barta ita ce ta amsa mata sallamar tana fad’in.

“Har kin dawo Aynu ?”.

“Ehh Ummata kinsan shagon Malami babu nisa ai”.

“To dauko kwano ki jik’a sai ki d’ibarwa Babanki ki d’ibi naki”.

“To Ummata”.

Ta amsa tana mai shiga cikin d’akin na su, sai gata ta dawo hannunta rik’e da babban kwano da kofuna guda uku.

Ta juye garin a cikin kwanon taje ta zuba ruwan da ta d’ebo tun asuba dake basu da ruwa sai asuba famfon unguwarsu yake zuwa.

Ta d’auraye garin sannan ta sake zuba ruwa ta dawo ta zauna ta dauki sugar ta sanya a ciki ta juya, ta zubawa Ummanta ta mik’a mata sannan ta sake zuba wani ta d’auka ta kaiwa Babanta d’akinsa yana kwance ta shiga da sallamarta yamik’e ya zauna yana amsa mata sallama.

Durk’usawa tayi ta ajiye masa kofin garin tana fad’in.

“Baba gashi inji Umma”.

“To sannun ki nagode sosai Allah muku Albarka !”.

“Amin”.

Ta amsa tare da mik’ewa ta dawo tsakar gidan inda Ummanta take ta zauna gefan ta tare da janyo ragowar garin ta hau sha.


YAMMACIN RANAR


Da yamma sai da ta kammala komai da zatayi a gidan, sannan tayi shirin islamiyya tayiwa Ummanta sallama ta tafi.


“Assalamu alaikum mutana nan gidan nan?”.

Wata mata ‘yar dattijuwa take ta kwad’a sallama cikin gida.


“Amin wa’alaikissalam Tasalla kece a gidan namu?, Bismillah shigo”.

Umma ta amsawa matar sallama tana daga cikin d’aki.

Matar ta shiga d’akin ta zauna bisa ‘yar guntuwar katifar dake yashe tsakar d’akin da bata da maraba da tabarma.

Suka gaisa da Umma tamik’awa Umma bak’ar ledar da ta shigo da ita tana fad’in.

“Gashi Umman Aynu dama abinci ne na kawo muku”.

“Amma kuwa mungode Allah ya saka da alkhairi kamar kinsan tun safe Aynu ba taci komai ba wallahi, yarinyar nabani tausayi sosai k’arama da ita amma tana fuskantar gararin rayuwa !?”.

“Haba Umman Aynu !, kada kice haka mana !, ko wanne bawa da irin jarabtarsa arayuwa, barema yau ina tafe da kyaky-kyawan albishir gareku ina kyauta ta zaton wasu matsololin naku zasu kau”.

“To Allah yasa Tasallah wanne albishir ne haka?”.

“Wato gidan Sarkin da Zainabu tawa take aiki zasu d’auki sababbin ma’aikata shine nake ganin mai zai hana Aynu taje ko Allah zai saka a dace”.

Umman tad’an jin jina kai kafin tace.

“Anya kuma?, nifa kin san bana son abin da zai saka inyi nesa da Aynu ko kad’an”.

“Ki yarje mata tayi aikin nan domin zaku samu alkhairi aciki, duk wannan abincin da ki kaga ina kawo muku daga gidan Zainabu ke zuwa dashi, bayan haka kuma ga kud’in da ake biya duk wata”.

“To zan duba ingani Allah yasa a dace”.

Cewar Umma kenan, Tasallah ta dubeta karo na biyu.

“Bawai zaki duba ba amincewa zakiyi domin nasan Babanta bashi da matsala akan hakan !, nazo miki da wannan maganar ne sabida ina da yak’inin zaku samu sauk’in rayuwar data tsananta a gare ku ne”.

Tayi shiru domin taji ko Umma za tace wani abu, jin da tayi ba tace komai ba yasa ta cigaba da magana.

“Sannan aiki a gidan ya dan ganta da b’an garen da kake aiki, kinga Zainabu Fulani Bingel takewa aiki albashinta dubu goma sha biyar ne, wad’anda ke aiki b’angaren Fulani Sokoto suna d’aukan Dubu goma, to kinga ko dubu goman ne ina laifi a wajen wanda baya dashi?”.

“Kinsan Jakadiyyar gidan Yayar Babar muce, shi ya sa ban ji komai ba nakai Zainabu aiki gidan sabida tana da kirki wallahi baza tab’a bari wata b’araka ta b’ullo ta gefen suba”.


“Hakane Tasallah !, bari Aynu tazo sai muyi maganar, mu ko b’angaren dubu goman ta samu Allah yasa masu albarka”.

“Amin, haka ya kamata kice ai”.

Nan suka cigaba da tattau nawa kafin Tasallah tayiwa Umma sallama tana fad’in.

“Idan ta amince zatayi ki turota da safe kamar shida da rabi domin anaso bakwai tayi musu acan”.

“Insha Allah zatazo kin san Aynu akwai himmar sammako ai”.

Suka sanya dariya ta fice daga gidan, tabar Umma nan zaune tana tunani.

Batafi mintuna talatin da tafiya ba Aynu tayi sallama da sauri ta shigo gidan ta ajiye jakarta tayi maza tad’auki buta ta shig e band’aki mintuna biyar tafito ta shiga cikin d’akin ta tadda Ummanta zaune tana lazimi, Aynu ta zauna gefanta tana fad’in.

“Sannu da gida Ummata”.

“Yauwa Aynu kin dawo lafiya ko?, fatan anyi karatu da yawa?”.

“Lafiya k’alau Ummata, nayi karatu sosai kuwa”.

“Masha Allah a dage sosai”.

“Insha Allahu Ummata”.


“Duba cikin kwanun da ke can rufe akwai abinci ki d’auka kici”.

“To Ummata”.

Tamik’e ta dauko ta zauna har tasa hannu zata fara ci sai kuma ta dubi Ummanta ta da tambayar.

“Umma kinci abincin kuwa?”.

“Ehh naci ‘yar gidan Umma, har Babanki shima yaci wannan nakine kici abinki”.

Aynu tasa hannu ta ci gaba da cin abincin ta.

“Ummata waye da aikin ladan nan haka?”.

“Kema ko ba’a fad’ab ba kinsan wace ai, Tasallah ce Babar Zainabu ta kawo mana d’azu”.

“Amma Umma babu abinda zamuce da Maman Zainab sai dai Allah yasaka mata kawai”.

“Amin dai, yauwa inkin gama inason magana da ke”.

“To Ummata nagama ai, bari in wanko hannuna”.

Tafice daga cikin d’akin hannunta rik’e da kwanun data gama cin abincin.
[07/07, 16:15] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIDDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©



03


Notes……………kuyi hak’uri nayi mistake a page 1 MAI BABBAN D’AKI ita ce mahaifiiyar Sarki, UWAR SORO babbar kwarkwara ce, Zakuga nasake post nashi na gyara ne.




*** *** *** 


Ta wanko hannunta ta dawo ta zauna kusa da Ummanta, Ummanta ta kamo hannunta tarik’e kafin ta fara magana.


“Aynu !, kiyi hak’uri abisa yanda kika tsinci kanki a rayuwa, ki sani komai yake faruwa da bawa haka Allah yatsara masa tun kafin zuwansa duniya, nasan ke mai hak’uri ce Aynu, ina rok’anki ki k’ara akan wanda kikeyi, domin bahaushe na cewa mahak’urci mawadaci, nasan wata rana sai labari”.

Ta danyi ajiyar zuciya na wani lokaci, kafin taci gaba da magana.

“Mahaifinki shine ya hanamin fita neman na kaina, a cewarsa bazanyi bara ba, kamar yanda shima bazaiyi ba, amma kuma duk wani hanyar samunsa ta kulle, gashi ni bana da ido bare inyi koda sana’ar k’arfice a gida, yau Tasallah tazomin da batun idan mun amince zata kaiki gidan sarki aiki, ana samun abinci sannan da albashi duk wata”.


Murmushi ne ya sub’ucewa Aynu duk da ‘yar kwallar dake saman idonta, tarik’e hannun mahaifiyarta ta k’am tana fad’in.

“Amma kun amince ko Ummata?, dannima ba nason bara wallahi gara nayi ko wanne aiki indai za’a biyani mu amfana”.

Ummanta itama murmushin tayi.

“Ya zamuyi Aynu?, ai dole mu amince sabida bamu da wani zab’i daya wuce amincewar tamu”.

“Kai amma naji dad’i Ummata kinga yanzu zamu samu kud’i mud’inka kaya musayi ta barma da katifa da takalmi, sannan kuma ga abinci, yanzu bamu ba yunwa ko Umma?”.

“Uhmmm Aynu kenan, sarkin buri arayuwa Allah dai ya warware mana !”.

“Amin Ummata”.

Daga haka suka cigaba da hira, Ummanta tanayi mata nasiha akan ta kula da kanta tayi biyayya kada tayi abinda za’a tsa neta ko ta b’atawa wani rai, sannan ta gargad’e ta akan ta zama mai hak’uri a duk inda tasamu kanta.


WASHE GARI….!


Washe gari tun asuba Aynu ta tashi tayi sallah tad’ebo ruwa ta cika gidan, tayi dukkan aikace-aikacen data saba kullum, tazo ta zauna gaban Ummanta ta gaisheta taje ta gaida Babanta ta dawo ta zauna tana jiran gari yad’anyi haske ta fita, domin babu agogo a gidan nasu.

A nanma nasihar Ummanta tayi ta mata, kafin tayi mata sallama ta lek’a d’akin Baban nata tayi masa sallama shima ya biyota da addu’a ta fice daga gidan.

Yau wani nishad’i ta keji arayuwarta domin ita dama burinta na rayuwa bai wuce yanda zata taimaki iyayenta ba, wad’anda sukai d’awainiya da ita tun tana cikin ciki, duk da gararin rayuwa da taulacin dasuke fama dashi amma hakan bai hana musu ganin sun kyautata mata ba, sai taci kafin suci, sai ta sha suke sha, intayi kuka suyi kuka idan tayi farin ciki suyi farin ciki, ba dan yanda rayuwa ta juyewa mahaifinta ba tasan bazai tab’a bari taje wani guri aikatau ba, tasan iyayenta sun sota arayuwa to itama meyesa ba zata kyautata musu ba?.


Haka ta isa gidan Babah Tasallah tana sak’e-sak’e cikin ranta, da sallamarta ta shiga gidan, Zainabu dake shara ta amsa mata sallamar tana fad’in.

“Uwar ‘yan sammako k’arfe shidda fa? Amma har kinzo!”.


Aynu tayi murmushi ta bata amsa da fad’in.

“Amma aikin san da zafi-zafi akan daki k’arfe”.

“Da gaskiyarki ‘yar gidan Umma”.

Babah Tasallah ta fad’a tana mai fitowa daga d’akinta, Aynu ta d’urk’usa ta gaisheta ta amsa fuskarta fal murmushi tana tambayarta ya ta baro Ummanta ta, Aynu ta bata amsa da.

“Lafiya k’alau take, tace ma agaishe da ke”.

“Ina amsawa, shiga d’akin ki zauna kafin da rabin tayi”.

Aynu ta shiga ta zauna, Zainabu ta gama shara ta kawo musu abin kari koko da k’osan da Babah Tasallah tayi tun asuba, suka karya dan kada su tafi da yunwa.


6:30.


Shida da rabi dai-dai suka isa gidan Sarkin tun awaje Aynu ta saki baki tana kallon girman gidan da tsaruwarsa, sabida ita ba ta yowa nan haka, to mema zai kawota tunda ita dai bayawo take ba, Zainabu ma tayi nacin suzo tak’i zuwa sai yau da aiki yakawota.

Bata k’ara tsinkewa da al’amarin gidan ba sai da suka shiga soron fad’a anan ta sha kallo kafin su wuce zuwa ciki gidan, nan kuwa mutuwar tsaye takusa yi, aranta tana fad’in.

“Dama akwai masu irin arzik’inan aduniya?, Allah yabasu kud’i da mulki amma basu damu da talakawansu ba”.

“Ke Aynu!, me kike kallo ne? ki nutsufa, duk abinda kika ga munayi kema kiyi”.

Cewar Zainabu kenan tana mai tab’ota, domin taga tad’daga kai sama tasaki baki tana kallo.

Wajen Jakadiyya suka wuce kai tsaye, suka gaisheta anan suka tadda ‘yan mata guda hud’u a tare da ita, ‘yan matan suka hauyiwa Aynu wani kallom gani-gani kamar sun ga kashi, ita dai hankalinta yana ga kallo, bama tasan sunayi ba.


“Ga yarinyar da nake fad’amiki, ‘yar gidan Malam Nasiru gurgu ce”.

Babah Tasallah ta gabatar da ita wajen jakadiyya.

Jakadiyya ta k’arewa Aynu kallo kafin tace.

“Allah sarki ! Yarinya k’arama da ita kuwa, Allah yasa dai ta samu domin mutum uku ake buk’ata kuma kinga ga guda hud’u sun zo tun d’azu, ban zaci zaki kawo taba domin kina k’ila wa k’ala akan zuwan nata, amma dai bari inkaisu wajen Fulani Bingel itace zata zab’a”.

Babah Tasallah tace.

“Amin dai insha Allahu zata samu”.

Aynu kuwa jin ance Allah yasa ta samu tuni ‘ya’yan hanjin cikinta suka murd’a gabanta yahau bugun sha uku-uku.

Jakadiyya dai ta d’ebesu su biyar suna binta abaya har b’an garen Fulani Bingel, Aynu har tuntub’e take tsabar kallo.

Suna shiga Jakadiyya ta zub’e gaban Fulani, suma sukayi yanda tayi suka kwashi gaisuwa, Aynu ta d’ago kai tana duban Fulani mace kyakykaywa mai haiba tasha ado da wani light blue d’in leshi dayasha adon stone…., jitayi an mintsineta ta gefanta dayake tana kusa da Jakadiyya tajuyo taga dukkansu kowa kansa ak’asa itama ta duk’ar da nata.

“An samo guda biyar duk da uku ake da buk’ata sai a azab’a ko?”.

Fulani ta gyad’a kai, tare da bada umarnin duk su mik’e tsaye, ba musu suka mik’e kansu duk a k’asa, ta bisu d’aya bayan d’aya da kallo, kafin tace ta gefan Aynu tayi gefe, sannan ta kuma zab’ar wata guda d’aya, yarage saura mutum d’aya ke nan?.

Jikin Aynu sai rawa yake ta tsananta addu’a sosai Allah yasa azab’e ta cikon ta ukun, domim sungama sa rai akan wannan aikin.

Cikin ikon Allah akace Aynu ta koma cikin mutum biyun da aka fara zab’a, tuni ta saki wata nan-nauyar ajiyar zuciyar.


“Wad’an nan ukun sunyi, biyun ki kai su kicin suyi aiki acan, ku kuma koware kanku”.

Ko wacce ta tsaya ita kad’ai aka nuna ta farko.

“Kece zaki dinga kula da abincinsa, wannan kuma ta kula da sharan falo da goge-goge, sai ke !”.

Akayi nuni da Aynu, gabanta yafad’i, tana jiran taji mai za’ace.


“Wannan yarinyace shiyasa nazab’eta, ke zaki dinga kula da gyaran d’akin kwanansa, ki kuma tsaftace band’aki ko da yaushe, sai kije ki basu kayan da zasu saka ku jira zuwan Yarima domin yana hanya anje tarbarsa”.

Jakadiyya tazube agaban Fulani tana fad’in.


“Angama Fulani”.

Muma muka zube tare dayin yanda tayi, muka mik’e da baya da baya muka fice, ashe wai ba’a juya musu baya sai mutum yaje bakin k’ofa, araina nace ikon Allah wani abun sai gidan sarauta.


Da murnata muka isa inda mukabar su Babah Tasallah nasanar musu an d’aukeni, suma sunyi farin ciki sosai, Babah Tasallah tayiwa Jakadiyya sallama ta tafi gida, mu kuma akayi wani d’aki damu.


Muna shiga nan naga abin mamaki, d’akine ciki da falo shak’are da kaya kala biyu pink da blue sai kace a shago, nan akace mu d’auki blue set biyu tare da abin wuya murjani da abin hannunsa da ‘yan kunne.

Jakadiyya tabarmu cikin d’akin muka sanya kayan, kayan kuwa da Jakadiyya ta nunawa kowa yad’auka dai-dai jikinmu kamar angwada.

Muka fito d’as damu kowa duk inda muka wuce sai kallonmu ake, ban saniba kyau mukayi ake kallonmu ko akasin haka?.

Mai makon mu koma cikin gidan sai naga kowa yana fita waje anjeru tun daga bakin k’ofar shiga gidan har zuwa soron fada, ashe pink d’in unifoam na b’angaren Fulani Sokoto ne, b’angaren Fulani Bingel blue, sai naga maza sunyi nasu layin mata ma haka, Allah ya taimake ni na tsaya kusa da Zainabu, mintuna kad’an da tsayuwarmu aka buga wata uwar bindiga data sanya ‘ya’yan hanjina kad’awa, na dank’e hannun Zainabu k’am, ita kuwa tana tamin dariya tana fad’in.

“Sarkin tsoron tsiya”.

K’asa-k’asa take maganar da dariya.

Ana gama buga bindigar kuma sai ga jiniyar kwanon motoci tana tana kawo kai.
[07/07, 16:15] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©.



04



••• 


Sarki ne da muk’arrabansa suka fara sau kowa fadawa suka ke wayesu suna yi musu kirari.

Babban abinda yabani Mamaki ya kuma d’auremin kai, shine sauran fadawan da suke tsaye bisa layi sai naga kowan ne mutum ya kwanta bisa cikinsa, Sarkin yataka yabi takan bayansu, har sai da yashiga cikin fada, suka mik’e suka kewayeshi yazauna bisa karagarsa, sanna suka dawo suka tsaya jiran fitowar yarima.

Ya ziro k’afarsa guda d’aya sai da yad’au mintuna sama da biyar kafin ya sake ziro d’aya k’afar cike da izza da k’asaita yafito yanda mahaifinsa yayi shima haka yayi takan bayan bayin fada yabi.

Sai da yashiga soron fada shima sannan sauran ‘yan uwansa mata masu aure da su Jalil da Jalila suka fito suma suka nufi fada, amma su bata kan mutane suka bi ba.

Ni kuwa abin ya tsaya min arai sosai, haka muka juya muka nufi cikin fadar zuciyata cike da wasi-wasi da ko kwanton al’amura na wannan masarauta, na fahimci wani abu guda d’aya ga masarautar tun yanzu, wato dai basu d’auki wani talaka abakin komai ba.

Sai da yarima yayi gaisuwa ga mahaifinsa Sarki Ubaiyd ya rungume d’an nasa cike da so da k’auna, kafin yamik’e yashige cikin gidan mu kuma mu da wasu mazan fada muka take masa baya.

Kai tsaye wajen Mai Baban d’aki muka nufa wato mahaifiyyar Sarkin kuma Kaka a wajensu Yarima, nan muka zube tsakar d’akin tana zaune abinta tasha irin shigarnan ta mutan da wadda suke kira da suna b’anti-b’anti, asa riga a d’aura zani har saman k’irji sannan a kawo wani zanin ad’aura k’asan wanan zanin, abun hannu da na wuyanta duka azurfa ce, mace mai fara’a, anan sun shafe kusan awa guda suna gaisawa cike da barkonci, kafin su fito su nufi b’angaren Fulani Sokoto.

Fuskarta wasai ta karb’esu, har da rungume Yarima wai sabida murna, muma kanmu dake sabbin zuwa ne mund’auka da gaske tana farin ciki da dawowarsa sab’anin yanda sauran mutan gidan suka sani.

Muka fito muka nufi b’angaren Fulani Bingel wato mahaifiyarsu Yarima Fudhal.

Muna shiga muka zube muka sake d’iban gaisuwa, ni kuwa da man nagaji da tsayuwa ina zama sai naji wata rahama ta ziyarce ni, musamman da naga sunyi kaman basu san muna wajen ba, araina nace.

“Ma huta ma wannan azaba har ina ?, da man haka aiki yake a gidan saraunata?”.


Sun shafe kusan a wanni biyu suna gaisawa, suna hira cike da so da k’aunar tare da murnar dawowarsa lafiya, amma shi abin mamaki wayarsa ce a hanunsa yana danna-dannesa.

Sai idan sun tambayeshi abu ya basu amsa da ehh ko a’a, amsar bata wuce haka abin ya bani mamaki sosai, na lura su basa damuwa darashin ko inkula d’insa, ko haka halinsa yake? Oho.

Mik’ewa yayi alamun yana buk’atar yaje ya huta sukayi sallama, mu kuma muka dafo masa baya muka fito.

Yana shiga part d’insa yayi kwanciyarsa bisa lallausan carpet d’in dake shinfid’e tsakar d’akin ya ta da kansa da kusun, Jakadiyya ta zube a gabansa tana fad’in.


“Fulani taba da umarnin canja maka bayi, gasu nan guda uku”.

Ta nuna ta farko.

“Wannan sunanta Naja’atu, wannan kuma Saima”.

Sannan ta nuna ni.

“Ita kuma wannan Aynu, sune zasu dunga kula da nan wajenka yanzu”.

Idanmu da muke tsaye munyi magana to shima yayi magana, ko d’ago kai bai yiba bare ma yasan suwaye ke zaune awajen, kawai danna-dannenta yake abinsa a wayarsa mai kama da littafi danni banko tab’a ganin irin taba sai yau a hannun yarima.

Jakadiyya bata damu da amsawarsa ba ko rashin ta, ta dubemu tana fad’in.

“Ku biyoni muje”.

Muka fice da sauri muka bi bayanta, kicin muka nufa kai tsaye aka mik’o mana tire guda uku manya ko wacce a cikinmu ta d’auki d’aya, Naja tad’auki mai kuloli manya, Saima ta d’auki mai k’ananun kuloli da flat -flat da kofuna akai, ni kuma aka bani mai kayan mar-mari aciki (Fruit).

Muka d’auka muka kai d’akin Yarima yana nan inda muka barshi, muka ajiye a gefensa Naja tad’auki flat ta zuba masa wani had’ad’dan farfeson kayan ciki, sannan ta zuba soyayyar hanta a cikin wani flat da ban, ta sake d’auko flat ta zuba masa da faf-fan naman kai, sannan ta koma gefe ta zauna.

Ita Kuma Saima a she duk kulolin data d’auko dambun nama ne aciki kala-kala ta zuba masa itama ta koma gefe.

Ni kuwa nayi diri-diri na rasa ya zanyi masa da kayan fruit d’in dana d’auko, na dubi su Naja naga ko kallon inda nake basuyi ba, na d’ago ka na dubi Yarima, da niyyar tambayarsa gabana yayi wani mummunar fad’uwa, sai a lokacin naga irin tsan-tsar kyawun da Allah ya zuba masa, domin duk shige da ficen da muke kai na ak’asa yake ban yarda ko kad’an na kalleshi ba.

Farine amma ba can ba mai matsakaicin tsayi ne, sumarsa bak’ace har zuwa sajensa da gashin baki, yana da manyan idanuwa mai cikar gashin girane daka ganshi zaka san ma’abocin son k’amshi da tsafta ne kuma masoyin son ado ne, zan iya cewa yafi kama da Fulani Bingel domin kamanninsa da ita sunfi fitowa fili mutum ne mai haiba da kwarjini sosai.


Da sauri na mai da kaina k’asa nafasa tambayar tasa, nima na koma gefe kamar yanda naga su Naja sunyi.


Mun shafe wajen mintuna talatin a zaune har zaman yafara gundura ta, sannan naga yamik’e ya zauna, yajawo flat d’in farfeson kayan ciki, Naja tamik’e da sauri ta d’auki Spoon ta mik’a masa yasaka cokalin a hankali ya d’ebi kad’an yakai bakinsa, ya hau taunawa kamar mai cin magani, ya ture gefe haka yayi ta bin farfesun ko wanne flat cokali d’aya ya keyi ya ture, kafin ya koma kan dambun daman shinema naga yad’anyi cokali uku zuwa hud’u, ya ture su gefe ya k’urawa kayan marmari ido na wani lokaci can yaja tsaki, sai jin kakausar muryarsa mukai ta daki kunnuwanmu .


“Wace takawo kayan fruit?, Je ku kiramin Jakadiyya”.

Yayi maganar kamar mai koyan magana, kuma umarni da tambaya duk a lokaci guda, hanjin cikina naji yak’ulle cike da tsoro na k’arasa inda yake na durk’usar.


Mai makon yasake magana sai gani nayi yamik’e tsaye, ban zata ba sai ji nayi ya jefe ni da tire d’in kayan marmarin duk sukayi kaca-kaca afalon Allah yasoni babu wanda ya tab’a jikina, amma duk da haka na takure waje d’aya jikina nab’ari.


Jakadiyya ta shigo da saurinta ta durk’usa tana nema min afuwa, nima ganin yanda tayi yasa nima na durk’usa kanmu a k’asa muka fara neman yafiya.


Bai ce komai ba ya shige cikin d’akinsa kawai ya barmu nan zaune.

Cike da tsoro namik’e nahau tsince kayan marmarin, Jakadiyya tace insameta b’angaren Shamaki, suka fice ita dasu Saima suka barni, nan da nan na share wajen na gyare tsaf, sannan natafi filin shamaki.

Nan na iske sauran ma aikatan gidan wasu na aiki wasu na hirarsu ciki har da Jakadiyya, naje inda take na durk’usa ta dubeni kafin ta fara magana.

“Mai kika yiwa Yarima?”.

Nan na bud’e baki na bata bayanin dukkan abin da yafaru, shiru tayi nad’an wani lokaci kafin ta cigaba da fad’in.


“Idan aka kai kayan marmari yayyan kawa ake a ajiye a gefen su, wani lokacin kuma a hannunki zaki rik’e kina yankowa kina mik’a masa yana ci, idan abinci ne zubawa zaki ki ajiye masa ki zauna gefe har saiya gama ci wannan aikin su Naja ne, sannan dole ki dinga zuwa da wuri kamar k’arfe bakwai na safe ki gyare ko ina na d’akinsa ki share, ki wanke toilet tsaf ki saka turare, idan ya shiga wanka kafin ya fito ki gyare gado da d’akin ki kunna turaren wuta, amma ke aikin ki uku ne wanke toilet d’innan da share cikin d’akin, sannan ki kai masa dukkan abin da yake da buk’ata ina fatan kin fahimce ni”.


Kai kawai na gyad’a mata domin nakasa magana, ta mik’omin wata leda viva tana fad’in.

“Ingo naki abinci kije gida, gobe kizo da wuri”.

“To nagode”.


Nafad’a ina mai mik’ewa na baro shamaki na nufi d’akin da muka canja kaya na d’auko kayan dana cire tare da set gudan na unifoam d’inmu.


Zan fito daga gidan kenan muka gamu da Zainab zata tafi gida ita ma da murnarta ta tarye ni muka fito tana fad’in.

“Ashe baki tafi ba?, naga farkon zuwa ana tafiya da wuri?”.

“Uhmm ke dai bari ! ai Allah ne ya tarfawa garina nono dan da tuni ankore ni”.

“Subhnallah ! garin yaya?”.

Zainab ta fad’a tana mai zaro ido waje.

Nan dai na bata labarin abin da ya faru, ta d’anyi shiru kafin tace.

“Sai kiyi hankali sosai da taka tsan-tsan, mancewa nayi wallahi inyi maki bayanin ayyukan gidan, amma yan zuma bari infad’a miki tun da Allah yarufa mana asiri ba’a kore kiba”.


Muna tafe tana yimin bayani har muka iso dai-dai layin mu mukayi sallama na shige gida ita kuma ta wuce zuwa gidan su.


Ina shiga Ummata ta tarbe ni cike da murna nan na zauna inata zuba mata labarin gidan sarki, ita kuma ta nata gargad’ina inkula sosai inyi abinda ya kaini ka wai ban da sha shanci, har dai da taji batun b’angaren Yarima zan dinga yin aiki, taji kuma irin tsarin aikin nawa, nan dai tayi tamin nasiha ban sanar mata abin da ya faru ba ko kad’an nayi shiru da bakina a ganina ba abin da zan sanar mata bane.


Na dauko kwanuka na juye abincin dake cikin ledar sai naga dukkan abincin da muka kaiwa Yarima ne, nan muka baje muka kwashi gara cike da farin ciki har na mance rabon da tsokar nama ta shiga baki na, Baba na dawowa na kai masa nashi abinci yakarb’a yaci yana ta samin albarka.
[07/07, 16:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©



05



*WASHE GARI*


Washe gari ma tun da na tashi da asuba ban koma ba, nan da nan nayi dukkan abin da na sabayi kullum sannan na d’umama mana ragowan abincin da nazo da shi jiya, naci na barwa su Ummata sauran.


6:30am

K’arfe shida da rabi agidansu Zainabu tamin, ko da nazo ta gama shiryawa itama tana jira na muka yiwa Babah Tasallah sallama muka tafi.

Muna isa gidan da Jakadiyya muka ci karo tana ta zirga-zirga, muka gaisheta ta amsa tana k’ara gargad’ina akan inkiyaye sosai nace.


“To insha Allah”.

Muka wuce Zainabu tayi b’angaren Fulani Bingel ni kuma nayi b’an garensu Yarima da yake b’angaren Yarima Fudhal dana Jalil a had’e suke daga ciki ne aka rabasu amma k’ofar falon ko wanne d’aki tana kallon d’ayar.


Da sallamata na shiga falon babu kowa ciki sai k’arar fanka da Tv kawai ke tashi.

Na nemi guri na zauna ina kallon k’ofar cikin d’akin nasa zuciyata na bugu, innayi kamar in tashi in shiga sai inji na kasa, ahaka na shafe kusan mintuna talatin a zaune, da k’yar dai nayi k’arfin hali na mik’e na sanya kai cikin d’akin muryata k’asa-k’asa nayi sallama.


Wani sanyi da k’amshi ya doki hancina, na d’aga kai ina kallon d’akin naga d’akin nasa kamar ba a nigeria ba, kayan cikin d’akin nidai tun da nake ban tab’a ganin irin suba, ga wata uwar katifa gado guda yana kwance abinsa abin mamaaki sai naga idonsa biyu yana dai sana’ar tasa danna waya.

Na k’arasa na zube na gaishe da shi bai amsa min ba kamar yanda bai ko kalli inda nake ba, na mik’e da sauri na shege toilet na fara wanke shi domin ina tsoron insake yin wani laifin.

Na wanke tas na sanya turarukan toilet sannan nafito domim insanar dashi cewa na gama, bai kalle niba illa zubo dogwayen k’afa fuwansa da yayi bisa lallausan carpet d’in dake shimfid’e tsakar d’akin, daga shi sai boxer abinsa, ya sanya takalmin da nagani gefan katifar yashige toilet.

Abin ya bani mamaki sosai ta kalmi a kusa da katifa, nan dai na mik’e a gaggauce na gyara katifar tasa na share ko ina na goge, akan mudubin sama nasha mamaki sai kace wani mace, kayan shafe-shafe kala-kala duk ciki babu wanda na tab’ani haka nagama k’are masu kallo danni ba wani iya karatun kirki nayi ba bare in karanta.

Naso yin karatun boko arayuwata amma Allah bai yarjemin ba, iya kacina primari 5 na daina zuwa sabida halin rayuwa na talauci daya sanyamu agaba, islamiyya ce dai nake zuwa har yanzu sabida ita sun d’aukemin biyan ko wanne kud’i dan sun san halin da muke ciki suna tausayawa rayuwata ainun, gashi itama ina ina neman dai na zuwa sabida wannan aikin.

“Tab ! bazai yuyuba yau kam dole inje islamiyya, domin bazanyi biyu babu ba”.

Na fad’a a fili ciki-ciki ina mai cigaba da gyara d’akin.


Ashe ma har yafito bansani ba ina can ina zancen zuci, sai da naji ana tab’a kwalaben kan mudubi sannan na lura da yafito, ban ko kalli inda yake ba na fice falo abina.

Saima na gani a falon tana shirya masa abin kari, muna had’a ido da ita ta jefeni da wata uwar harara, ni kuwa nad’auke kai na kamar ban san tana yiba, nayi zamana abina ina jiran umarnin Yarima.

Sai dai kuma naga ba’a gyara falon ba amma tajere masa abin kari.

“Meye zai dame ni ma tunda ba aikina bane?”.

Nayi maganar cikin rai na, sai da muka shafe awa guda zaune sannan mukaji takun fitowar Yarima, muka mik’e tsaye kanmu a k’asa ya tako cikin takun k’asaitar nasa k’amshinsa mai sanyi ya cika falon, ya nemi guri ya zauna ba tare daya ko dubi inda muke ba bare abincin da aka jere masa.


“Ohh ikon Allah ! ni dai tun da nake arayuwata ban tab’a ganin miskilin mutum irin Yarima ba, ko d’an yana tak’ama da mulki da kud’i ne oho”.

A cikin raina nake ta zancen ni kad’ai, Saima naga ta matsa tahau jere masa abin kari kala-kala ni wani girkinma ko ganin irinsa ban tab’ayiba bare ince na ci.

Da katar da ita yayi da hannu ba tare da yayi magana ba.

Ina ganin haka ‘ya’yan hanjina suka kad’a tsoro ya kamani ko wani laifin muka sakeyi.

“Kira Jakadiyya”.

Abin da kawai ya furta kenan ya cigaba da aikin sa ko ince sana’ar tasa.

Da rawar jiki na fice na tafi neman Jakadiyya, wata mata Ladidi na tambaya tasanar min tana b’an garen Fulani Sokoto ai kuwa can d’in na nufa.


Ina shiga na zube na kwashi gaisuwa wajen Fulani Sokoto, wani kallo ta watsomin kafin tace da Jadiyya.

“Wannan kuma fa?”.


“D’aya ce daga cikin ma aikatan Yarima”.


“Cikinsu har da yarinya irin wannan ?”.

“Ehh Yarinyarce suna fama da gararin talauci ne, tazo aikine domin su dunga samun abin da zasu ci”.

Sai naga Fulani Sokoto tayi murmushin da bansan ko na mene neba, araina ina tunanin meye yasa zatayi wannan maganar akaina?.

“Meke tafe dake?”.

Maganar Jakadiyya ta katse n i daga tunanin da nake, na bata amsa da fad’in.

“Yarima keson ganinki da gaggawa”.

Ta mik’e tana yiwa Fulani Sokoto sallama nima nabiyo bayanta, a hanyarmu ta zuwa b’angarensu Yarima ta dube ni tana fad’in.

“Ki iya takunki da kowa a gidan nan, ki kame kanki kada ki soma shiga abin da ba ruwanki, sannan kiyi taka tsan-tsan da al’amuran b’angaren Fulani Sokoto”.

Ni dai har tagama bayaninta ban fahimci komai ba, sabida tunani na yagama bani yau korata z’ayi kawai tuni na fara matsar kwalla.

Muna shiga ta zube a gabansa nima haka, Saima kuwa dama tana inda nabarta illa gani da nayi ta zubawa Yarima ido kamar zata cinyeshi


Bai ko kalli inda mukeba ya fara magana.

“Gaskiya wa ‘yannan basu san aikin su ba, in da dama acanja wasu”.

Jakadiyya ta russuna tana fad’in.


“Sunyi laifi ne ranka dad’e?”.


Ya tsuna fuska yayi kafin ya bud’e baki a hankali yana magana.

“Ya za’a ajiyemin breakfast ba tare da anshare ba?”.

“Ayi afuwa Magajin gobe, Kai kace a cire mutum d’aya, to laifi nawane aga farceni ban sanarwa Aynu gyaren falo ya dawo gare ta ba na mance ne wallahi”.

Kai kawai ya gyad’a alamun ya gamsu, yamik’e ya fice daga d’akin ya barmu nan zaune, Jakadiyya ta dubeni.

“Aikin kine Aynu share falon nan ki goge sosai kisa turare domin Yarima ma’abocin son k’amshi ne, ki kiyaye da kyau”.

“To ba damuwa”.

Haka kawai nace, domin ko bata gayamin ba na fahimci irin so da k’aunar da yakewa dangin turare, ta mik’e ta fice daga d’akin ta barmu ni da Saima, ita ma Saiman bayan ta gama kwashe kwanukan abincin tafice abinta tana fad’in.

“Idan kin gama zaki iya zuwa ki juye abincin nan nakine, domin kece kalar yunwa”.

Ta fice abinta nabi bayanta da kallo araina ina mai-maita kalmar.


“Kalar yunw? Kalar yunw?, Ehh gaskiya ni kalar yunwace kowa ya ganni zai san haka, to amma mai yasa zatacemin haka?, na d’auka duk wanda yazo aiki yazone domin nemana abin da zai ci ne ko?, ko kuma akwai masu zuwa aiki ne domin ra’ayi kawai?”.

Ganin bani da amsa dukkan tambayoyi na, kuma babu mai amsamin yasa na hak’ura nahau yin aikin dake gabana, duk k’ok’arina yau in koma gida da wuri domin inje islamiyya.


“Mama kina nufin Yarima Fudhal zaki nema wa auren Gimbiya Safiyya?”.

Cewar Jalil kenan dake zaune gefan mahaifiyyar tasa, murmushi tayi kafin ta bashi amsa.

“Ehh mana haka nake ganin shine mafita, bayan auren zan sanar maka shiri na na gaba”.

“Amma fa ni nake son tafa kin sani Mama!”.

“Kai fa sha-shane wallahi mutumin da ake nema masa hanyar sarauta mai zai yi da wata soyayya?”.

“Nasani Mama amma gaskiya banjin zan iya hak’uri da sonta”.

Murmushi tayi akaro na biyu kafin ta dube shi da takaici.

“Na zaci ko sanin kana sonta Gimbiya batayi ba?”.

“Ehh amma aike nake nufi ki gayawa Mai Martaba anema min aurenta”.

Fulani Sokoto dariya tayi mai sauti awan nan lokacin tana mai yiwa d’an nata kallon soko baka san abin da kake yi ba, amma a fili kuma cewa tayi.


“Amma kai dai baka da tunani ko kad’an Jalil taya Mai Martaba zaiyi maka aure ga yayan ka bai ko kawo maganar auren ba !, ka dai sake tunani amma ni maganata na gama”.

Jalil yayi shiru yana duban Mahaifiyar tasa batare daya sake furta ko mai ba itama haka.

Yarima Jalil suna matuk’ar kama da Yarima Fudhal ban-ban cinsu kawai shekaru da kuma k’asumbar fuska, Yarima Jalil shekararsa ashirin da bakwai kuma shi baya tara k’asumba a fuskarsa illa siririn sajen da yayuwa fuskarsa k’awanya, yayin da Yarima Fudhal ke da shekaru talatin aduniya ma’abocin tara suma ne ta kai da kuma fuska da suke shan gyara ko yaushe wanda hakan bak’aramin kyau yake k’ara masa ba.

Mik’ewa yayi zai fice bata dubeshi ba take fad’in.

“Ka kiramin Ladidi”.

“To”.

Kawai yace ya fice daga d’akin, a hanyarsa ta zuwa b’angaren sane ya gamu da Ladidin ya bata umarnin taje mahaifiyarsa na kiranta, shi kuma ya shige b’angarensu.

Fitowa ta kenan daga falon Yarima na gama gyarawa zan tafi mukayi karo da shi yana shirin shiga d’akinsa, durk’usawa nayi na gaishe shi bai amsaba sai k’uramin ido da yayi yana bina da kallo, na mik’e na wuce abina domin tunanina shima miskilin ne irin Yarima Fudhal.

Har sai da nak’ule ya daina ganina sannan ya shige d’akin nasa yana sosa k’ewa fuskarsa cike da murmushi kona menene ? oho.

Yau ban jira Zainab ba sabida saurin da nake, naje na juye abincin da Yarima ya bari acikin Viva nayiwa Jakadiyya sallama na tafi gida.
[09/07, 00:23] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©


06




Yauma kamar kullum haka na tadda shi kwance bisa katifarsa mai kama da gado ya lullub’e jikinsa da bargo mai taushi, hannunsa dake rik’e da waya kawai sune a waje yana danne-dannansa.

Naje na gaishe shi duk da baya amsawa amma hakan bai sa na dai na gaidashi ba sabida gudun yin laifi, na mik’e na wanke toilet na fito na sanar masa na gama.

Ya ziro k’afafuwansa ya saka takalmimsa yashige toilet batare daya kalli inda nake ba, ni kuwa na mik’e na kad’e ko ina na share na goge , na kalli agogo naga kusan awa guda kenan, araina nace.

“Wannan wane irin wanka ne?, mutum yayi awa guda a toilet kamar mai canja fata?”.

A fili kuwa na furta.

“Ko da yake komai na masu sarauta da ban ne”.

Jin motsin fitowarsa da nayi ne yasa na d’ebi tsin tsiya da abin mooping nayi falo, na cigaba da gyaran falon, na kusa gamawa sannan sai ga Saima ta shigo hannunta rik’e da tire bata ko kalli inda nake ba ta wuce inda Yarima ke cin abinci ta fara jere masa, ni kuwa na gaggauta tsaftace falon sabida kada ya fito yaga ban gamaba.

Allah kuwa ya taimakeni bai fito ba sai da na gama na d’auke komai sannan ya fito, shigar coat yayi fara har zuwa wando da agogon hannunsa da takalmi duk farare ne na fahimci dai baya son manyan kaya domin tun dawowarsa banga ya saka kayan nan k’asar ba.

Yaje ya zauna yana wani shan k’amshi, Saima ta jere masa dukkan nin abin da tasan zai buk’ata ta koma gefe ta zauna tana kallonsa, ni dai kaina ak’asa yake addu’a nake Allah ya rabamu dashi lafiya yau.

Cokali d’aya yayi na ruwan tea wayarsa dake hannunta tahau ringing ya d’aga yana mai sata free, domin duk muna jin abin da ake cewa a waya r sai dai bana fahimtar abin da suke fad’i domin yaren turanci naji sunayi ni kuwa kun dai san banko k’arasa primari ba bare ince zan ji turanci, Saima ce dai naga tana ta murmushi kamar tana fahimtar wani abu da yake fad’a a wayar.

Yana kashe wayar yamik’e ya fice, Saima ta tattara kayan da sauri ta fice da su tabarni zaune a falon nayi ta gumi ina wani tunani na da ban, sai kawai ji nayi andafa ni ta baya firgigit na juya domin ganin waye?, domin tunanina ya bani Zainab ce.

Ina juyawa sai naga sab’anin tunani na a she Yarima Jalil ne, na durk’usa da sauri na gaishe shi duk da fad’uwar gaban da nake fuskanta awannan lokaci.

Amsawa yayi yana mai cigaba da kallo na, ni kuwa kaina na k’asa cike da tsoro na furta .

“Ko kana buk’atar wani abu ne?”.

Kai kawai ya girgiza alamun a’a yana mai neman guri ya zauna yana fad’in.

“Ku nawa kuke yiwa Yarima aiki?”.

“Mu biyu”.

Na bashi amsa a gag-gauce, yad’an tab’e baki a hankali kafin yace.

“Kina jin dad’in aiki anan kuwa?”.

“Ehh”.

Na kuma bashi amsa.

Shiru ya gauraye d’akin na wani lokaci, nidai kaina yana k’asa Allah Allah nake insamu in fice daga d’akin, dan haka kawai nidai hankalina bai kwanta da al’amarin Yarima Jalil ba, ina cikin tunanin yanda zansamu in fice daga d’akin sai kawo jin hucin numfashinsa nayi a fuskata naja baya da sauri, bina yayi da kallo kafin yayi murmushi kawai ya fice daga d’akin, ajiyar zuciya na saki kafin in mik’e da sauri nima na fice daga d’akin har ina tun-tub’e.

A hanyata ta zuwa inda sauran ma’aikatan gidan ke zama insungama aiki naci karo da Zainab taa ganni duk a wani tsorace, jana tayi wani b’angare na gidan da ban tab’a sanin da shiba domin Zainab tasan ko ina a cikin gidan kuma kowa ya san ta.

Muka zauna ta rik’o hannunta tana tambayata.

“Lafiya Aynu?”.

Nayi shiru nad’an lokaci ina kallon wani gefe na wajen, kafin na dawo da kallona kanta na fara bata labarin abin da yafaru.

Zainab ta zaro ido waje tana fad’in.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, sai kinyi taka tsan-tsan da Yarima Jalil sosai wallahi”.

“Kamar yaya?”.

“Nasan baki san waye Yarima Jalil bako Aynu?”.

Tad’an rage muryarta k’asa-k’asa.

“To Yarima Jalil ya wuce dukkan tunaninki, ya ksance mashayin giya kuma manemin mata a cikin gidan nan duk wacce aka kawo aiki indai ta burgeshi to wallahi duk hanyar da zai bi sai yabi domin ta zama yarinyarsa, ma aikata uku aka zubarwa cikinsa, kuma aka kulle bakinsu da kud’i kada su fad’a babu wanda yasan haka sai mahaifiyarsa sai kuma Jakadiyya, domin ita ce ma take sanarwa Babah Tasallah lokacin dana fara aiki a gidan nan, ko Mai Martaba kansa bai san muna nan halin Yarima Jalil ba”.

Gumi ne ya ketomin ta gefan fuskata jin wannan bayani na Zainab nayi maza na goge ina fad’in.

“Ina hakan ma ba zata tab’a faruwa ba, babu dole sai in hak’ura da aikin”.

Dariya Zainab tayi kafin tace.

“Kina hauka kenan?, ai barin aikin ki bai ta soba domin ko kinbar aikin sai ya binciko inda kike kuma sai ya biki”.

“Wayyo Allah na to yanzu ya zanyi?”.

Nace da Zainab cike da tsoro, domin kunsan halina akwai tsoro kamar farar kura.

Zainab tayi shiru kafin tace.

“Ki kwantar da hankalinki ko Ummanki kada ki fad’awa, tun da Allah yasa ba aikin dare kike ba, ko kad’an kada ki bashi fuska iya kaci gaisuwa bazai tab’a saki wani aiki ba tunda yasan ba b’angarensu ki kewa aiki ba kawai dai ki iya takun ki a gidan nan”.

Shiru nayi ina duban Zainab kafin ince.

“Au dama akwai masu aikin dare ne?”.

“Ehh akwai koni da farkon zuwana aikin dare na farayi sai da Jakadiyya tayi magana na dawo safe”.

Aynu tayi ajiyar zuciya domin kalaman Zainab ya kwantar mata da hankali ya kuma bata kwarin gwiwa, har dai da taji batun bazai tab’a umartatta da wani aiki ba tunda ba’a b’angarensu take aiki ba taji dad’i sosai.

Nan sukayi ta hirarsu har Zainabu take sanarwa Aynu taji Yarima Fudhal yana fad’in zai fita shida abokansa sun shirya masa party na murnar kammala karatunsa lafiya.

Aynu tace “kaji illar wasu masu kud’inba, idan har murnar za’ayi da gaske mai zai hana ayi saukar al’qur’ani da walima”.

“Kema dai kya fad’a kinsan bakowa yake son abin da za’a fad’i abin da Allah da Manzonsa suka ce ba, al’amuran yahudawa yafi rinjaye a zukatan yawancin mutanen mu nayanzu, duk da cewa ba duka aka taru aka zama d’aya ba”.


“Haka ne, Allah dai yasa mu dace”.

“Amin ya Allah”.

Suka amsa baki d’ayansu da haka har lokacin ta shinsu yayi kowacce taje ta d’auki abincinta suka tafi gida.


*** ***

Filin wajen cike yake mak’il da jama’a maza da mata kowanne yana ji da kansa, domin kowa ka kalla a wajen za kasan kud’i ya zauna sabida daga d’an Alhaji da Hajiya sai d’an menister wane ‘yayan ‘yan kasuwanni da ‘yan siyasa sune suka cika wajen bakajin komai sai tashin kid’an turawa kala-kala da wannan ya katse sa kaji wannan ya d’ora, dare ne amma tamkar rana haka wajen yake sabida hasken daya haske wajen wanda shine ya basu kwarin gwiwar yin harkokinsu hankalinsu kwance.

Filin wajen kansa abin mamaki ne banda irin cikar da yayi, jerin motoci goma ne sukai layi a harabar wajen duka bak’ak’e ta tsakiya ce kawai fara, jikin lambar motar kowacce anrubuta Emirs 1 har zuwa 10.

Baki d’aya gurin yarud’e da ihun kiran sunan YARIMA FUDHAL.

Cikin takun k’asaita yafito kamar bazai iya taka k’asa ba yana wani shan k’amshi yayi shiga irin tasu ta sarauta kowa ya ganshi yasan Yarima ne wanda akeji da shi a gida da kuma waje, sauran abokansa suka take masa baya.

Waje na musamman aka ware masa shi da abokansa, hankalin ‘yan matan gurin nan kaf yayi kansa kowacce burinta tasamu shiga wajensa.

Bayan kowa ya natsa kuma aka buk’aci Yarima Fudhal yayanka cake, yamik’e fuskarsa cike da murmushi ya d’auki wuk’ar zai yanka, aka fara irga.

“One….two…..thr..”.

K’arar motar dake shirin yin parking a wajence ta katse kowa, dukkan hankulan jama’ar gurin ya koma kan motar.

Domin mota ce da duk wajen babu wand ya halarci gurin da ita mota ce k’irar Perrari mota mafi kyau da tsada.

Kowa burinsa a wajen yaga waye ma mallakin wannan motar?.

A hankali ta ziro shantaleliyar k’afarta da tasha dogon takalmi mai tsini yana da igiyoye wanda sune suka taimaka wajen rik’e k’afa fuwanta, shigar dake jikinta kuwa guwn ce pink da tabi dukkan jikinta ta d’ame, daga gaban rigar har zuwa k’asa yasha adon stone blue dark tayi rolling da mayafi k’arami shima blue.

Wayar dake hannunta ta d’orata bisa cinyarta X ce itama kalar takalminta blue, duk wannan bayanin da akefa bata fito da dukkan jikinta ba bare har mukai da ganin duskarta.


Ta shafe mintuna kusan biyar a haka kafin ta fito zuwa waje, anan ne fa dukkan nin mumfashin mutanen dake wajen ya kusa d’aukewa sabida kyakykyawar halittar da idanuwansu yayi tozali da ita, duk da bak’im glass d’in dake fuskarta daya rufe kusan rabin fuskarta, amma hakan bai hana ganin tsan-tsan kyawun halittar dake tattare da ita ba.

Cike da murmushi ta doso inda Yarima yake tana wani taku tare da rangaji kamar bishiyar da iska ke kad’awa.

Nidai tunani na banyi zaton zata iya taku da takalmin dake k’afar taba, amma sai naga tana tafiya kamar wadda tasanya silifas .

Bata tsaya ba sai da taje dai-dai inda Yarima Fudhal yake tsaye rik’e da wuk’ar yanka cake sannan ta tsaya jikinsu har yana gogar juna ta juyo tana k’arewa sauran mutanan wajen kallo kafin ta saka hannu ta cire glass d’in da yayiwa kusan rabin fuskarta k’awajen.


A fili na furta “SAIMA!”.
[10/07, 20:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*




NWA®


FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN)


07



A fili na furta “Saima !”.

Amma Yarima Fudhal kuwa tsaya wa yayi yana dubanta cike da mamaki tare da tunanin inda ya tab’a ganin fuskarta.

A hankali ta dawo da kallonta kan fuskar Yarima da ya tsare ta da shanyayyun idanuwansa yana nazari a kanta sosai, tunaninsa ya tsaya adai-dai lokacin daya tuna yatab’a ganin mai kama da ita awani guri.

Idan zai iya tunawa lokacin daya ba da umarinin a kira wo masa Jakadiyya ranar da ba’ashare falo ba, a lokacin bai zaci da mutum zaune ba yad’auka dukansu suka fita yana ta danne-dannan wayarsa ya d’ago kai bai zata ba suka had’a ido tayi saurin sauke kanta k’asa shine ganin da zaice yayiwa mai kama da ita.


“Wacece ke!”.

Bai san sanda ya samu kansa da jefa mata tambayar ba, bata bashi amsaba illa rik’o hannunsa dake rik’e da wuk’ar yan kan cake d’in da tayi ta fara irga, sai kawai gani yayi ta yanko cake ta nufi bakinsa da shi kau da kansa yayi gefe yana mai komawa inda yake a zaune ya zauna.

A dai-dai lokacin da aka k’ara sakin kid’a ana ciye-ciye da shaye-shaye, Saima ta koma kusa da shi ta zauna tana dubansa tare da zuk’ar lemon da ke rik’e hannunta, ta d’an basar kamar yanda taga yayi mata amma ta kasa jure shirun nasa ta gyara zama tana fad’in.

“Suna na Saima ‘yar gidan Alhaji Buba ‘yarsa tilo guda d’aya da akeji da ita tamkar kwai, nice first kuma nice last a gidanmu, bawai nazo wajen nan dan wani abu ba, nazone intayaka murnar dawowarka k’asarka lafiya sanna in sanar maka irin son da nake maka, sauran bayani zan baka numberta sai muyi magana a waya”.

Duk zubar datake ko kallon inda take bai yi ba, shidai burinsa kawai ya fita daga kokwanton da zuciyarsa takeyi masa, aransa yana fad’in.

“To idan wannan ‘yar gidan Alhaji Buban dana sani ce waccan kuma da take min aiki wacece?”.

Babu amsa domin maganar aransa yake yinta bai ko yi k’ok’arin tambayarta ba, sai ji yayi ta zare wayarsa dake rik’e a hannunsa binta kawai yayi da kallo kafin ya mai da kansa kan al’ummar wajen, sai da ta sanya numberta a wayarsa ta d’auki tasa a tata wayar sannan ta ajiye masa wayar a gabansa ta mik’e ta shiga filin rawa.

‘Yam matan dake wajen baki d’aya sun raina kansu, da had’uwa da kud’i irin na Saima, samari kuwa tuni sukayi ca a kanta kowa yana zuba mata kud’i, domin su sami shiga a wajen ta duk da sun saddak’ar ita d’in ta Yarima Fudhal ce.

Shidai Yarima bai ko taka inda ake rawar ba, har suka gama aka hau d’auke d’auken hotuna kuma.

11:30pm

Sai sha d’aya na dare aka tashi kowa ya nufi hanyar gidansu, Yarima ya dawo a gajiye wanka kawai yayi da sallah ya nemi makwancinsa ya kwanta, yana Allah Allah gari ya waye ya warwarewa zuciyarsa wasi-wasin da take ciki.


*** ** ***


7:30am.


Muryar Aynu ita ce tayi sanadiyyar ta shinsa daga dad-da d’an baccin da yake, domin da k’yar dama ya samu yayi sallar asuba ya koma, domin shi mutum ne da baya wasa da sallah ko kad’an, mik’a yayi tare da salati ya mik’e ya nufi toilet ba tare daya kula da gaishe shin da take ba, domin inda sabo yaci ace ta saba da halin Yarima.


Nan d nan sai gashi yafito falo Aynu ta cika da mamakin shirya warsa da wuri haka yau, lokacin Saima na zaune ta gama jere masa abincin, zama yayi yana mai k’urawa Saima ido, sai dai wani abu daya rud’ar da shi akan Saiman jiya da wadda take masa aiki shine.

Wan nan bak’ace waccen kuwa farace sol kamar a tab’a fatarta jini ya zubo duk da manyan idanuwansu yazo d’aya, sannan kuma ta jiya tana da hip sab’anin wannan siririya.

“Ke ! mik’e tsaye”.

Sukaji saukar muryarsa akunnu wansu da sauri suka mik’e duka, sai kuma ya tuna ai ta jiya ta sanya dogon takalmi ne bazai iya tan-tance tsayunsu ba.

“Mene sunanki?”.

“Ay….”.

Aynu tabud’e baki zatayi magana yakatseta da fad’in.

“Ba ke ba “.

Ba tare daya dubeta ba, domin idonsa na kafe kan Saima kawai.

Tayi shiru abinta tana kallon ikon Allah yau.

“Saima “.

Ta bashi amsa, sai yaji muryar Saiman jiya tafi siririya akan ta wannan, kai ya girgiza yana fad’in

“Sunan ne yazo d’aya tare da kama kenan?”.

A fili yayi maganar yayin da Saima da Aynu suka dubi juna, Saima ta jefawa Aynu wata muguwar harara, Aynu kuwa ta mayar mata da murmushi.

Mik’ewa yayi ya fice ba tare daya bi takan abincin nasa bama.

Kai tsaye shashin mahaifiyarsa ya nufa, ya sameta tana bada umarnin wasu abubuwa a gidan neman guri yayi ya zauna yana mai gaishe da mahaifiyyar tasa yayin da ma aikanta suka gaishe da shi, bai amsa ba suka mik’e duk suka fice.

Sai yayi shiru kuma yana jujjuya wayarsa a hannunsa, kallonsa Fulani Bingel ta tsayayi tana karantar yanayinsa.

“Lafiya Magaji?”.

A jiyar zuciya yayi kafin ya fara magana.

“Hajiya dama a kwai mutanen da zakiga basu san junaba basu had’a wani relation ba amma kuma kiga suna kama sosai?”.

Fulani Bingel tad’anyi dariya tana fad’in.

“Magaji kenan ! to ai ko wanne mutum da kagani akwai copy d’insa bakwai a duniya, wani abune ya faru kake wan nan tambayar?”.

“A’a babu komai”.

Abin da yace kenan bai sake magana ba, yamik’e ya shiga b’an garen Kakarsa Mai Babban d’aki, anan yayi breakfast d’insa bai bar wajen taba sai k’arfe biyu da aka kira sallar azahar ya fito ya tafi masallaci, kafin ya dawo su Aynu tuni sun gama aikinsu sun nufi gida, ya shige d’akinsa ya kwanta abinsa.


***

BAYAN SATI GUDA !.


Sati guda kenan da had’uwar Saima da Yarima Fudhal kullum tana zuba ido taga kiransa a wayarta, amma girman kai da jiji da kai ya hana ta nemeshi ita, yayin da shi kuma yama mance da al’amuranta domin shi mutum ne da baya son sanya abu aransa domim yan zunnan sai abin ya nemi ya zame masa matsala tunda ya samu Mahaifiyarsa tayi masa bayanin ana samun copy d’in mutum bakwai aduniya shikenan domin dama kokwan tonsa ko ta zo aiki gidanne sabida wani nufi nata amma yanzu zuciyarsa ta bashi waccen Saiman daban wadda ke masa aiki daban.

B’angare guda kuma kwana uku kenan Aynu batazo aiki ba sabida Ummanta dake kwance babu lafiya, sai dai ta fad’awa Zainab ta sanar a gidan sarki kada aga bata zuwa, Jakadiyya tace babu komai taje ta sanarwa Yarima shima cewa yayi ba damuwa sannan ya ciro dubu biyar yace a bata su sai magani Jakadiyy da kanta ta kai musu gida domin macace mai kirki da rik’on gaskiya da amana.

A rana ta biyar ne Aynu taga jikin Mahaifiyar tata yayi sauk’i ta shirya tace zata koma aiki ta yima Ummanta sallama da Babanta ta tafi.

7:30am.


Bakwai da rabi na safe kamar yanda ta saba ta isa gidan, bayan taje ta gaishe da Jakadiyya ta gaida Fulani Bingel kai tsaye kuma b’angarensu Yarima ta nufa.


Tana shiga taga Naja ta fito daga d’akin Yarima Jalil da alamun rashin gaskiya a fuskarta, Aynu tayi kaman bata ganta ba ta wuce d’akin Yarima.

Kamar yanda ta saba batayi tunanin komai ba tasa kai cikin d’akin, yanda ta ganshi ne ya sata zubewa bisa gwiyoyinta ta runtse idonta k’am jikinta na faman b’ari kamar mazari.

Ta mudubi ya ga shigowarta a fili ya furta.


“Ohhh my God !”.

Yana mai dafe goshinsa.
[17/07, 16:25] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


SADAUKARWA:- Namesy ta Pheerdauceey Jeebour.


Amma wannan page naki ne SAFIYYA GALADANCHI Allah yabar zumunci.


08





“Ohhh my God !”.

Ya fad’a yana mai dafe goshinsa.


Aynu kuwa tuni hawaye ya fara zarya a kan kuncinta harta saddak’ar yau aikinta yak’are a gidan.

“Wanne kuskure tayi da har ta shigo ta taddashi a wannan yanayin?”.

Tayi tambayar cikin ranta.

“Sallama !, Ita ce kuskuren da nayi da a ce nayi sallama da ban shigo na same shi a haka ba, da yayi k’ok’arin kintsawa kafin shigo wata, ko ya da katar dani harya suturce jikinsa”.

“Wayyo Allah na !”.

Ta fad’a a fili kuma da k’arfi wanda har sai da Yarima Fudhal dake k’ok’arin suturce jikinsa ya juyo yana dubanta, wannan shine karo na farko da Yarima ya tab’a duban fuskar Aynu tun zuwanta gidan aiki, gabansa ya buga dammm, yayi saurin d’auke kai yana mai ci gaba da sanya rigarsa tare da tunanin yanda a kaima tazo ta taddashi a haka, aransa ya furta.

“Kuskure na ne !”.


MINTUNA TALATIN DA SUKA WUCE


Kasancewar Aynu ta daina zuwa aiki kwana biyu sabida jinyar Ummanta, sai aikin wankin toilet da shara ya koma hannun Saima duka.

Yau ya tashi yajishi a gajiye ga kuma gumi da yaji yanayi duk da sanyin AC da ke d’akin amma hakan bai hana shi jin zafi ba, ha kan ne yasa ya nufi toilet domin watsa ruwa.


Sai dai Yarima nada wata al’ada guda d’aya, kasan cewarsa mai tsafta da kuma kyankyami shiyasa ko kad’an baya iya barin abu jik’ak’k’ema ajikinsa yana fitowa daga toilet yake wurgi da towel d’insa sannan ya nemi wani ya d’aura ko ya bari ya gama shafa mai da koma kafin ya suturce jikinsa, sabida ya san babu mai shigo masa d’aki sai da izininsa hakan ya kuma zame masa jiki sosai, to yauma a hakan ne Aynu ta shigo ta tadda shi.


Yana gama sanya rigar ya sake dawo da dubansa kan Aynu da jikinta ke ta tsuma tana jiran saukar duka ko wani mugun hukunci daga Yarima.

Zama yayi gefan katifarsa yana fad’in.

“Ke !, zo nan”.

Aynu ta rarrafa da jan gwiwa ta k’arasa inda ta jiyo muryarsa idonta har lokacin a kulle bata bud’e ba, cike da tsoro ta haufad’in.

“Kayi hak’uri ka gafarce ni dan Allah !, wallahi tallahi banyi zaton zan tadda kai a haka ba Allah, dan Allah kada ka kore ni da wannan aikin muka dogara nasha wuya kafin in same shi amma….!”.

Kuka ne yaci k’arfinta ba tare da ta iya k’arasa mganarba ta mak’ale a mak’oshinta.


Yarima kuwa murmushi yayi yana mai k’arewa halittarta kallo yayin da yakeji bugun zuciyarsa na k’aruwa sosai amma yana jin da d’in kallon nata sosai, musamman yanda take sarrafa leb’anta wajen magana, sai zara-zaran gashin idonta da suka jik’e da hawaye duk da bai ga idon nata ba.

“Bud’e idonki babu abin da zanyi miki”.

Yayi maganar yana mai kafe idanuwansa bisa nata.

Aynu ta hau bud’e idonta kad’an-kad’an wai dan kada ta kuma ganinsa a yanda ta ganshi d’azu, tana gama bud’ewa sukayi ido biyu da shi, tayi saurin sauke idonta tana mai rissi nawa da fad’in

“Nagode sosai, Allah yak’ara girma”.

“Amin”.

Da sauri ta d’ago kai ta dubeshi sabida mamakin yau karo na farko tayi magana ya mayar mata, murmushi kawai ta ga yayi mata, ta d’auke kanta tana mai shigewa toilet din domin wankewa.

Mintuna kad’an ta fito ta taddashi a inda tabarshi illa wayarsa dake hannu yana daddan nawa, yanaji ta fito ya d’aga kai yana binta da kallo har ta zo ta durk’usa tana sanar masa ta gama.

Mik’ewa yayi ya fice bai ce da ita komai ba, yana fita Aynu tayi ajiyar zuciya domin ita kanta kallon da yake mata ya fara bata tsoro sosai, ji take aranta kamar hukuncin da zai yi mata yake shiryawa.

Ta gama komai ta fito falo ta taddashi zaune, amma wannan karan ya akiye wayar gefansa yana kallon ball a TV, gefe guda kuma Saima ce zaune Aynu na fitowa ta hau aika mata sak’on harara ita kuwa bama tasan tanayi ba, ta fara k’ok’arin gyara falon duk abin da ta keyi idon Yarima akanta shi kansa bai san dalilin da yasa yau d’aya yanajin dad’in kallon yarinyar sosai, komai takeyi a nutse cikin sanyi kuma hakan na burgeshi sosai.


Sai da ta gama komai yau duk yana zaune, sannan Saima tazo ta jere masa kayan Breakfast d’insa, yana ci yana faman kallom Aynu yayi mamakin irin abincin da yaci yau sosai, ya gama Saima takwashe kwanukan ta fice tabar Aynu nan zaune.

Zaman duk ya gun dureta ga kallon da Yarima Fudhal keta jifanta dashi domin lokaci-lokaci data d’ago kai sai sun had’a ido baki d’aya jinta take yau duk a takure sai take tayin data sanin zuwanta aikin ma yau baki d’aya.


“Mene sunanki?”.

Taji tambayarsa ta jefi kunnuwanta, ta d’an gyara zama tana fad’in.

“AYNU”.

“Aynu kuma?, ci kakken sunanki nakeson ji”.

Ajiyar zuciya tad’anyi kafin ta bashi amsa.

“AYNUL-HAYAT”.

Ta fad’a tana mai gyara zamanta da kyau domin ji tayi k’afafuwanta duk sunja jini sunyi wani iri babu dad’i sabida zaman d’urk’ushen da tayi.


“Aynul-hayat !”.

Taji ya mai-maita cikin wata irin murya da ta sanya tsigar jikinta tashi, ta d’ago kai akaro na biyu ta dube shi shima ita d’in ya kafe da idanuwa ya jefe ta da murmushi kafin yace.


“Nice Name”.


Tayi saurin sauke idonta yayin da bugun zuciyarta ya cigaba da k’aruwa, aranta tana fad’in.


“To me ya zauna yi yau ayanda nasan shi da yana gama cin abinci yake ficewa zuwa wajen Kakarsa ko Babarsu amma yau ya wani zauna ya tsare mutane”.

A fili kuwa ita ma murmushin ta d’anyi duk da bai kai zuci ba.


“Beautiful smile”.

Taji yak’ara fad’a ita ta d’auka ma waya yake da turawa dan bata fahimci mai yake fad’i ba.


Mik’ewa yayi ya shige bedroom d’insa mintuna kad’an sai gashi ya fito sanye da jeans bak’i da T.sheet blue yayi kyau sosai, yazo yad’an rage tsayinta akanta yana fad’in.


“Aynul-hayat !”.

Taji gabanta ya fad’i, ta d’ago kai ba tare data amsa ba, shima bai da muba ya cigaba da fad’in.

“Yaushe kuke tafiya gida?”.

“K’arfe biyu ko biyu da rabi”.

“Ok”.

Abin da yace kenan ya kama hanya ya fice ya barta nan zaune tana tunanin abubuwan da suke faruwa da ita yau.


“AYNU”.

Ta sake jin muryarsa ta daki kunnuwanta ta juyo da sauri sai taga ashe Yarima Jalil ne tsaye bakin k’ofa ya nad’e hannuwansa bisa k’irjinsa yana jifanta da wani mugun murmushi.

Gaishe shi tayi ya amsa yana fad’in

“Mai yasa bakyason sakin jiki da ni, da zaran kin ganni sai kin tsora ta?”.

“Babu komai”.

“Da wani abu mana fad’i gaskiya dai?”.

Ji yayi andafa kafad’arsa ta baya ya juya da sauri sai yaga ashe Yarima Fudhal ne ya kuwa had’e girar sama data k’asa, ya dubi Aynu yana fad’in.

“Ke…!, tashi ki fita”.

Sum-sum Aynu ta fice dama neman hanyar fita ta keyi, Yarima Jalil kwafa yayi yana cijen lab’e yabar k’ofar d’akin, domin yasan yanzu kome zai yi Yarima Fudhal bazai kulashi ba kuma ba zai tsaya suyi maganar arzik’iba tunda ya d’aure fuska.




Assalamu alaikum

Nagode sosai ‘yan uwa da abokan arzik’i abisa addu’arku agareni Allah yabani lafiya sosai, masu inbox zuwa call da message ina godiya Ubangiji Allah yasaka da alkhairi amin.

Zaku cigaba da jina insha Allahu kamar ko yaushe.
[18/07, 18:08] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namesy ta Pheerdauceey Jeebour.


Wannan page naki ne Tawan ta hannun damana HAFSAT M. ki morewa abinki.



09


Aynu na fita can baya taje ta samu waje babu kowa ta zauna abinta tana nazari a kan abubuwan da suka faru, a haka Zainab ta tadda ita.

Neman guri tayi kusa da Aynu ta zauna tana tambayarta “lafiya kuwa?”.

Aynu bata ji komai ba ta kwashe dukkan abin da ya faru ta sanar da ita sai dai ta b’oye abu guda bata fad’a mata ba, wato ganin da ta yiwa Yarima wanda aganinta bai dace ta fad’awa kowa ba.

Zainab tace.

“Haba Aynu wannan d’an abin shine kuma abin da zai ta da hankalinki, ki kwantar da hankalinki wallahi babu abin da zai faru insha Allahu”.

Nan dai tayi ta jan Aynu da hira har ta samu ta war-ware daga damuwar da take ciki, kafin su mik’e su koma ciki domin k’arasa ayyukansu, Zainabu tayi b’an garen Fulani Bingel ita kuma ta nufi b’an garensu Yarima.


***

“Ni kuwa mai Martaba dama akwai wata shawara da nakeson baka akan Magaji !”.

Mai Martaba dake kishin gid’e kan kusun ya d’an sake gyara kwanciyarsa, Fulani Sokoto ta mik’o masa yan kakken tufa d’in da yake ci yakarb’a ya kai bakinsa yana fad’in.

“Ina jinki, wacce shawara ce wannan?”.

“Kan batun auren Magaji da kake taso yayi shi kuma kaga har yanzu baice komai ba, wata k’ila baiga wacce yake so ba, shi ne nace mai zai hana anema masa auren Gimbiya Safiyya !”.

Mai Martaba yayi shiru yana duban Fulani Sokoto cike fa nazari bisa maganar da tayi yanzu can ya gyad’a kai yana fad’in.

“Shawara mai kyau Safiyya ‘yar Sarki Maina yarinyace mai tarbiya ai babu wanda zai ganta yace batayi masaba, gaskiya naji dad’i sosai akan wannan zab’in da kika yiwa d’an namu”.

“Mai Martaba kenan ai nima d’ane a wajena inda abin da yafi hakama zanyi masa”.

“Gaskiya ne aikuwa zamuje nema masa aurenta batare da b’ata lokaci ba”.

Tuni wani sanyin dad’i ya ziyarci zuciyar Fulani Sokoto domin tarkonta ya kama, addu’arta d’aya Allah yasa kada ta samu matsala da Yarima Fudhal kuma?.

***


Kwance yake falo kan d’aya daga cikin kusun d’in dake falon rawar sanyi yake sosai amma ya kasa tashi ya nufi d’aki ko ya nemi abin da zai rufa dashi gashi wayarsa ma tana cikin d’akin, bai jin zai iya d’aga ko da dai-dai da yatsansa d’aya bare ya bud’e baki yayi magana.

A haka Aynu tayi sallama cikin falon ta taddashi, k’ara sawa tayi da zauri zuwa inda yake tana tambayarsa lafiya? ganin da tayi jikinsa sai rawa yake yasa ta fahimci cewa sanyi yakeji.

Mik’ewa tayi ta nufi d’aki ta d’auko masa k’aton bargon da yake rufa dashi ta zo ta rufa masa sannan ta koma ta fara aikin ta mintuna kad’an da gama wankin toilet tana gyara cikin d’akin ta dinga jiyo kakarin amansa, ta fito zuwa falo taga yayi aman bisa carpet ne kawai amma ban da jikinsa .

“Ko inkirawo maka Yarima Jalil ne?”.

Kai ya girgiza mata alamun a’a, Aynu tayi shiru tana dubansa shima ita d’in yake kallo.

“Ko a kira Hajiya?”.

“Bana buk’atar kowa”.

Abin da yace da ita kenan kawai, tayi shiru na tsawon lokaci kafin ta sake fad’in.

“To koma d’aki in gyara falon”.

Dubanta ya tsayayi yana k’ok’arin bud’e bakinsa domin yin magana amma kuma maganar tak’i fita, a hankali ya dafa bango ya mik’e yana tafiya har ya isa d’akin toilet ya wuce ya watsa ruwa a daddafe tare da wanke baki ya fito ya sanya jallabiya ya kwanta.

Aynu ta gyare falon tas tasanya turare aranta tana jin tausayin Yarima domin tasan bak’aramin ciwo ne zai kwantar dashi har haka ba.

Lokaci-lokaci takan lek’a tayi masa sannu ta dawo ta cigaba da aikinta, sai da ta gama komai sannan ta koma ta tambayeshi koyana buk’atar wani abune?, Ruwan tea kawai ya buk’ata ta kawo masa.

Lokacin k’arfe bakwai da mintuna arba’in da yake tazo da wuri yau burinta bai wuce ta samu ta koma gida da wuriba sabida wani dalili nata.

Kitchent ta nufa ta sanar da buk’atar Yarima nan da nan aka mik’o mata flast da cofuna da sauran tarkacen kayan tea.

A gabansa ta ajiye ta zuba masa ruwan tea d’in kawai da sugar domin yace baya buk’atar komai da k’yar yamik’e ya karb’i tea d’in yana sha, ita kuma ta fice daga d’akin ta nufi wajen Fulani Bingel wato mahaifiyarsa domin ta sanar da ita halin da yake ciki.


Tare suka tawo da ita da sauran ma’aikatanta, sukayi masa sannu suka fice ni dama falo nayi zamana muna shigowa, Yarima Jalil ne ya shiga yayi masa sannu shima ya fito ya koma d’akinsa, cikin k’ank’anin lokaci ciwon Yarima Fudhal ya bazu ko ina sai faman dubiya ake zuwa abin har ya bani mamaki, sai na tuna da ni kaina idan zamuyi wata nawa muna ciwo sai wanda ya zama dole yake zuwa dubamu, Allah sarki arayuwa idan a kace kud’i da mulki angama komai.


Fulani Bingel ta jima a tare da shi komai ta tambayeshi yana so sai yace A’a daga k’arshema cewa yayi baya buk’atar masu zuwa duba shi suna k’ara masa ciwo ne, mu dai muna zaune falo munyi jugum, can sai ga Fulani sokoto tazo duba shi sai da tak’are mana kallo tana wani yatsina sannan ta wuce ciki.


Tare suka fito da Fulani Bingel tana fad’in.

“Aynu ki kula dashi yace baya buk’atar kowa likita zai zo nan da anjima ya dubashi “.

“To angama Fulani”.

Abin da nace kenan na koma na zauna, Fulani Sokoto ta bini da wani mugun kallo tana mai ficewa, suma sauran ma’aikatan suka takewa Fulani Bilgel baya suka fice, suka barni ni kad’ai zaune falo kamar wata mayya.


Har doctor yazo ya dubashi yayi masa allurai sannan ya kirani yayimin bayanin magun-gunansa da yanda za’a dinga bashi ya tafi, na nemi guri na zauna ina kallon yanda yake fitar da numfashi da kyar hucin zafin jikinsa kuwa ina daga inda nake ina jiyo zafin.


Ganin alamun yana magana nayi na k’arasa da sauri zuwa dai-dai kansa domin idan ba haka kayi ba ba zakaji mai yake cewa ba, sai ji nayi ya kamo hannuna yarik’e kam ya had’a da hannusa, har sai da naji zafin rik’on ga kuma zafin jikinsa, a haka na zauna ina kallon ikon Allah domin da nayi k’ok’arin janyewa zai hud’e ido yana girgiza kai alamun kar incire, araina nace.

“Sai kace wani k’aramin yaro, kome yake damunsa ma oho?”.


A haka har bacci mai nauyi ya d’aukeshi sabida allurar da akai masa na samu na cire hannuna na dawo falo na zauna ina kallom TV films d’in india ne ake duk da bana fahimtar abin da suke cewa amma kallon yana min dad’i sosai, na jima a zaune sai ga Yarima Jalil ya shigo ya zauna na gaishe shi yana tambayar mai jiki nace.

“Yayi bacci ma”.

Da haka yayi ta jana da hira jefi-jefi har na mance a tare da waye nake ga Yarima Jalil akwai ban dariya tuni na ware yana bani labaran abin dariya ina dariya, abin da yake burgeni dashi kenan ba ruwansa da girman kai illa abu biyun da sukaiwa rayuwarsa illa ban dasu na fahimci Yarima Jalil na da kirki sosai har yafi Yarima Fudhal ma anawa ganin kenan.


Ya gama bani wani labari ina cikin dariya sai ganin mutum kawai mukayi a kanmu kamar mala’ikan mutuwa haka muganshi a tsaye.

Yarima Jalil ya washe baki yana fad’in.

“Sannu broda ka tashi kenan, ya k’arfin jikin?”.

Idan TV d’in dake d’akin tayi magana to shima yayi magana, nima na durk’usa inayi masa sannu wani kallo ya watsomin daya sanya hanjin cikina k’ullewa ba k’aramin k’ok’ari nayi ba wajen rik’e fitsarin da yayi shirin zubomin a wando.
[19/07, 17:42] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:- Namesy Pheerdauceey Jeeebour



Wannan page d’in naki ne FIRDAUSI SODANGI A cigaba da suburbud’a mana cakwakiyar KWAD’AYI MABUD’IN WAHALA muna tare da ke har zuwa inda al’kalamin ki zai tsaya.


10




Na mik’e tsam na koma waje guda na zauna ina jiran umarninsa.

“Sannu Broda Allah yak’ara lafiya”.

Cewar Yarima Jalil kenan yana mai ficewa daga d’akin.

“Ke zo nan”.

Na mik’e da sauri na k’arasa wajensa ya kafeni da sexy eyes d’insa da bana iya juran kallonsu, ya jima a haka kafin ya bud’e baki ya fara magana.

“Kada insake ganin ki tare da Jalil”.

“To”.

Na sake mik’ewa na nufi cikin d’akinsa na d’auko magun-gunansa na d’auko ruwa a robar faro na kawo na ajiye, ina mai b’alli maganin na mik’a masa ya karb’a yasha ya jawo kusun ya koma ya kwanta, sai lokacin na lura k’arfe biyu tayi ashe dubansa nayi ina fad’in.

“Zan iya tafiya?”.

Bak’aramin k’arfin hali nayi ba wajen tambayarsa domin bansan amsan da zai bani ba.

Kai kawai ya d’agamin alamun ehh, na mik’e da sauri ina k’ara yi masa Allah sauwak’e na fice daga d’akin duk da ban juya ba amma nasan ni yake kallo.

Kitchen na nufa kai tsaye naje na juye abincin nayiwa Jakadiyya sallama na tafi gida, araina ina tunanin rashin zuwan Saima yau.

“Ko da yake jiki da jini a kace”.


***

5:00pm


“Assalamu alaikum wai Aynu tazo”.

Aynu dake shara tsakar gidan ta ajiye tsin-tsiyar tana tambayar.

“Waye ya aiko ka Mallam?”.

“Ya Sayyadi ne fa na Islamiyya !”.

“Au kace ina zuwa”.

Yaron da ta kira da Mallam ya fice domin isar da sak’onta.

Aynu ta shige d’aki ta d’auko hijab d’in islamiyyarta tana mai duban Ummanta.

“Umma bari inje wai Ya Sayyadinmu ke kira na”.

“To sai kin dawo a kula dai da kyau”.

“To Ummata”.

Aynu ta sanya ta mutsats-tsan silifas d’inta ta fice.

Yana tsaye jikin bishiyar darbejiyar k’ofar gidan, fari ne d’an siriri mai doguwar fuska sai saje bak’i da yayiwa fuskarsa k’awanya da ka ganshi ka ga tsan-tsan bafulatani, yana sanye da jallabiya fara har k’asa da hula fara da ake kira tashi ka fiye naci.

Aynu ta k’arasa wajensa fuskarta cike da fara’a kamar yanda tasa take, ta d’an rissina ta gai dashi ya amsa yana fad’in.

“Malama Aynu kwana biyu na jiki shiru bakya zuwa makaranta?”.

Aynu ta d’anyi murmushi tana mai gyara tsayuwarta tare da fad’in.

“Wallahi Ya Sayyadi aikin dana samu ne sai a hankali, ban cika da wowa gida da wuri ba”.

“To ikon Allah adinga dai daurewa ana zuwa”.

“Insha Allahu kuwa”.

Zuwan Babanta dake shirin shiga gidan ya ka tsesu daga tattau nawar da suke, Ya Sayyadi ya durk’usa ya gaishe da Babanta cikin girmamawa, shima ya amsa fuskarsa fal farin ciki ya wuce ya barsu nan, yana shiga gida Ya Sayyadi yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta koma cikin gidan.


Tana shiga taji Ummanta da Baban nata suna tattaunawa akan Ya Sayyadin ita dai bata tsaya taji mai suke fad’iba ta cigaba da aikinta ganin babu wanda ya sakota a zancen.


*** *** ***

Yaune ta kama ranar da za’a fara biyan su Aynu albashi, tun asuba ta tashi zuciyarta fes cike da nishad’i, nan da nan ta kammala komai nata na gidan kafin k’arfe bakwai da yake Zainab ta bata wani k’aramin agogo da shi take amfani, bakwai nayi taci abinci tayi komai ta kama hanyar zuwa gidansu Zainab domin su tafi tare.

Tana isa ta tadda itama ta gama shiryawa suka kama hanya.

Yau dai ta tadda Yarima Fudhal ya war-ware tsaf har ya tashi yayi wanka ya shirya yana zaune gefan katifarsa ta taddashi, ta durk’usa ta gaishe da shi ya amsa fuskarsa cike da fara’a, ta mik’e ta nufi toilet ta kama aikinta.

Tana fitowa ta cigaba da sauran gyare-gyarenta k’arfe takwas akai kiransu za’a bawa kowa kud’insa na aiki.

Su nasu b’an garen har k’ari suka samu daga dubu goma sha biyar zuwa a shirin ba k’aramin dad’ine ya rufe Aynu ba sosai tana tafe tana lissafin abubuwan da zasu siya sai ji tayi taci karo da mutum taja baya da sauri tare da d’ago kai sai taga ashe Yarima Fudhal ne, ya kuwa had’e fuska kamar bashi ne ta ganshi d’azu cikin fara’a ba.

“Bani kud’in !”.

Yayi maganar babu alamun sassauci, jiki na b’ari ta mik’a masa yasake kallonta yana fad’in.

“Jeki kawomin breakfast”.

Ba musu ta juya ta nufi kitchent domin cika umarninsa.


Haka tayi ta zaryar shirya masa breakfast sai da ta gama ta had’a mai komai ta mik’a masa sannan ta koma gefe tana jira ya gama, komai baya wuce cokali d’aya zuwa biyu yake ci ya gama ta kwashe kwanukan ta mayar ta dawo ta zauna kenan yace taje ta kawo masa fruit, haka ta sake mik’ewa taje ta kawo, ta kuma zauna a gefansa yana daga kishingid’e tana yankawa tana mik’a masa yana sha, musamman apple ta fahimci yana cinsa sosai.

Sai da ya gama ta kwashe ta mayar ta dawo ta zauna ta jira taji yace ga kud’inta ta tafi, amma taji shiru gashi tana jin nauyin tambayarsa sai dai ta dubeshi kaman zatai magana sai taji ta kasa.


Sun jima a haka kafin yamik’e ya shige cikin d’akinsa, ya barta nan zaune tana tufka da war-wara.


“Aynul-hayat !”.

Taji ya kira sunanta ta amsa a hankali tana mai nufar d’akin nasa da sallamarta ta sanya kai d’akin.

“Zo nan”.

Ya kuma kiranta ta k’arasa inda yake a zaune gefan katifa ta durk’usa tana kallon ikon Allah.

Kud’ine dank’am a gabansa tun daga dollar zuwa dubu-dubu d’ari biyar-biyar ‘yan d’ari biyu har zuwa kan naira biyar kowanne bandir-bandir.

“D’ebi duk yanda ki keso”.

Aynu ta saki baki tana dubansa, sai take ganin abin kamarma wasa yake mata.

“D’ebi mana”.

Ta kai hannu kan ‘yan goma ta d’auka, dariya ya d’anyi yana fad’in.

“Sarkin tsoro”.

Karb’a yayi ya d’auki bandir d’in ‘yan dubu ya mik’a mata, girgiza kai tayi alamu a’a, shiru yayi Yarima yana dubanta cike da mamaki fal cikin ransa.

“Kyauta tace a gareki karb’i”.

“A’a nidai ka bani kad’an, sunmin yawa wad’annan”.

Jujjuya kud’in yayi tayi na wani lokaci kafin yayi murmushi yace.

“To idan na k’ara miki goma akan naki zaki karb’a?”.

Shiru tayi ba tare da ta ce dashi komai ba, ya irgo dubu talatin ya mik’a mata ta k’i karb’a.

“Idan baki karb’i wannan ba sai dai ki rasa kud’in naki duka”.

Aynu ta dube shi da sauri ya gyad’a kai alamun da gaske yake, hannu biyu ta sanya ta karb’a tana yi masa godiya, yace baya buk’atar godiya nan da nan taja bakinta ta tsuke.


***


Aynu ce zaune gaban Ummanta tana faman lissafin abin da ya kamata su saya, Ummanta ta murmushi tayi tana fad’in.

“Aynu kenan !, to ai duk lissafin da kike kud’in ba zasu kai ba sai dai asayi abin da ya samu kawai”.

“To Umma amma dai ya kamata musayi atamfa ko ta dubu d’aya da d’ari biyu ce, sai a asiyawa Baba yadi shi kuma ya d’inka, sauran sai mu sayi takalma da ta barma ko?”.


“Uhmmm yanzu dai d’auki dubu biyu ki kaiwa mai shagon da muke karb’o sabulu, ki bashi dubu kud’insa ne da yake binmu, dubu d’ayan kuma ki siyo silifas ki sayo mana sabulun wanka da wanki tare da makilin”.

“To Ummata”.

Ta fad’a tana mai mik’ewa tare da d’aukan kud’in ta fice.

A hanya ta gamu da Ya Sayyadi suka gaisa yana fad’in.

“Ina zaki haka da rana tsaka?”.

“Ummata ce ta aikeni”.

“To masha Allahu muje in taka maki”.

Haka suka tafi suna hira jefi-jefi har zuwa shagon tayo siyayyar suka dawo tare har k’ofar gida ya rakota sukai sallama ya tafi.

A ranar dai aka siyawa Aynu sabon hijab da atamfa Daviva guda biyu suka sayi sabuwar tabarma da ‘yan kwanuka da cofuna domin nasun duk sun lalace.

Aynu sai jinta take kamar sun shiga wata sabuwar rayuwa, jinta take kamar ba ita ba yau ita ce da sabon d’inki abin da sai dai abata kwance yau kuwa gashi ta d’inka da guminta.

“Alhamdulillahi, Alhamdulillahi ala kulli halin !”.

Abin da take ta faman mai-mai tawa kenan cikin ranta cike da nishad’i da jin dad’i.



7:40am

Yau dai Saima ta rigata zuwa gidan, sabida yau ta makara sosai ko da ta gaishe da Yarika k’in amsawa yayi bata damu ba domin tasan halin sa, tayi dukkan abin da ta saba ta gama ta nemi guri ta zauna, har lokacin ko kallonta bai yiba gefe guda kuma ga Saima sai faman wani ciccika take tana batsewa da zaran sun had’a ido da Aynu ta jefe ta da harara.

“Zaku iya tafiya”.


Suka ji muryarsa yana basu umarni, ko wacce tamik’e ta fice daga d’akin a hanyane Aynu ta dubi Saima tana fad’in.

“Kwana biyu bakya zuwa har anyi albashi….”.

Bata k’arasa maganar ba Saima ta katseta da fad’in.


“Ke kud’in ya dama”.

Ta wuce ta barta nan tsaye tana searching d’in maganar Saima.

“Me take nufi da ni kud’i ya dama?”.

Kafin ta kai da bai wa kanta amsa sai ganin Yarima Jalil tayi a gabanta fuskarsa fal murmushi yake fad’in.

“Beauty kin b’uya !? ko da yake naga Yayan namu baya buk’atar ganinmu tare”.

Aynu ta tsaya tana nubanshi dan ko kad’an bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba.

“Zauna nan magana za muyi da ke”.

Yayi mata nuni bisa d’an da kalin dake kusa da su, Aynu ta zauna shima ya zauna gefe da ita kad’an.

“Kin san wani abu?”.

“A’a sai ka fad’a”.

“Wai me yasa Yarima baya son gani na da ke ne?”.

“Nima ban sani ba gaskiya”.

“Ok”.

Shiru ne ya biyo baya na d’an wani lokaci, kafin yasake dubanta yana fad’in.

“D’an juyo nan”.

Aynu ta zuyo tana dubansa, ya kai hannu gefan fuskarta yana fad’in.

“Wani abu ya b’ata beauty face d’inki bari in goge miki”.


“Jalil…..!”.

Suka ji muryar Yarima Fudhal akansu, Yarima Jalil ya sauke hannunsa yana fad’in.


“Sannu da fitowa Broda”.

Bai ko dubeshi ba, illa kafe idanuwansa da suka fara rinewa daga fari zuwa ja akan Aynu da yayi, a hankali ya furta.

“Jeki k’arasa aikin ki”.

Sum-sum Aynu ta wuce zuwa falon Yarima ita dai tasan ta gama aikin ta, may be wani aikin zai saka ta abin da ta raya aranta kenan.

Mintuna kad’an da zamanta ya shigo fuskarnan babu annuri neman guri yayi ya zauna yana fad’in.

“Had’amin tea”.

Da rawar jiki ta mik’e ta zuba masa tea d’in tafa shashshe sosai, yace ka da ta sanya komai illa sugar nan da nan ta had’a ta mik’a masa yasa hannu ya karb’a, tana shirin mik’ewa taji ya jawo hannunta kafin ta ankara sai jin rad’ad’i da azabar zafin ruwan tea d’in tayi bisa hannunta wanda ya ratsa har cikin kwakwalwar kanta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button